Kuma da saɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rayar da ƙasa game da shi a bayan mutuwarta, da juyawar iskoki, akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali
Gaba gare su (a Lahira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sana'anta ba ya wadatar da su daga kome, kuma abubuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, ba su wadatar da su daga kome. Kuma suna da wata azaba mai girma
Kuma Ya hore muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gaba ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙiƙa, akwai ayoyi ga mutane waɗanda ke yin tunani
Ka ce wa waɗanda suka yi imani, su yi gafara ga waɗanda ba su fatan rahama ga kwanukan Allah, *domin (Allah) Ya saka wa mutane da abin da suka kasance suna aikatawa
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun bai* (wa Bani Isra'ila Littafi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abubuwa masudaɗi, Kuma Mun fifta su a kan mutanen duniya (a zamaninsu)
Kuma Muka ba su hujjoji na umarni. Ba su saɓa ba face bayan ilmi ya je musu, saboda zalunci a tsakaninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakaninsu, a Ranar ƙiyama a cikin abin da suka kasance suna saɓa wa (juna)
Ko waɗanda suka yagi miyagun ayyuka suna zaton Mu sanya su kamar waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rayuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntawa ya munana
Shin, ka ga wanda ya riƙi son zuciyarsa sih ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi,* Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zuciyarsa, kuma Ya sa wata yana a kan ganinsa? To, wane ne zai shiryar da shi bayan Allah? Shin to, ba za ku yi tunani ba
Kuma suka ce: "Babu kome face rayuwarmu ta duniya; muna mutuwa kuma muna rayuwa (da haihuwa) kuma babu abin da ke halaka mu sai zamani." Alhali kuwa (ko da suke faɗar maganar) ba su da wani ilmi game da wannan, ba su bin kome face zato
Kuma idan ana karanta ayoyin Mu bayyanannu a kansu, babu abin da ya kasance hujjarsu face suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance masu gaskiya
Ka ce: "Allah ne ke rayar* da ku kuma Shi ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tara ku zuwa ga Ranar ¡iyama, babu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba
Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shi kaɗai. Kuma ranar da Sa'a ke tsayuwa, a ranar nan masu ɓatawa (ga hujjojin Allah domin su ki bin shari'arSa) za su yi hasara
Kuma za ka ga kowace al'umma tana gurfane, kowace al'umma ana kiran ta zuwa ga littafinta. (A ce musu) "A yau ana saka muku da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Kuma amma waɗanda suka kafirta (Allah zai ce musu): "Shin, ayoyi Na ba su kasance ana karanta su a kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutane masu laifi
Kuma idan aka ce, lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, babu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cewa Sa'a ba, ba mu zato (game da ita) face zato mai rauni, Kuma ba mu zama masu yaƙni ba
Wancan domin lalle ku, kun riƙi ayoyin Allah da izgili, Kuma rayuwar duniya ta ruɗe ku. To, a yau ba za su fita daga gare ta ba, Kuma ba za su zama waɗanda ake neman yardarsu ba