Back to Languages

Hausa - Chapter 43 - Az-Zukhruf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Az-Zukhruf 43:1

Verse 2 — Surah Az-Zukhruf 43:2

Ina rantsuwa da Littafi Mabayyani

Verse 3 — Surah Az-Zukhruf 43:3

Lalle Mu, Mun sanya shi abin karatu na Larabci, tsammaninku, kuna hankalta

Verse 4 — Surah Az-Zukhruf 43:4

Kuma lalle, shi, a cikin uwar littafi a wurin Mu, haƙiƙa, maɗaukaki ne, bayyananne

Verse 5 — Surah Az-Zukhruf 43:5

Shin, za Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne domin kun kasance mutane masu ɓarna

Verse 6 — Surah Az-Zukhruf 43:6

Alhali kuwa sau nawa Muka *aika wani Annabi a cikin mutanen farko

Verse 7 — Surah Az-Zukhruf 43:7

Kuma wani Annabi bai je musu ba face sun kasance, game da shi, suna masu yin izgili

Verse 8 — Surah Az-Zukhruf 43:8

Sai Muka halakar da waɗanda suke su ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misalin mutanen farkon ya shuɗe

Verse 9 — Surah Az-Zukhruf 43:9

Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wane ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle za su ce, "Mabuwayi Mai ilmi ne Ya halitta su

Verse 10 — Surah Az-Zukhruf 43:10

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyoyi a cikinta, tsammaninku za ku nemi shiryuwa

Verse 11 — Surah Az-Zukhruf 43:11

Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rayar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari)

Verse 12 — Surah Az-Zukhruf 43:12

Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbobin ni'ima, abin da kuke hawa

Verse 13 — Surah Az-Zukhruf 43:13

Domin ku daidaitu a kan bayansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lokacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hore mana wannan alhali kuwa ba mu kasance masu iya rinjaya gare Shi ba

Verse 14 — Surah Az-Zukhruf 43:14

Kuma lalle mu haƙiƙa masu* juyawa muke, zuwa ga Ubangijinmu

Verse 15 — Surah Az-Zukhruf 43:15

Kuma suka sanya *Masa juz'i daga bayinsa. Lalle ne mutum, haƙiƙa, mai yawan kafirci ne, mai bayyanawar kafircin

Verse 16 — Surah Az-Zukhruf 43:16

Ko za Ya ɗauki 'ya'ya mata daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zaɓe ku da ɗiya maza

Verse 17 — Surah Az-Zukhruf 43:17

Alhali kuwa idan an bayar da bushara ga ɗayansu da abin da ya buga misali da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tana wadda aka baƙanta launinta, kuma yana cike da baƙin ciki

Verse 18 — Surah Az-Zukhruf 43:18

Ashe, kuma (Allah zai zaɓi) wanda ake reno a cikin ƙawa alhali kuwa ga shi a husuma ba mai iya bayyanawar magana ba

Verse 19 — Surah Az-Zukhruf 43:19

Kuma suka mayar da mala'iku ('ya'ya) mata, alhali kuwa su, waɗanda suke bayin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? za a rubuta shaidarsu kuma a tambaye su

Verse 20 — Surah Az-Zukhruf 43:20

Kuma suka ce: "Da Mai rahama ya so, da ba mu bauta musu ba." Ba su da wani ilmi game da wancan! Babu abin da suke yi face yanki-faɗi

Verse 21 — Surah Az-Zukhruf 43:21

Ko Mun ba su wani littafi ne a gabaninsa (Alƙur'ani) saboda haka da shi suke riƙe

Verse 22 — Surah Az-Zukhruf 43:22

A'a, sun ce dai, "Lalle mu, mun sami ubanninmu a kan wani addini (na al'ada) kuma lalle mu, a kan gurabansu muke masu neman shiryuwa

Verse 23 — Surah Az-Zukhruf 43:23

Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabaninka, a cikin wata alƙarya, face mani'imtanta sun ce, "Lalle mu, mun sami ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mu, masu koyi nea kan gurabansu

Verse 24 — Surah Az-Zukhruf 43:24

(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sami ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mu dai masu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi

Verse 25 — Surah Az-Zukhruf 43:25

Saboda haka Muka yi musu azabar ramuwa. To, ka dubi yadda aƙibar masu ƙaryatawa take

Verse 26 — Surah Az-Zukhruf 43:26

Kuma (ka ambaci) lokacin da Ibrahim ya ce wa ubansada mutanensa, "Lalle ni mai barranta ne daga abin da kuke bautawa

Verse 27 — Surah Az-Zukhruf 43:27

Face wannan *da Ya ƙaga halittata, to, lalle Shi ne zai shiryar da ni

Verse 28 — Surah Az-Zukhruf 43:28

Kuma (Ibrahim) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammaninsu su komo daga ɓata

Verse 29 — Surah Az-Zukhruf 43:29

A'a, Na jiyar da waɗannan mutane daɗi su da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu

