Back to Languages

Hausa - Chapter 40 - Ghafir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ghafir 40:1

Verse 2 — Surah Ghafir 40:2

Saukar da Littafi daga Allah ne, Mabuwayi, Masani

Verse 3 — Surah Ghafir 40:3

Mai gafarta zunubi kuma Mai karɓar tuba Mai tsananin azaba, Mai wadatarwa babu abin bautawa face Shi, zuwa gare Shi makoma take

Verse 4 — Surah Ghafir 40:4

Babu mai jayayya a cikin ayoyin Allah, face waɗanda suka kafirta. Saboda haka kada juyawarsu a cikin garuruwa ta ruɗe ka

Verse 5 — Surah Ghafir 40:5

Mutanen Nuhu sun ƙaryata a gabaninsu, da ƙungiyoyin da suke a bayansu, kuma kowace al'umma ta yi nufi game da Manzonsu, domin su kama shi. Kuma suka yi jayayya da ƙarya domin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kama su. To, yaya azaba Ta take

Verse 6 — Surah Ghafir 40:6

Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kafirta, domin su 'yan wuta ne

Verse 7 — Surah Ghafir 40:7

Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kewayenta, suna tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin imani da Shi, kuma suna yin istigfari domin waɗanda suka yi imani, (suna cewa), "Ya Ubangijinmu! Ka yalwaci dukan kome da rahama da ilmi to Ka yi gafara ga waɗanda suka tuba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azabar Jahim

Verse 8 — Surah Ghafir 40:8

Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidajen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, su da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da matan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 9 — Surah Ghafir 40:9

Kuma Ka tsare su daga munanan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga munanan ayyuka a ranarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma

Verse 10 — Surah Ghafir 40:10

Lalle waɗanda suka kafirta, ana kiran su, "Haƙiƙa, ƙin Allah (a gare ku) shi ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lokacin da ake kiran ku zuwa ga imani, sai kuna ta kafircewa

Verse 11 — Surah Ghafir 40:11

Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka matar da mu sau biyu, kuma Ka rayar da mu sau biyu, saboda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita

Verse 12 — Surah Ghafir 40:12

Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirayi Allah Shi kaɗai, sai ku kafirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi imani. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne

Verse 13 — Surah Ghafir 40:13

Shi ne Wanda ke nuna muku ayoyin Sa, kuma Ya saukar da arziki daga sama saboda ku, kuma babu mai yin tunani face mai mayar da al'amari ga Allah

Verse 14 — Surah Ghafir 40:14

Saboda haka ku kirayi Allah, kuna masu tsarkake addini a gare Shi, kuma ko da kafirai sun ƙi

Verse 15 — Surah Ghafir 40:15

Mai ɗaukaka darajoji (domin muminai), Mai Al'arshi, Yana jefa ruhi *daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bayinSa, domin ya yi gargaɗi kan ranar gamuwa

Verse 16 — Surah Ghafir 40:16

Ranar da suke bayyanannu, babu wani abu daga gare su wanda yake iya boyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa

Verse 17 — Surah Ghafir 40:17

Yau ana saka wa kowane rai a game da abin da ya aikata, babu zalunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne

Verse 18 — Surah Ghafir 40:18

Kuma ka yi musu gargaɗi kan ranar (Sa'a) makusanciya, a lokacin da zukata suke masu cika da bakin ciki, ga maƙosansu. Babu wani masoyi ga azzalumai, kuma babu wani mai ceto da za a yi wa da'a (ga cetonsu)

Verse 19 — Surah Ghafir 40:19

(Allah) Ya san yaudarar idanu da abin da ƙiraza ke ɓoyewa

Verse 20 — Surah Ghafir 40:20

Kuma Allah Shi ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, wanin Sa, ba su yin hukunci da kome. Lalle Allah, Shi ne Mai ji, Mai gani

