Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakaninsu, face da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kafirta, masu bijirewa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi)
Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nuna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Ko kuwa suna da tarayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littafi na gabanin wannan (Alƙur'ani) ko wata alama daga wani ilmi, idan kun kasance masu gaskiya
Kuma wane ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da ba zai karɓa masa ba, bar Ranar Kyama, alhali su (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu
Kokuwa suna cewa: "Ya ƙirƙira shi (Alƙur'ani) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi ne, to ba ku mallaka mini kome daga Allah. Shi ne Mafi sani ga abin da kuke kutsawa a cikinsa na magana. (Allah) Ya isa Ya zama shaida a tsakaninada tsakaninku. Kuma shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Ka ce: "Ban kasance farau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da za a yi game da ni ko game da ku (na gaibi) ba, ba ni bin kome face abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, face mai gargaɗi mai bayyanawa
Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ani) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kafirta da shi, kuma wani mai shaida daga Bani Isra'ila ya bayar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi imani, kuma kuka kangare? Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce wa waɗanda suka yi imani: "Da (Alƙur'ani) ya kasance, wani alheri ne," da ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shi ba, to, za su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe
Alhali kuwa a gabaninsa akwai littafin Musa, wanda ya kasance abin koyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ani) littafi ne mai gaskatawa (ga littafin Musa), a harshe na Larabci domin ya gargaɗi waɗanda suka yi zalunci, kuma ya zama bushara ga masu kyautatawa
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum* game da mahaifansa biyu da kyautatawa, uwarsa ta yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yayensa wata talatin. Har a lokacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shekara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijina! Ka kange nidomin in gode wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifana biyu, kuma domin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle ni, na tuba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, ina daga masu sallamawa (ga umurninKa)
Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gafarta mafi munanan ayyukansum (suna) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance ana yi musu alkawari (da shi)
Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kuna tsoratar da ni cewa za a fitar da ni daga (kabari) ne, alhali kuwa ƙarnoni na mutane da yawa sun shuɗe a gabanina (ba su komo ba)?" Kuma su (mahaifan) suna neman Allah taimako (sunace masa) "Kaitonka! Ka yi imani, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan ba kome ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko
Waɗancan ne waɗanda kalmar azaba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummomi waɗanda suka shuɗe, (ba da daɗewa ba), a gabaninsu, daga aljannu da mutane. Lalle su, sun kasance masu hasara
Kuma ga kowane nau'i, yana da darajoji daga abinda suka aikata. Kuma domin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhali kuwa su, ba za a zalunce su ba
Kuma ranar da ake gitta waɗanda suka kaflrta a kan wuta (a ce musu): "Kun tafiyar da abubuwanku na jin daɗi a cikin rayuwarku ta duniya, kuma kun nemi jin dadi da su, to, ayau ana saka muka da azabar wulakanci, domin abin da kuka kasance kana yi na girman kai a cikin ƙasa, ba da wani hakki ba, kuma domin abin da kuka kasance kuna yi na fasiƙansi
Kuma ka ambaci ɗan'uwan* Adawa a lokacin da ya yi gargaɗi ga mutanensa, a Tuddan Rairayi, alhali kuwa waɗansu masu gargaɗi sun shuɗe agaba gare shi da baya gare shi (da cewa) "Kada ku bauta wa kowa face Allah. Lalle ni ina tsorata muku azabar yini mai girma
Suka ce: "Shin, ka zo mana ne domin ka karkatar da mu daga gumakaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan ka kasance daga masu gaskiya
To, a lokacin da suka ga azabar, kumar hadari mai fuskantar rafukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. A'a, shi na abin da kuke neman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun ba su iko ga abin da ba Muba ku iko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin ji da gani dazukata. Sai dai jnsu bai amfane su ba, kuma zukatansu ba su amfane su ba ga kome, domin sun kasance suna musu game da ayoyin Allah, kuma abin da suka kasance suna aikatawa na izgili game da shi ya wajaba* a gare su
To, don mene ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abubuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? A'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance suna ƙirƙirawa
Kuma a lokcin da Muka juya waɗansu jama'a na aljamiu* zuwa gare ka suna sauraren Alƙur'ani. To, alokacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙare, suka juya zuwa ga jama'arsu suna masu gargaɗi
Suka ce: "Ya mutanenmu! Lalle mu, mun ji wani littafi an saukar da shi a bayan Musa, mai gaskatawa ga abin da ke a gaba da shi, yana shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya
Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwaya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan suna a cikin ɓata bayyananna
Shin, kuma ba su gani ba cewa: "Lalle Allah, Wanda Ya halitta sammai da ƙasa kuma bai kasa ga halittarsu ba, Mai ikon yi ne a kan rayar da matattu?" Na'am, lalle Shi, Mai ikon yi ne a kan kome
Kuma ranar da ake gittar da waɗanda suka kafirta a kan wuta, (a ce musu) "Ashe, wannan ba gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azabar saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci
Saboda haka, ka yi haƙuri kamar yadda masu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggawa. Kamar dai su, a ranar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, face sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Babu), face mutane fasiƙai