Verse 30 — Surah Az-Zukhruf 43:30

Kuma a lokacin da gaskiyar ta je musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mu masu kafirta da shi ne

Verse 31 — Surah Az-Zukhruf 43:31

Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ani a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun* nan biyu ba

Verse 32 — Surah Az-Zukhruf 43:32

Shin, su ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mu ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rayuwar duniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajoji domin waɗansunsu su riƙi waɗansu leburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci*), ita ce mafificiya daga abin da suke tarawa

Verse 33 — Surah Az-Zukhruf 43:33

Kuma ba domin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, da Mun sanya wa masu kafirce wa Mai Rahama, a gidajensu, rufi na azurfa, kuma da matakalai, ya zama a kanta suke taƙawa

Verse 34 — Surah Az-Zukhruf 43:34

(Kuma a gidajensu, Mu sanya) ƙyamare da gadaje, a kansu suke kishingiɗa

Verse 35 — Surah Az-Zukhruf 43:35

Da zinariya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin daɗin rayuwar duniya nekawai' alhali kuwa Lahira, a wurin Ubangijinka, ta masu taƙawa ce

Verse 36 — Surah Az-Zukhruf 43:36

Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, za Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shi ne abokinsa

Verse 37 — Surah Az-Zukhruf 43:37

Kuma lalle su haƙiƙa suna kange su daga hanya, kuma suna Zaton cewa su masu shiryuwa ne

Verse 38 — Surah Az-Zukhruf 43:38

Har a lokacin da (abokin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka, tir da kai ga zama abokin mutum

Verse 39 — Surah Az-Zukhruf 43:39

Kuma (wannan magana) ba za ta amfane ku ba, a yau, domin kun yi zalunci, lalle ku masu tarewa ne a cikin azaba

Verse 40 — Surah Az-Zukhruf 43:40

Shin to, kai kana jiyar da kurma ne, ko kana shiryar da makaho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna

Verse 41 — Surah Az-Zukhruf 43:41

To, ko dai Mu tafi *da kai to, lalle Mu, masu yin azabarramu, wa ne a kansu

Verse 42 — Surah Az-Zukhruf 43:42

Ko kuma Mu nuna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mu, Masu ikon tasarrufi a kansu ne

Verse 43 — Surah Az-Zukhruf 43:43

Saboda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kana a kan hanya madaidaiciya

Verse 44 — Surah Az-Zukhruf 43:44

Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutanenka, kuma za a tambaye ku

Verse 45 — Surah Az-Zukhruf 43:45

Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabaninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumaka, wasun (Allah), Mai rahama, ana bauta musu

Verse 46 — Surah Az-Zukhruf 43:46

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun aika Musa, game da ayoyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashawartansa, sai ya ce: "Lalle ni, Manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 47 — Surah Az-Zukhruf 43:47

To, a lokacin da ya je musu da ayoyin Mu, sai ga su suna yi musu dariya

Verse 48 — Surah Az-Zukhruf 43:48

Kuma ba Mu nuna musu wata aya ba, face ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kama su da azaba, tsammaninsu ko suna komowa

Verse 49 — Surah Az-Zukhruf 43:49

Kuma suka ce: "Ya kai mai sihiri! Ka roƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mu, haƙiƙa, masu shiryuwa ne

Verse 50 — Surah Az-Zukhruf 43:50

To, a lokacin da duk Muka kuranye musu azaba, sai ga su suna warware alkawarinsu

Verse 51 — Surah Az-Zukhruf 43:51

Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutanensa, ya ce: "Ya mutanena! Ashe mulkin Masar ba a gare ni yake ba, kuma waɗannan koguna suna gudana daga ƙarƙashina? Ashe, ba ku gani ba

Verse 52 — Surah Az-Zukhruf 43:52

Ko kuma ba ni ne mafifici ba daga wannan wanda yake shi wulakantacce ne kuma ba ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar

Verse 53 — Surah Az-Zukhruf 43:53

To, don me, ba a jefa mundaye na zinariya a kansaba, ko kuma mala'iku su taho tare da shi haɗe

Verse 54 — Surah Az-Zukhruf 43:54

Sai ya sassabce hankalin mutanensa, saboda haka suka bi shi. Lalle su, sun kasance waɗansu irin mutane ne fasiƙai

Verse 55 — Surah Az-Zukhruf 43:55

Saboda haka a lokacin da suka husatar da Mu, Muka yi musu azabar ramuwa sai Muka nutsar da su gaba ɗaya

Verse 56 — Surah Az-Zukhruf 43:56

Sai Muka sanya su magabata kuma abin misali ga mutanen ƙarshe

Verse 57 — Surah Az-Zukhruf 43:57

Kuma a lokacin da aka buga misali da ¦an Maryama, sai ga mutanenka daga gare shi (shi misalin) suna dariya da izgili

Verse 58 — Surah Az-Zukhruf 43:58

Kuma suka ce: "Shin, gumakanmu ne mafifita ko shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misali ba a gare ka face domin yin jidali.* A'a, su mutane nemasu husuma