Verse 21 — Surah Ghafir 40:21

Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, domin su duba ga yadda aƙibar waɗanda suka kasance a gabaninsu ta zama? Sun kasance su ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasa, sai Allah Ya kama su da laifuffukansu. Kuma ba su da wani mai tsarewa daga Allah

Verse 22 — Surah Ghafir 40:22

Wancan sababinsa, domin su Manzanninsu sun kasance suna zuwa gare su da hujjoji bayyanannu, sai suka kafirta, sai Allah Ya kama su. Lalle Shi Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azaba

Verse 23 — Surah Ghafir 40:23

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun aika Musa a game da ayoyinMu da wani dalili bayyananne

Verse 24 — Surah Ghafir 40:24

Zuwa ga Fir'auna da Hamana da Karuna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci

Verse 25 — Surah Ghafir 40:25

Sa'an nan, a lokacin da ya je musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi imani tare da shi, kuma ku rayar da matansu." Kuma mugun shirin kafirai, bai zama ba face a cikin bata

Verse 26 — Surah Ghafir 40:26

Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Musa, kuma shi, ya kirayi Ubangijinsa. Lalle ne ni, ina tsoron ya musanya addininku, ko kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasa

Verse 27 — Surah Ghafir 40:27

Kuma Musa ya ce: "Lalle ni, na nemi tsari da Ubangijina kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda ba ya imani da ranar Hisabi

Verse 28 — Surah Ghafir 40:28

Kuma wani namiji mumini daga dangin Fir'auna, yana boye imaninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum domin ya ce Ubangijina Allah ne, alhali kuwa haƙiƙa ya zo muku da hujjoji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan ya kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sashen abin da yake yi muku wa'adi zai same ku. Lalle ne Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya

Verse 29 — Surah Ghafir 40:29

Ya ku mutanena! Kuna da mulki a yau, kuma ku ne marinjaya a cikin kasa to wane ne zai taimake mu daga azabar Allah idan ta zo mana?" Fir'auna ya ce: "Ba ni nunamuku kome face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa

Verse 30 — Surah Ghafir 40:30

Kuma wannan da ya yi imani ya ce: "Ya mutanena! Lallene, ni, ina yi muku tsoron kwatankwacin ranar ƙungiyoyi

Verse 31 — Surah Ghafir 40:31

Kwatankwacin al'adar mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da waɗanda ke a bayansu. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga bayin Sa

Verse 32 — Surah Ghafir 40:32

Kuma ya mutanena! Lalleni, ina yi muku tsoron ranar kiran juna

Verse 33 — Surah Ghafir 40:33

A ranar da za ku juya, kuna masu bayar da baya (gudane) ba ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, ba shi da wani mai shiryarwa

Verse 34 — Surah Ghafir 40:34

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Yusufu ya zo muku daga gabani, da hujjoji bayyanannu, ba ku gushe ba kuna a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lokacin da ya halaka kuka ce, 'Allah ba zai aiko wani Manzo ba, a bayansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka

Verse 35 — Surah Ghafir 40:35

Waɗanda kejayayya a cikin ayoyin Allah, ba da wani dalili da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi imani. Kamar haka Allah ke bicewar haske a kan zuciyar dukan makangari, mai tilastawa

Verse 36 — Surah Ghafir 40:36

Kuma Fir'auna ye ce, "Ya Hamana! Ka gina mini bene, dammanina za ni isa ga ƙofofi

Verse 37 — Surah Ghafir 40:37

¡ofofin sammai domin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautawar Musa. Kuma lalle ni haƙiƙa ina zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawace wa Fir'auna munanan aikinsa kuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba face yana a cikin hasara

Verse 38 — Surah Ghafir 40:38

Kuma wannan da ya yi imani ya ce: "Ya mutanena! Ku bi ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa

Verse 39 — Surah Ghafir 40:39

Kuma ya mutanena! Wannan rayuwa ta duniya dan jin daɗi ne kawai, kuma lalle Lahira ita ce gidan tabbata

