Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku* bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanawar sashenku ga sashe, domin kada ayyukanku su ɓaci, alhali kuwa ku ba ku sani ba
Lalle waɗanda ke runtsewar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Ya, jarrabi zukatansu ga taƙawa. Suna da wata irin gafara da ijara mai girma
Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan fasiƙi* Ya zo muku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, domin kada ku cuci waɗansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuna masu nadama
Kuma ku sani (cewa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Da Yana bin ku ga (halaye) masu Yawa na al'amarin, da kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Ya soyar da imani a gare ku, kuma Ya ƙawata shi a cikin zukatanku kuma Ya ƙyamantar da kafirci da fasicci da saɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifofin nan) su ne shiryayyu
Kuma idan jama'a biyu ta muminai suka yi yaki, to, kuyi sulhu, a tsakaninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zalunci a kan gudar, to, sai ku yaƙi wadda ke yin zalunci har ta koma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta koma, sai ku yi sulhu a tsakaninsu da adalci kuma ku daidaita.* Lalle Allah na son masu daidaitawa
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada waɗansu mutane su yi izgili game da waɗansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma waɗansu mata kada su yi izgili game da waɗansu mata mai yiwuwa ne su kasancc mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na laƙabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, waɗannan su ne azzalumai
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gulmar sashe. Shin, ɗayanku na son ya ci naman ɗan'uwansa yana matacce? To, kun ƙi shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tuba ne, Mai jin ƙai
Ya ku mutane!* Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabiloli, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafificinku a taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne, Mai ƙididdigewa
¡auyawa suka ce: "Mun yi imani." Ka ce: "Ba ku yi imani ba, amma dai ku ce, 'Mun miƙawuya, imani bai gama shiga a cikinzukatanku ba. Kuma idan kun yi ɗa'a ga Allah da Manzon Sa, to, ba zai rage muku kome daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Muminan gaskiya kawai, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihadi da dukiyarsu da kuma rayukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan su ne masu gaskiya
Ka ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhali kuwa Allah Ya san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kome
Suna yin gori a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gorin kun musulunta a kaina. A'a, Allah ne ke yi muku gori domin Ya shiryar da ku ga imani, idan kun kasance masu gaskiya