Back to Languages

Hausa - Chapter 50 - Qaf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Qaf 50:1

Ina rantsuwa da Alƙur'ani Mai girma

Verse 2 — Surah Qaf 50:2

A'a, sun yi mamaki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, ya zo musu, sai kafirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mamaki

Verse 3 — Surah Qaf 50:3

Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓaya (za a komo da mu)? Waccan komowa ce mai nisa

Verse 4 — Surah Qaf 50:4

Lalle ne Mun san abin da ƙasa ke ragewo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littafi mai tsarewa

Verse 5 — Surah Qaf 50:5

A'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lokacin da ta je musu, saboda haka suna a cikin wani al'amari mai raurawa

Verse 6 — Surah Qaf 50:6

Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga sama a bisa gare su, yadda Muka gina ta, kuma Muka ƙawace ta, kuma ba ta da waɗansu tsagogi

Verse 7 — Surah Qaf 50:7

Da ƙasa, Mun miƙe ta, kuma Mun jefa kafaffun duwatsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kowane ma'auri mai ban sha'awa

Verse 8 — Surah Qaf 50:8

Domin wayar da ido da tunatarwa ga dukan bawa mai tawakkali

Verse 9 — Surah Qaf 50:9

Kuma Mun sassakar, daga sama ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itacen) lambuna da ƙwaya abin girbewa

Verse 10 — Surah Qaf 50:10

Da itacen dabino dogaye, suna da'ya'yan itace gunda masu hauhawar juna

Verse 11 — Surah Qaf 50:11

Domin arziki ga bayi, kuma Muka rayar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake

Verse 12 — Surah Qaf 50:12

Mutanen Nuhu sun ƙaryata, a gabaninsu (mutanen yanzu) da ma'abuta Rassi, *da Samudawa

Verse 13 — Surah Qaf 50:13

Da Adawa da Fir'auna da 'yan'uwan Luɗu

Verse 14 — Surah Qaf 50:14

Da ma'abuta ƙunci *da mutanen Tubba'u,** kowanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacewaTa ta tabbata

Verse 15 — Surah Qaf 50:15

Shin, to, Mun kasa ne game da halittar farko? A'a, su suna a cikin rikici daga halitta sabuwa

Verse 16 — Surah Qaf 50:16

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswasi da shi, kuma Mu ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayensa

Verse 17 — Surah Qaf 50:17

A lokacin da masu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dama, kuma daga hagu akwai wani (mala'ika) zaunanne

Verse 18 — Surah Qaf 50:18

Ba ya lafazi da wata magana face a liƙe da shi akwai mai tsaro halartacce

Verse 19 — Surah Qaf 50:19

Kuma mayen mutuwa ya je da gaskiya. Wannan shi ne abin da ka kasance daga gare shi kana bijirewa

Verse 20 — Surah Qaf 50:20

Kuma aka hura a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacewar ne fa

Verse 21 — Surah Qaf 50:21

Kuma kowane rai ya zo, tare da shi akwai mai kora da mai shaida

Verse 22 — Surah Qaf 50:22

(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙiƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, saboda haka ganinka a yau, mai kaifi ne

Verse 23 — Surah Qaf 50:23

Kuma abokin haɗinsa* ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tare da ni halarce

Verse 24 — Surah Qaf 50:24

(A ce wa Mala'iku), "Ku jefa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kafirci, mai tsaurin rai

Verse 25 — Surah Qaf 50:25

Mai yawan hanawa ga alheri, mai zalunci, mai shakka

Verse 26 — Surah Qaf 50:26

Wanda ya sanya, tare da Allah wani abin bautawa na dabam, saboda haka kujefa shi a cikin azaba mai tsanani

Verse 27 — Surah Qaf 50:27

Abokin haɗinsa* ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nisa

Verse 28 — Surah Qaf 50:28

Ya ce: "Kada ku yi husuma a wur Nalhali Na gabatar da ƙyacewa zuwa gare ku

Verse 29 — Surah Qaf 50:29

Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zalunci ba ga bayi Na

Verse 30 — Surah Qaf 50:30

Ranar da Muke cewa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,* akwai wani ƙari

Verse 31 — Surah Qaf 50:31

Kuma a kusantar da Aljanna ga masu taƙawa, ba da nisa ba

Verse 32 — Surah Qaf 50:32

Wannan shi ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan komawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa)

Verse 33 — Surah Qaf 50:33

Wanda ya ji tsoron Mai rahama a fake, *kuma ya zo da wata irin zuciya mai tawakkali

Verse 34 — Surah Qaf 50:34

(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, *waccan ita ce ranar dawwama

Verse 35 — Surah Qaf 50:35

Suna da abin da suke so a cikinta, kuma tare da Mu akwai ƙarin ni'ima

Verse 36 — Surah Qaf 50:36

Kuma da yawa Muka halakar, a gabaninsu, (mutanen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) su ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasashe: 'Ko akwai wurin tsira'?* (Babu)

Verse 37 — Surah Qaf 50:37

Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunatarwa ga wanda zuciyarsa ta kasance gare shi, ko kuwa ya jefa sauraro, alhali kuwa yana halarce (da hankalinsa)

Verse 38 — Surah Qaf 50:38

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun halitta sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu, a cikin kwanaki shida, alhali wata'yar wahala ba ta shafe Mu ba

Verse 39 — Surah Qaf 50:39

Saboda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fada, kuma ka yi tasihi* game da gode wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabanin fitowar rana da gabanin ɓacewarta

Verse 40 — Surah Qaf 50:40

Kuma daga dare, sai ka yi tasbihi a gare Shi da bayan sujada

Verse 41 — Surah Qaf 50:41

Kuma ka saurara a ranar da mai kira ke yin kira daga wuri *makusanci

Verse 42 — Surah Qaf 50:42

Ranar da suke sauraron tsawa da gaskiya. Wancan shi ne yinin fita (daga kabari)

Verse 43 — Surah Qaf 50:43

Lalle Mu ne haƙiƙa, Mu ne ke rayarwa, kuma Mu ne ke kashewa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makomar take

Verse 44 — Surah Qaf 50:44

Ranar da ƙasa ke tsattsagewa daga gare su, suna masu gaggawa. Wancan tarawar mutane ne, mai sauƙi a gare Mu

Verse 45 — Surah Qaf 50:45

Mu ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma ba za ka zama mai tilasta su ba. Saboda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,* ga wanda ke tsoron ƙyacewaTa