Verse 59 — Surah Az-Zukhruf 43:59

Shi (¦an Maryama) bai zama ba face wani bawa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin koyi ga Bani Isra'ila

Verse 60 — Surah Az-Zukhruf 43:60

Kuma da Muna so lalle ne da Mun sanya mala'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, suna mayewa

Verse 61 — Surah Az-Zukhruf 43:61

Kuma lalle shi, haƙiƙa, wani ilmi ne na Sa'a, saboda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya

Verse 62 — Surah Az-Zukhruf 43:62

Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shi maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanawar ƙiyayya

Verse 63 — Surah Az-Zukhruf 43:63

Kuma a lokacin da Isa ya je da hujjoji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne na zo muku da hikima kuma domin in bayyana muku, sashen abin da kuke saɓa wa juna acikinsa, saboda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a

Verse 64 — Surah Az-Zukhruf 43:64

Lalle ne, Allah Shi ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku saboda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya

Verse 65 — Surah Az-Zukhruf 43:65

Sai ƙungiyoyi *suka saɓa a tsakaninsu. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka yi zalunci daga azabar yini mai raɗaɗi

Verse 66 — Surah Az-Zukhruf 43:66

Shin suna jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta je musu bisaga abke, alhali kuwa ba su sani ba

Verse 67 — Surah Az-Zukhruf 43:67

Masoya a yinin nan, sashensu zuwa ga sashe maƙiya ne, face masu taƙawa (su kam masu son juna ne)

Verse 68 — Surah Az-Zukhruf 43:68

Ya bayiNa! Babu tsoro a kanku a yau, kuma ba za ku yi baƙin ciki ba

Verse 69 — Surah Az-Zukhruf 43:69

Waɗanda suka yi imani da ayoyin Mu, kuma suka kasance masu sallamawar al'amari (ga Allah)

Verse 70 — Surah Az-Zukhruf 43:70

Ku shiga Aljanna, ku da matan aurenku, ana girmama ku

Verse 71 — Surah Az-Zukhruf 43:71

Ana kewayawa a kansu da akussa na zinariya da kofuna, alhali kuwa a cikinsu akwai abin da rayuka ke marmari kuma idanu su ji daɗi, kuma ku, a cikinta (Aljannar), madawwama ne

Verse 72 — Surah Az-Zukhruf 43:72

Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gadar da ku ita saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 73 — Surah Az-Zukhruf 43:73

Kuna samu, a cikinta, 'ya'yan itacen marmari masu yawa, daga cikinsu kuke ci

Verse 74 — Surah Az-Zukhruf 43:74

Lalle masu laifi madawwama ne a cikin azabar Jahannama

Verse 75 — Surah Az-Zukhruf 43:75

Ba a sauƙaƙar da ita (azabar) daga gare su, alhali kuwa su, a cikinta, masu kasa magana ne

Verse 76 — Surah Az-Zukhruf 43:76

Kuma ba Mu zalunce su ba, amma su ne suka kasance azzalumai

Verse 77 — Surah Az-Zukhruf 43:77

Kuma suka yi kira, "Ya Maliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana* " (Maliku) ya ce: "Lalle ku mazauna ne

Verse 78 — Surah Az-Zukhruf 43:78

Lalle ne, haƙiƙa, Mun je muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku masu ƙi ga gaskiyar ne

Verse 79 — Surah Az-Zukhruf 43:79

Ko kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mu, Masu tukkawa ne

Verse 80 — Surah Az-Zukhruf 43:80

Ko suna zaton lalle Mu, ba Mu jin asirinsu da ganawarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tare da su suna rubutawa

Verse 81 — Surah Az-Zukhruf 43:81

Ka ce: "Idan har akwai ɗa ga Mai rahama, to, ni ne farkon masu bauta (wa ɗan)

Verse 82 — Surah Az-Zukhruf 43:82

Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantawa

Verse 83 — Surah Az-Zukhruf 43:83

Saboda haka, ka ƙyale su, su kutsa kuma su yi wasa har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi

Verse 84 — Surah Az-Zukhruf 43:84

Kuma Shi ne wanda ke abin bautawa a sama kuma abin bautawa a ƙasa, kuma, Shi ne Mai hikima, Masani

Verse 85 — Surah Az-Zukhruf 43:85

Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasa abin da ke a tsakaninsu ta bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 86 — Surah Az-Zukhruf 43:86

Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki ceto ba, face wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma su, suna sane* (da haka)

Verse 87 — Surah Az-Zukhruf 43:87

Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta su?" Lalle ne za su ce Allah ne. To, yaya ake juyar da su

Verse 88 — Surah Az-Zukhruf 43:88

Kuma da (ilmin) maganar Sa (Annabi) "Ya Ubangijina! Lalle waɗannan mutane ne waɗanda ba za su yi imani ba

Verse 89 — Surah Az-Zukhruf 43:89

To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salama." Sa'an nan kuma za su sani