Verse 40 — Surah Ghafir 40:40

Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a saka masa ba face da misalinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji ko mace alhali kuwa shi mumini ne, to, waɗannan suna shiga Aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba

Verse 41 — Surah Ghafir 40:41

Kuma ya mutanena! Me ya same ni, ina kiran ku zuwa ga tsira, kuma kuna kira na zuwa ga wuta

Verse 42 — Surah Ghafir 40:42

Kuna kira na zuwa ga in kafirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da babu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni ina kiran ku zuwa ga Mabuwayi, Mai gafara

Verse 43 — Surah Ghafir 40:43

Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, ba ya da wani kira a cikin duniya, kuma ba shi da shi a Lahira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata su ne 'yan wuta

Verse 44 — Surah Ghafir 40:44

To za ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma ina fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bayin Sa

Verse 45 — Surah Ghafir 40:45

Sai Allah Ya tsare shi daga munanan abubuwa da suka yi na makirci, kuma mummunar azaba ta wajaba ga mutanen Fir'auna

Verse 46 — Surah Ghafir 40:46

Wuta, ana gitta su a kanta, safe da maraice, kuma a ranar da Sa'a take tsayuwa, ana cewa, "Ku shigar da mutanen Fir'auna a mafi tsananin azaba

Verse 47 — Surah Ghafir 40:47

Kuma a lokacin da suke husuma a cikin wuta, sai raunana (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mu, mun kasance mabiya gare ku, to, shin ku masu wadatar da mu ne daga barin wani rabo daga wuta

Verse 48 — Surah Ghafir 40:48

Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mu duka muna a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayin Sa

Verse 49 — Surah Ghafir 40:49

Kuma waɗanda suke a cikin wuta suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku roki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azaba

Verse 50 — Surah Ghafir 40:50

Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su je muku da hujjoji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun je!" Suka ce: "To, ku roƙa." Kuma roƙon kafirai bai zamo ba face a cikin ɓata

Verse 51 — Surah Ghafir 40:51

Lalle Mu, hakika, Muna taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi imani, a cikin rayuwar duniya da ranar da shaidu ke tsayawa

Verse 52 — Surah Ghafir 40:52

Ranar da uzurin azzalumai ba ya amfaninsu, kuma suna da la'ana, kuma suna da munin gida

Verse 53 — Surah Ghafir 40:53

Kuma lalle haƙiƙa, Mun bai wa Musa shiriya, kuma Mun gadar da Bani Isra'ila Littafi

Verse 54 — Surah Ghafir 40:54

Shiryarwa da tunawa ga ma'abuta hankali

Verse 55 — Surah Ghafir 40:55

Saboda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nemi gafara ga zunubinka, kuma ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, maraice da kuma wayewar safiya

Verse 56 — Surah Ghafir 40:56

Lalle waɗanda ke jayayya a cikin ayoyin Allah, ba game da wani dalili wanda ya je musu ba, babu kome a cikin kirazansu, face girman kai, ba su zama masu isa ga gurinsu ba, saboda haka ka nemi tsari daga Allah. Lalle Shi, Shi ne Mai ji, Mai gani

Verse 57 — Surah Ghafir 40:57

Lalle halittar sammai da ƙasa, ita ce mafi girma daga halittar mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba

Verse 58 — Surah Ghafir 40:58

Kuma makaho da mai gani ba su daidaita kuma waɗanda suka yi imani suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai munanawa ba su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunani

Verse 59 — Surah Ghafir 40:59

Lalle Sa'a, haƙiƙa mai zuwa ce, babu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutane ba su yin imani

Verse 60 — Surah Ghafir 40:60

Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu

Verse 61 — Surah Ghafir 40:61

Allah ne Wanda Ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, da rana mai ganarwa. Lalle Allah, haƙiƙa, Ma'abucin falala ne a kan mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa

Verse 62 — Surah Ghafir 40:62

Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kome, babu abin bautawa face Shi. To, yaya ake karkatar da ku

Verse 63 — Surah Ghafir 40:63

Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance suna jayayya game da ayoyin Allah

