Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi imani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhali kuwa shi ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Ya karkare musu miyagun ayyukansu, kuma Ya kyautata halayensu
Wannan kuwa saboda lalle, waɗanda suka kafirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi imani, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutane misalansu
Saboda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kafirta, sai ku yi ta dukan wuyoyinsu har a lokacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bayan' haka ko biyan fansa, har yaƙi ya saukar da kayansa masu nauyi. Wancan, da Allah na so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) domin Ya jarraba sashenku da sashe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah,* to, ba ai ɓatar da ayyukansu ba
Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, domin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabaninsu ta kasance? Allah Ya darkake a kansu. Kuma akwai misalan wannan aƙibar ga kafirai (na kowane zamani)
Lalle ne, Allah na shigar da waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidajen Aljanna, kogunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kafirta suna jin ɗan daɗi (aduniya) kuma suna ci, kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare su
Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa babu wani mai taimako a gare su
Misalin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga masu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu koguna na ruwa ba mai sakewa ba da waɗansu koguna na madara wadda ɗanɗanonta ba ya canjawa, da waɗansu koguna na giya mai daɗi ga mashaya, da waɗansu koguna na zuma tatacce kuma suna samu, a cikinta, daga kowane irin 'ya'yan itace, da wata gafara daga Ubangijinsu. (Shin, masu wannan ni'ima na daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wuta kuma an shayar da su wani ruwa mai zafi har ya kakkatse hanjinsu
Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare* zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mene ne (Muhammadu) ya faɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shafe haske daga zukatansu, kuma suka bi son zuciyoyinsu
Saboda hakaa ka sani, cewa babu abin bautawa face Allah, kuma ka nemi gafara ga zunubin, ka,* (kuma saboda muminai maza da muminai mata kuma Allah Ya san majuyaiku da mazauninku)
Kuma waɗanda suka yi imani suna cewa: "Don mene ne ba a saukar da wata sura ba? "To idan aka saukar da wata sura, bayyananna, kuma aka ambaci yaƙi a cikinta, za ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu suna kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da magagi saboda mutuwa. To, abin da yake mafifici a gare su
Wancan, domin lalle su sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗa'a ga sashen al'amarin," alhali kuwa Allah Yana sane da ganawarsu ta asiri
Kuma da Muna so, da lalle Mun nuna maka su. To, lalle kana sanin su game da alamarsu. Kuma lalle kana sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yana sanin ayyukanku
Lalle ne, waɗanda suka kafirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bayan shiriyar ta bayyana a gare su, ba za su cuci Allah da kome ba, kuma za Ya ɓata ayyukansu
Lalle ne waɗanda suka kafirta sa'an nan kuma suka kange (mutane) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhali kuwa suna kafirai, to, Allah ba zai yi gafara ba a gare su
Saboda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zuwaga sulhi alhali kuwa ku ne mafiɗaukaka kuma Allah na tare da ku, kuma ba, zai naƙasa muku ayyukanku ba
Rayuwar duniya, wasa da abin shagala kawai* ce, kuma idan kun yi imani, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kawo muku ijarorinku, kuma ba zai tambaye ku dukiyarku ba
Ga ku, ya ku waɗannan! Ana kiran ku domin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rowa. Kuma wanda ke yin rowa, to, yana yin rowar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadatacce alhali kuwa ku faƙirai ne. Kuma idan kuka juya (daga yi Masa ɗa'a), zai musanya waɗansu mutane waɗansunku sa'an nan ba za su kasance kwatankwacinku ba