Back to Languages

Hausa - Chapter 42 - Ash-Shura

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ash-Shura 42:1

Verse 2 — Surah Ash-Shura 42:2

Verse 3 — Surah Ash-Shura 42:3

Kamar wancan *(asirin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabaninka

Verse 4 — Surah Ash-Shura 42:4

(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma

Verse 5 — Surah Ash-Shura 42:5

Sammai na kusan su tsage daga bisansu, kuma mala'iku na yin tasihi game da gode wa Ubangijinsu kuma suna istigfari domin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah Ash-Shura 42:6

Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda ba Shi ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, ba wakili ne a kansu ba

Verse 7 — Surah Ash-Shura 42:7

Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karantawa (Alƙur'ani) na Larabci zuwa gare ka, domin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kewayenta, kuma ka yi gargaɗi game da ranar taruwa, babu shakka gare ta, wata ƙungiya tana a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tana a cikin sa'ir

Verse 8 — Surah Ash-Shura 42:8

Kuma da Allah Ya so, da Ya haɗa su al'umma guda, kuma Amma Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhali kuwa azzalumaii ba su da, wani majiɓinci, kuma ba su da wani mataimaki

Verse 9 — Surah Ash-Shura 42:9

Ko kuma sun riƙi wanin Sa majiɓinta? To Allah Shi ne Majiɓinci, kuma Shi ne ke rayar da matattu alhali kuwa Shi, Maiikon yi ne a kan dukan kome

Verse 10 — Surah Ash-Shura 42:10

Kuma abin da kuka saɓa wa juna a cikinsa ko mene ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina

Verse 11 — Surah Ash-Shura 42:11

(Shi ne) Mai ƙaga halittar sammai da ƙasai, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbobi maza da mata, Yana halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shi ne Mai ji, Mai gani

Verse 12 — Surah Ash-Shura 42:12

Shi ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yana shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yana hukuntawa. Lalle ne, Shi Masani ne ga dukan kome

Verse 13 — Surah Ash-Shura 42:13

Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nuhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrahim da Musa da Isa, cewa ku tsayar da addini sosai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. *Abin da kuke kira zuwa gare shi,** ya yi nauyi a kan masu shirki. Allah na zaɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yana shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyar Sa

Verse 14 — Surah Ash-Shura 42:14

Kuma ba su rarraba ba face bayan da ilmi ya je musu, domin zalunci a tsakaninsu kuma ba domin wata kalma* ta gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, da an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gadar wa Littafi daga bayansu, haƙiƙa, suna cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto

Verse 15 — Surah Ash-Shura 42:15

Saboda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zuciyoyinsu, kumaka ce, "Na yi imani da abin da Allah Ya saukar na littafi, kuma an umurce ni da in yi adalci a tsakaninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shi ne Ubangijinku, ayyukanmu na gare mu, kuma ayyukanku na gare ku, kuma babu wata hujja a tsakaninmu da tsakaninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makoma take

Verse 16 — Surah Ash-Shura 42:16

Kuma waɗannan da ke jayayya a cikin al'amarin Allah daga bayan an karɓa masa, hujjarsu ɓatacciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma suna da wata azaba mai tsanani

Verse 17 — Surah Ash-Shura 42:17

Allah ne Wanda Ya saukar da Littafi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cewa ana) tsammanin Sa'ar kusa take

Verse 18 — Surah Ash-Shura 42:18

Waɗanda ba su yi imani da ita ba, (su) ke neman gaggautowarta. Alhali kuwa waɗanda suka yi imani, masu tsoro ne daga gare ta, kuma sun sani, cewa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙiƙa, suna a cikin ɓata Mai nisa

Verse 19 — Surah Ash-Shura 42:19

Allah Mai tausasawa ne ga bayinsa. Yana azurta wanda yake so, alhali kuma Shi ne Maiƙarfi, Mabuwayi

Verse 20 — Surah Ash-Shura 42:20

Wanda ya kasance yana nufin noman Lahira za Mu ƙara masa a cikin nomansa, kuma wanda ya kasance yana nufin noman duniya, za Mu sam masa daga gare ta, alhali kuwa ba shi da wani rabo a cikin Lahira

Verse 21 — Surah Ash-Shura 42:21

Ko suna da waɗansu abokan tarayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma ba domin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle azzalumai suna da azaba mai raɗaɗi

Verse 22 — Surah Ash-Shura 42:22

Kana ganin azzalumai suna masu tsoro daga abin da suka sana'anta alhali kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai suna a cikin fadamun Aljanna suna da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma

Verse 23 — Surah Ash-Shura 42:23

Wancan shi ne Allah ke bayar da bushara da shi ga bayin Sa waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijara a kansa, face dai soyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu ƙara masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai godiya

Verse 24 — Surah Ash-Shura 42:24

Ko za su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zuciyarka, kuma Allah Yana shafe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmominSa. Lalle ne Shi Masani ne ga abin da ke cikin zukata

Verse 25 — Surah Ash-Shura 42:25

Kuma Shi ne ke karɓar tuba daga bayinSa, kuma Yana Yafe ƙananan laifuffuka, alhali kuwa Yana sanin abin da kuke aikatawa

Verse 26 — Surah Ash-Shura 42:26

Kuma Yana karɓa wa waɗannan da suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yana ƙara musu (sakamako) daga falalar Sa. Kuma kafirai suna da wata azaba mai tsanani

Verse 27 — Surah Ash-Shura 42:27

Kuma da Allah Ya shimfiɗa arziki ga bayinSa, da sun yi zaluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yana sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shi, game da bayinSa, Mai labartawa ne, Mai gani

