Kuma suka ce: "Zukatanmu na a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shamaki. sahoda haka ka yi aiki, lalle mu masu aiki ne
Ka ce: "Ni mutum kawai ne kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa abin bautawarku, abin bautawa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nemi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga masu yin shirki
Ka ce: "Ashe lalle ku, haƙiƙa, kuna kafurta a game da wanda Ya halitta kasa a cikin kwanuka biyu, kuma kuna sanya Masa kishiyoyi? Wancan fa, shi ne Ubangijin halittu
Kuma Ya sanya, a cikinta, duwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abubuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu masu daidaita, domin matambaya
Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhali kuwa ita (a lokacin) hayaƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasa "Ku zo, bisa ga yarda ko a kan tilas." Suka ce: "Mun zo, muna masu ɗa'a
Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwanuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kowace sama da al'amarinta, kuma Muka kawata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarawar Mabuwayi ne, Masani
A lokacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bayansu, "Kada ku bauta wa kowa face Allah." suka ce: "Da UbangiJinmu Ya so, lalle da Ya saukar da mala' iku, saboda haka lalle mu, masu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi
To, amma Adawa, sai suka yi girman kai a cikin kasa, ba da wani hakki ba, suka ce: "Wane ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cewa Allah, wanda Ya halitta su Shine Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ayoyin Mu suna yin musu
Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwanuka na shu'umci, domin Mu ɗanɗana musu azabar wulaƙanci, a cikin rayuwar duniya, kuma lalle azabar Lahira ita ce mafi wulaƙantarwa, kuma su ba za a taimake su ba
Kuma amma Samudawa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, domin haka tsawar azabar wulakanci, ta kama su saboda abin da suka kasance suna aikatawa (domin neman wata fa'ida)
Kuma suka ce wa fatunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda ke sanya kowane abu ya yi furuci, Shi ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shi ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku
Ba ku kasance kuna sani ba a ɓoye, cewa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fatunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cewa Allah bai san abubuwa masu yawa daga abin da kuke aikatawa ba
Kuma Muka sallaɗar da mabiya* a gare su, sai suka ƙawata musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bayansu. Kuma kalmar azaba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummomi da suka shuɗe a gabaninsu daga aljannu da mutane. Lalle su, sun kasance masu hasara
Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurara ga wannan Alkur' ani, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lokacin karatun) sa, tsammaninku za ku rinjaya
Saboda haka, lalle za Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azaba mai tsanani, kuma lalle za Mu saka musu da mafi munin abin da suka kasance suna aikatawa
Wancan shi ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Suna a gidan dawwama a cikinta, domin sakamako ga abin da suka kasance suna yin musu game da ayoyin Mu
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nuna mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a karkashin, ƙafafunmu, domin su kasance daga ƙaskantattu
Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shi ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, mala'iku na sassauka a kansu (a lokacin saukar ajalinsu suna ce musu) "Kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushara da Aljanna, wadda kun kasance ana yi muku wa'adi da ita
Mu ne majibintanku a cikin rayuwar duniya da kuma a cikin Lahira, kuma a cikinta kuna da abin da rayukanku ke sha'awa, kuma kuna da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta
Kuma wane ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle niina daga masu sallamawar al'amari zuwa ga Allah
Kuma kyautatawa ba ta daidaita kuma haka munanawa. Ka tunkuɗe cuta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi
Kuma akwai daga ayoyin Sa, dare da yini, da rana da wata. Kada ku yi sujada ga rana, kuma kada ku yi ga wata. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shi ne kuke bauta wa
Kuma akwai daga ayoyinSa cewa lalle kai kana ganin ƙasa ƙeƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya raya ta, haƙiƙa, Mai rayar da matattu ne. Lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kowane abu
Lalle waɗannan da ke karkacewa a cikin ayoyinMu, ba su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jefawa a cikin Wuta ne mafifici ko kuwa wanda zai je amintacce a Ranar ¡iyama? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shi Mai gani ne ga abin da kuke aikatawa
Ba za a fada maka ba face abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabaninka. Lalle Ubangijinka, haƙiƙa, Ma'abucin gafara ne, kuma Ma'abucin azaba mai raɗaɗi ne
Kuma da Mun sanya shi abin karatu na ajamanci, lalle da sun ce, "Don me ba a bayyana ayoyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sami littafi ba'ajame da Manzo Balarabe?" Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi imani. Kuma wadanda ba su yi imani ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan ana kiran su daga wuri mai nisa
Kuma lalle Mun bai wa Musa Littafi, sai aka yi ɗaɓani a cikinsa, Kuma ba domin wata kalma da ta gabata ba daga Ubangijinka, lalle da an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle su, haƙiƙa suna a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kokanto
Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'ya'yan itace ba su fita daga kwasfofinsu, kuma wata mace ba ta yin ciki, kuma ba ta haihuwa, face da saninSa, kuma a ranar da Yake kiran su (Ya ce): "Ina abokan tarayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai babu mai bayar da shaida da haka nan daga gare mu
Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bayan wata cuta ta shafe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tawa ce kuma ba ni zaton Sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijina, haƙiƙa, ina da makoma mafi kyau, a wurin Sa." To, lalle za Mu ba da labari ga waɗanda suka kafirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Muna ɗanɗana musu daga azaba, Mai kauri
Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ani) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kafirta a game da Shi, wane ne mafi ɓata daga wanda yake yana a cikin saɓani manisanci (daga gaskiya)
Za Mu nuna musu ayoyin Mu a cikin sasanni da kuma cikin rayukansu, har ya bayyana a gare su cewa lalle (Alƙur'ani), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cewa lalle Shi halartacce ne a kan kowane abu ne