Back to Languages
Hausa - Chapter 48
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Lalle Mu, Mun yi maka rinjaye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne
Verse 2
Domin Allah Ya shafe abin da ya gabata na laifinka* da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imar Sa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya
Verse 3
Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwayi
Verse 4
Shi ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukatan muminai domin su ƙara wani imani tare da imaninsu, alhali kuwa rundunonin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima
Verse 5
Domin Ya shigar da muminai maza da muminai mata gidajen Aljanna, kogunan ruwa na gudana daga ƙarƙashin gidajen, suna madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu munanan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia
Verse 6
Kuma Ya yi azaba ga munafikai maza da munafikai mata da mushirikai maza da musbirikai mata, masu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masifa mai kewayewa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta munana ta zama makoma (gare su)
Verse 7
Rundunonin sammai da ƙasa na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima
Verse 8
Lalle Mu Mun aike ka, kana mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma mai gargaɗi
Verse 9
Domin ku yi imani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) safiya da maraice
Verse 10
Lalle waɗanda ke yi maka mubaya'a,* Allah kawai ne suke yi wa mubaya'a, Hannun Allah na bisa hannayensu, saboda haka wanda ya warware, to, yana warwarewa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kawo masa ijara mai girma
Verse 11
Waɗanda aka bari daga ƙauyawa* za su ce maka, "Dukiyoyinmu da iyalanmu sun shagaltar da mu, sai ka nema mana gafara." Suna faɗa, da harsunansu, abin da ba shi ne a cikin zukatansu ba. Kace: "To, wane ne ke mallakar wani abu daga Allah saboda ku, idan Ya yi nufin wata cuta agare ku ko kuma (idan) Ya yi nufin wani amfani a gare ku? A'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatawa
Verse 12
A'a kun yi zaton Annabi da muminai, ba za su komo zuwa ga iyalansu ba, har abada. Kuma an ƙawata wannan (tunani) a cikin zukatanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutane halakakku
Verse 13
Kuma wanda bai yi imani da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mu, Mun yi tattalin wuta mai tsananin ƙuna, domin kafirai
Verse 14
Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne, Yana gafartawa ga wanda Yake so, kuma Yana azabta wanda Yake so alhali kuwa Allah Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Verse 15
Waɗanda aka bari za su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganimomi* domin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bi ku." Suna son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Ba za ku bi mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabanin haka." Sa'an nan za su ce: "A'a, kuna dai hassadar mu ne." A'a, sun kasance ba su fahimtar (abubuwa) sai kaɗan
Verse 16
Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyawa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutane* masu tsananin yaƙi (domin) ku yaƙe su ko kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗa'a, Allah zai kawo muku wata ijara mai kyau, kuma idan kuka juya baya kamar yadda kuka juya a gabanin wancan, zai azabta ku, azaba mai raɗadi
Verse 17
Babu laifi a kan makaho, kuma babu laifi a kan gurgu, kuma babu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗa'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidajen Aljanna, koguna na gudana daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya juya baya, (Allah) zai azabtashi, azaba mai raɗaɗi
Verse 18
Lalle ne haƙiƙa, Allah Ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya, a* a ƙarƙashin itaciyar nan domin Ya san abin da ke cikin zukatansu sai Ya saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya saka musu da wani cin nasara makusanci
Verse 19
Da waɗansu ganimomi masu yawa da za su karɓo su. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima
Verse 20
Kuma Allah Ya yi muku wa'adin waɗansu ganimomi masu yawa, waɗanda za ku karɓo su, kuma Ya gaggauta* muku wannan. Kuma Ya kange** hannayen mutane daga gare ku, kuma domin ta kasance wata aya ce ga muminai, kuma Ya shiryar da ku ga hanya madaidaiciya
Verse 21
Da waɗansu (ganimomin) *da ba ku da iko a kansu lalle Allah Ya kewaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kome
Verse 22
Kuma da waɗanda suka kafirta sun yake ku, da sun juyar da ɗuwaiwai (domin gudu) sa'an nan ba za su sami majiɓinci ba, kuma ba za su sami mataimaki ba
Verse 23
Hanyar Allah wadda ta shuɗe daga gabanin wannan, kuma ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah (ta taimakon muminai akan mai zaluntarsu)
Verse 24
Kuma Shi ne Ya kange hannayensu *daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bayan Ya rinjayar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatawa
Verse 25
Su ne waɗanda suka kafirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tana tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma ba domin waɗansu maza muminai da waɗansu mata muminai ba ba ku sansu ba ku taka su har wani aibi ya same ku daga gare su, ba da sani ba, (da Allah Ya yi muku iznin yaƙi), domin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamar Sa. Da (muminai) sun tsabbace da Mun azabtar da waɗanda suka kafirta daga gare su da azaba mai raɗiɗi
Verse 26
A lokacin da waɗanda suka kafirta suka sanya hananar ƙabi lanci a cikin zukatansu hananar ƙabilanci irin *na Jahiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan Manzon Sa, kuma da a kan muminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa** alhali kuwa sun kasance mafi dacewa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance Masani game da dukan kome
Verse 27
Lalle ne haƙiƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle za ku shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kuna masu natsuwa, masu aske kawunanku da masu sui suye, ba ku jin tsoro, domin (Allah) Ya san abin da ba ku sani ba, sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bayan wannan
Verse 28
Shi ne wanda Ya aiki Manzon Sa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai shaida
Verse 29
Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna masu ruku'i masu sujada, suna neman falala* daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda.** Wannan shi ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu, a cikin Injila ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafafunsa, yana bayar da sha'awa ga masu shukar' domin (Allah) Ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gafara da ijara mai girma