Back to Languages

Hausa - Chapter 44 - Ad-Dukhan

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ad-Dukhan 44:1

Verse 2 — Surah Ad-Dukhan 44:2

Ina rantsuwa da Littafi Mabayyani

Verse 3 — Surah Ad-Dukhan 44:3

Lalle ne, Mu, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mu' Mun kasance Masu yin gargaɗi

Verse 4 — Surah Ad-Dukhan 44:4

A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kowane umurui bayyananne

Verse 5 — Surah Ad-Dukhan 44:5

Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mu ne Muka kasance Masu aikawa

Verse 6 — Surah Ad-Dukhan 44:6

Saboda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shi, Shi ne Mai ji, Masani

Verse 7 — Surah Ad-Dukhan 44:7

(Shi ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu, idan kun kasance masu yaƙini (za ku gane haka)

Verse 8 — Surah Ad-Dukhan 44:8

Babu abin bautawa face Shi. Yana rayarwa Kuma Yana kashewa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko

Verse 9 — Surah Ad-Dukhan 44:9

A'a su, suna wasa a cikin shakka

Verse 10 — Surah Ad-Dukhan 44:10

Saboda haka, ka dakata ranar da sama za ta zo da hayaƙi bayyananne

Verse 11 — Surah Ad-Dukhan 44:11

Yana rufe mutane. Wannan wata azaba ce mai raɗaɗi

Verse 12 — Surah Ad-Dukhan 44:12

Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azaba. Lalle Mu, masu imani ne

Verse 13 — Surah Ad-Dukhan 44:13

Ina tunawa take a gare su, alhali kuwa, haƙiƙa, Manzo mai bayyanawa Ya je musu (da gargaɗin saukar azabar, ba su karɓa ba)

Verse 14 — Surah Ad-Dukhan 44:14

Sa'an nan suka juya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayawa* ne, mahaukaci

Verse 15 — Surah Ad-Dukhan 44:15

Lalle Mu, Masu kuranyewar azaba ne, a ɗan lokaci kaɗan, lalle ku, masu komawa ne (ga laifin)

Verse 16 — Surah Ad-Dukhan 44:16

Ranar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mu masu azabar ramuwa ne

Verse 17 — Surah Ad-Dukhan 44:17

Kuma lalle ne haƙiƙa a gabaninsu, Mun fitini mutanen Fir'auna, kuma wani Manzo karimi ya je musu

Verse 18 — Surah Ad-Dukhan 44:18

(Mazon ya ce): "Ku kawo mini (imaninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku

Verse 19 — Surah Ad-Dukhan 44:19

Kuma kada ku nemi ɗaukaka a kan Allah. Lalle ni mai zo muku ne da dalili bayyananne

Verse 20 — Surah Ad-Dukhan 44:20

Kuma lalle ni na nemi tsari da Ubangijina, kuma Ubangijinku, domin kada ku jefe ni

Verse 21 — Surah Ad-Dukhan 44:21

Kuma idan ba ku yi imani saboda ni ba, to, ku nisance ni

Verse 22 — Surah Ad-Dukhan 44:22

Sai ya kirayi Ubangjinsa cewa waɗannan mutanene masu laifi

Verse 23 — Surah Ad-Dukhan 44:23

(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle ku, waɗanda ake bi ne (domin a kama ku)

Verse 24 — Surah Ad-Dukhan 44:24

Kuma ka bar teku rarrabe. Lalle su, runduna ce abar nutsarwa

Verse 25 — Surah Ad-Dukhan 44:25

Da yawa suka bar gonaki da maremari

Verse 26 — Surah Ad-Dukhan 44:26

Da shuke-shuke da matsayi mai kyau

Verse 27 — Surah Ad-Dukhan 44:27

Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta suna masu hutu

Verse 28 — Surah Ad-Dukhan 44:28

Kamar haka! Kuma Muka gadar da ita ga waɗansu mutane na dabam

Verse 29 — Surah Ad-Dukhan 44:29

Sa'an nan sama da ƙasa ba su yi kuka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba

Verse 30 — Surah Ad-Dukhan 44:30

Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun tsirar da Bani Isra'ila daga, azaba mai wulakantawa

Verse 31 — Surah Ad-Dukhan 44:31

Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin masu ɓarna

Verse 32 — Surah Ad-Dukhan 44:32

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun zaɓe su saboda wani ilmi (na Taurata) a kan mutane

Verse 33 — Surah Ad-Dukhan 44:33

Kuma Muka ba su, daga ayoyin mu'ujizoji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

Verse 34 — Surah Ad-Dukhan 44:34

Lalle waɗannan mutane*, haƙika, suna cewa

Verse 35 — Surah Ad-Dukhan 44:35

Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tayarwa ba

Verse 36 — Surah Ad-Dukhan 44:36

Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance masu gaskiya

Verse 37 — Surah Ad-Dukhan 44:37

shin, su ne mafifita ko kuwa mutanen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabaninsu? Mun halaka su, lalle su, sun kasance masu laifi

Verse 38 — Surah Ad-Dukhan 44:38

Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu ba, alhali kuwa Muna masu wasa

Verse 39 — Surah Ad-Dukhan 44:39

Ba Mu halitta su ba face da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba

Verse 40 — Surah Ad-Dukhan 44:40

Lalle ranar rarrabewa, ita ce lokacin wa'adinsu gaba ɗaya

Verse 41 — Surah Ad-Dukhan 44:41

Ranar da wani zumu ba ya amfanin wani zumu da kome kuma ba su zama ana taimakon su ba

Verse 42 — Surah Ad-Dukhan 44:42

face wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai

Verse 43 — Surah Ad-Dukhan 44:43

Lalle itaciyar zaƙƙum (ɗanyen wuta)

Verse 44 — Surah Ad-Dukhan 44:44

Ita ce abincin mai laifi

Verse 45 — Surah Ad-Dukhan 44:45

Kamar narkakken kwalta yana tafasa a cikin cikunna

Verse 46 — Surah Ad-Dukhan 44:46

Kamar tafasar ruwan zafi

Verse 47 — Surah Ad-Dukhan 44:47

(A ce wa mala'ikun wuta), "Ku kama shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahim

Verse 48 — Surah Ad-Dukhan 44:48

Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azabar ruwan zafi

Verse 49 — Surah Ad-Dukhan 44:49

(A ce masa), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwayi mai girma

Verse 50 — Surah Ad-Dukhan 44:50

Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kuna shakka game da shi

Verse 51 — Surah Ad-Dukhan 44:51

Lalle masu taƙawa suna cikin matsayi amintacce

Verse 52 — Surah Ad-Dukhan 44:52

A cikin gidajen Aljanna da maremari

Verse 53 — Surah Ad-Dukhan 44:53

Suna tufanta daga tufafin alharini raƙiƙi, da mai kauri, suna masu zaman fuskantar juna

Verse 54 — Surah Ad-Dukhan 44:54

Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mata masu kyawun idanu, masu girmansu

Verse 55 — Surah Ad-Dukhan 44:55

Suna kira, a cikinsu (gidejen) ga dukan 'ya'yan itacen marmari, suna amintattu (daga dukan abin tsoro)

Verse 56 — Surah Ad-Dukhan 44:56

Ba su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, face mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azabar Jahim

Verse 57 — Surah Ad-Dukhan 44:57

Saboda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma

Verse 58 — Surah Ad-Dukhan 44:58

Domin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ani) da harshenka, tsammaninsu, su riƙa tunawa

Verse 59 — Surah Ad-Dukhan 44:59

Sai ka yi jira. Lalle su, masu jira ne