Verse 28 — Surah Ash-Shura 42:28

Kuma Shi ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a bayan sun yanke ƙauna kuma Yana watsa rahamar Sa, alhali kuwa Shi ne Majiɓinci, Mai godiya

Verse 29 — Surah Ash-Shura 42:29

Kuma akwai daga ayoyin Sa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya watsa a cikinsu na dabba alhali kuwa Shi Mai iko ne ga tara su, a lokacin da Yake so

Verse 30 — Surah Ash-Shura 42:30

Kuma abin da ya same ku na wata masifa, to, game da abin da hannayenku suka sana' anta ne kuma (Allah) Yana Yafewar (waɗansu laifuffuka) masu yawa

Verse 31 — Surah Ash-Shura 42:31

Kuma ba ku zama masu buwaya ba a cikin ƙasa kuma ba ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma ba ku da wani mataimaki

Verse 32 — Surah Ash-Shura 42:32

Kuma akwai daga ayoyinsa, jirage masu gudana a cikin teku kamar duwatsu

Verse 33 — Surah Ash-Shura 42:33

Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jiragen su yini suna masu kawaici a kan bayan tekun, Lalle ne ga wancan, haƙiƙa, akwai ayoyi ga dukan mai haƙuri, Mai godiya

Verse 34 — Surah Ash-Shura 42:34

Ko Ya halaka su (su jiragen) saboda abin da masu su suka sana'anta, alhali kuwa Yana yafe (laifuffuka) masu yawa

Verse 35 — Surah Ash-Shura 42:35

Kuma domin waɗanda ke jayayya a cikin ayoyin Mu su sani (cewa) ba su da wata mafaka

Verse 36 — Surah Ash-Shura 42:36

Saboda haka abin da aka ba ku, ko mene ne, to, jin daɗin rayuwar duniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shi ne mafifici, kuma Shi ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi imani kuma suna dogara a kan Ubangijinsu kawai

Verse 37 — Surah Ash-Shura 42:37

Kuma waɗanda *ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfasha, kuma idan sun yi fushi, su, suna gafartawa

Verse 38 — Surah Ash-Shura 42:38

Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shawara ne a tsakaninsu, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa

Verse 39 — Surah Ash-Shura 42:39

Da waɗanda* idan zalunci ya same su, suna neman taimako (su rama)

Verse 40 — Surah Ash-Shura 42:40

Kuma sakamakon cuta shi ne wata cuta kamarta, sai dai wanda Ya yafe kuma ya kyautata, to ladarsa na ga Allah. Lalle ne, Shi (Allah) ba Ya son azzalumai

Verse 41 — Surah Ash-Shura 42:41

Kuma Lalle ne, wanda ya nemi taimakon ramawa a bayan an zalunce shi, to waɗannan babu wata hanyar zargi a kansu

Verse 42 — Surah Ash-Shura 42:42

lnda hanyar zargi kawai take, shi ne a kan waɗanda ke zaluntar mutane kuma suna ƙetare haddin shari'a cikin ƙasa ba tare da haƙƙi ba. Waɗannan suna da azaba Mai raɗaɗi

Verse 43 — Surah Ash-Shura 42:43

Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gafarta (wa wanda ya zalunce shi), to shi wancan aiki haƙiƙa, yana daga manyan al'amura (da Allah ke so)

Verse 44 — Surah Ash-Shura 42:44

Kuma wanda* (Allah Ya ɓatar, to, ba shi da wani majiɓinci bayan Sa, kuma za ka ga azzalumai, a lokacin da suka ga azaba, suna cewa, "Shin, akwai hanya zuwa ga komawa)

Verse 45 — Surah Ash-Shura 42:45

Kuma kana ganin su ana gitta su a kanta, suna ƙasƙantattu saboda wulakanci, suna hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi imani sai su ce, "Lalle ne, masu hasara, su ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu da iyalansu a Ranar ¡iyama." To, lalle ne, azzalumai suna a cikin wata azaba zaunanniya

Verse 46 — Surah Ash-Shura 42:46

Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, ba shi da wani godabe na tsira

Verse 47 — Surah Ash-Shura 42:47

Ku karɓa wa Ubangijinku tun gabanin wani yini ya zo, babu makawa gare shi daga Allah, ba ku da wata mafaka a ranar nan, kuma ba ku iya yin wani musu

Verse 48 — Surah Ash-Shura 42:48

To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kana mai tsaro a kansu ba, babu abin da ke a kanka face iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mu idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masifa ta same su saboda abin da hannayensu suka gabatar, to, lalle ne mutum mai tsananin kafirci ne

Verse 49 — Surah Ash-Shura 42:49

Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yana halitta abin da Yake so. Yana bayar da 'ya'ya mata ga wanda yake so, kuma Yana bayar da ɗiya maza ga wanda Yake so

Verse 50 — Surah Ash-Shura 42:50

Ko kuma Ya haɗa su maza da mata, kuma Yana sanya wanda Ya so bakarare.* Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ikon yi

Verse 51 — Surah Ash-Shura 42:51

Kuma ba ya kasancewa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana* face da wahayi, ko daga bayan wani shamaki, ko Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shi, Maɗaukaki ne Mai hikima

Verse 52 — Surah Ash-Shura 42:52

Kuma kamar wancan Mun aika wani ruhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance ka san abin da yake littafi ba, ko abin da Yake imani, kuma amma Mun sanya shi (ruhin, watau Alƙur'ani) wani haske ne, Muna shiryar da wanda Muke so daga cikin bayin Mu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙiƙa, kana shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya

Verse 53 — Surah Ash-Shura 42:53

Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke komawa