Verse 64 — Surah Ghafir 40:64

Allah ne Ya sanya muku kasa tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya suranta ku, sa'an nan Ya kyautata surorinku,, kuma Ya azurta ku daga abubuwa masu daɗi. Wancan Shine Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu ta bayyana

Verse 65 — Surah Ghafir 40:65

Shi ne Mai rai, babu abin bautawa face Shi. Saboda haka ku kira Shi, kuna masu tsarkake addini a gare Shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu

Verse 66 — Surah Ghafir 40:66

Ka ce: "Lalle ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lokacin da hujjoji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu

Verse 67 — Surah Ghafir 40:67

Shi ne Wanda Ya halitta ku daga turɓaya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga saren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kuna jariri, sa'an nan domin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan domin ku kasance tsofaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabanin haka, kuma domin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammaninku ko za ku hankalta

Verse 68 — Surah Ghafir 40:68

Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa)

Verse 69 — Surah Ghafir 40:69

Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jayayya a cikin ayoyin Allah, yadda ake karkatar da su

Verse 70 — Surah Ghafir 40:70

Waɗanda suka ƙaryata, game da Littafin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani

Verse 71 — Surah Ghafir 40:71

A lokacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyoyinsu, da sarƙoƙi ana jan su

Verse 72 — Surah Ghafir 40:72

A cikin ruwan zafi, sa'an nan a cikin wuta ana babbaka su

Verse 73 — Surah Ghafir 40:73

Sa'an nan a ce musu, "Ina abin da kuka kasance kuna shirki da shi

Verse 74 — Surah Ghafir 40:74

Wanin Allah?" Suka ce: "Sun ɓace mana. A'a, ba mu kasance muna kiran kome ba a gabani."Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kafirai

Verse 75 — Surah Ghafir 40:75

Wancan domin abin da kuka kasance ne kuna farin ciki da shi, a cikin ƙasa, ba da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kuna yi na nishaɗi

Verse 76 — Surah Ghafir 40:76

Ku shiga kofofin Jahannama kuna madawwama a cikinta. To, mazaunin masu girman kai ya munana

Verse 77 — Surah Ghafir 40:77

Saboda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, ko dai lalle Mu nuna maka sashen abin da Muka yi musu wa'adi da shi ko kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su

Verse 78 — Surah Ghafir 40:78

Kuma lalle haƙiƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabaninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka labarinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta labarinsa ba a gare ka. Ba ya yiwuwa ga wani Manzo ya je da wata ayar mu'ujiza face da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya je, sai a yi hukunci da gaskiya, masu ɓatawa sun yi hasara a can

Verse 79 — Surah Ghafir 40:79

Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbobi domin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci

Verse 80 — Surah Ghafir 40:80

Kuma kuna da abubuwan amfani a cikinsu, kuma domin ku isar da wata buƙata, a cikin ƙirazanku a kansu kuma a kansu da a kan jirage ake, ɗaukar ku

Verse 81 — Surah Ghafir 40:81

Kuma Ya nuna muku ayoyin Sa. To, wane ayoyin Allah kuke musu

Verse 82 — Surah Ghafir 40:82

Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, domin su duba yadda aƙibar waɗanda ke a gabaninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurabun sana'o'i a cikin ƙasa. To, abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar da su ba

Verse 83 — Surah Ghafir 40:83

A lokacin da Manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi* kuma abin da suka kasance suna yi na izgili da shi ya wajaba a kansu

Verse 84 — Surah Ghafir 40:84

Sa'an nan a lokacin da suka ga azabarMu, suka ce: "Mun yi imani da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kafirta da abin da muka kasance muna shirki da shi

Verse 85 — Surah Ghafir 40:85

To imaninsu bai kasance yana amfaninsu ba a lokacin da suka ga azabarMu. Hanyar Allah wadda ta gabata a cikin bayin Sa. Kuma kafirai sun yi hasara a can