Back to Languages

Hausa - Chapter 51 - Adh-Dhariyat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Adh-Dhariyat 51:1

Ina rantsuwa da iskoki masu shekar abubuwa, sheƙewa

Verse 2 — Surah Adh-Dhariyat 51:2

Sa'an nan da giragizai masu ɗaukar nauyi (na ruwa)

Verse 3 — Surah Adh-Dhariyat 51:3

Sa'an nan da jirage masu gudana (a kan ruwa) da sauƙi

Verse 4 — Surah Adh-Dhariyat 51:4

Sa'an nan da Mala'iku masu rabon al'amari (bisa umurnin Allah)

Verse 5 — Surah Adh-Dhariyat 51:5

Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙiƙa gaskiya ne

Verse 6 — Surah Adh-Dhariyat 51:6

Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙiƙa, mai aukuwa ne

Verse 7 — Surah Adh-Dhariyat 51:7

Ina rantsuwa da sama ma'abuciyar hanyoyi (na tafiyar taurari da sautin rediyo)

Verse 8 — Surah Adh-Dhariyat 51:8

Lalle ku, haƙiƙa, kuna cikin magana mai saɓa wa juna (game da Alƙur'ani)

Verse 9 — Surah Adh-Dhariyat 51:9

Ana karkatar da wanda aka juyar (daga gaskiya)

Verse 10 — Surah Adh-Dhariyat 51:10

An la'ani masu ƙiri-faɗi

Verse 11 — Surah Adh-Dhariyat 51:11

Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jahilci

Verse 12 — Surah Adh-Dhariyat 51:12

Suna tambaya: "Yaushe ne ranar sakamako za ta auku

Verse 13 — Surah Adh-Dhariyat 51:13

Ranar da suke a kan wuta ana fitinar su

Verse 14 — Surah Adh-Dhariyat 51:14

(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shi ne abin da kuka kasance kuna neman zuwansa da gaggawa

Verse 15 — Surah Adh-Dhariyat 51:15

Lalle masu taƙawa, suna a cikin lambunan itace da maremari

Verse 16 — Surah Adh-Dhariyat 51:16

Suna masu dibar abin da Ubangijinsu Ya ba su. Lalle su, sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka (a duniya)

Verse 17 — Surah Adh-Dhariyat 51:17

Sun kasance a lokaci kaɗan na dare suke yin barci

Verse 18 — Surah Adh-Dhariyat 51:18

Kuma a lokutan asuba suna ta yin istigfari

Verse 19 — Surah Adh-Dhariyat 51:19

Kuma a cikin dukiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai roƙo da wanda aka hana wa roƙo

Verse 20 — Surah Adh-Dhariyat 51:20

Kuma a cikin ƙasa akwai ayoyi ga masu yaƙini

Verse 21 — Surah Adh-Dhariyat 51:21

Kuma a cikin rayukanku (akwai ayoyi). To, ba za ku duba ba

Verse 22 — Surah Adh-Dhariyat 51:22

Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitowa) da abin da ake yi muku alkawari

Verse 23 — Surah Adh-Dhariyat 51:23

To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasa, lalle shi (abin da ake yi muku alkawari), haƙiƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kuna karantawa na magana

Verse 24 — Surah Adh-Dhariyat 51:24

Shin, labarin Baƙin Ibrahim, waɗanda aka girmama, ya zo maka

Verse 25 — Surah Adh-Dhariyat 51:25

A lokacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutane baƙi

Verse 26 — Surah Adh-Dhariyat 51:26

Sai ya juya zuwa ga iyalinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna

Verse 27 — Surah Adh-Dhariyat 51:27

Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Ba za ku ci ba

Verse 28 — Surah Adh-Dhariyat 51:28

Sai ya ji tsoro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsoro." Kuma suka yi masa bushara da (haihuwar) wani yaro mai ilmi

Verse 29 — Surah Adh-Dhariyat 51:29

Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallowa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsohuwa bakarariya (za ta haihu)

Verse 30 — Surah Adh-Dhariyat 51:30

Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shi, Shi ne Mai hikima, Mai ilmi

Verse 31 — Surah Adh-Dhariyat 51:31

(Ibraim) ya ce: "To mene ne babban al'almarinku, ya ku Manzanni

Verse 32 — Surah Adh-Dhariyat 51:32

Suka ce: "Lalle mu, an aike mu zuwa ga waɗansu mutane, masu laifi

Verse 33 — Surah Adh-Dhariyat 51:33

Domin mu saka musu waɗansu duwatsu na wani yumɓu (bom)

Verse 34 — Surah Adh-Dhariyat 51:34

Waɗanda aka yi wa alama daga wajen Ubangijinka, domin masu ɓarna

Verse 35 — Surah Adh-Dhariyat 51:35

Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga muminai

Verse 36 — Surah Adh-Dhariyat 51:36

Sai dai ba mu samu ba, a cikinta, face gida guda na Musulmi

Verse 37 — Surah Adh-Dhariyat 51:37

Kuma Muka bar wata aya, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsoron azaba, mai raɗaɗi

Verse 38 — Surah Adh-Dhariyat 51:38

Kuma ga Musa, a lokacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalili bayyananne

Verse 39 — Surah Adh-Dhariyat 51:39

Sai ya juya baya tare da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne ko kuwa mahaukaci

Verse 40 — Surah Adh-Dhariyat 51:40

Saboda haka, Muka kama shi tare da rundunarsa, sa'an nan Muka jefa su a cikin teku, alhali kuwa yana wanda ake zargi

Verse 41 — Surah Adh-Dhariyat 51:41

Kuma ga Adawa, a lokacin da Muka aika iska ƙeƙasasshiya a kansu

Verse 42 — Surah Adh-Dhariyat 51:42

Ba ta barin kome da ta je a kansa, face ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasusuwa

Verse 43 — Surah Adh-Dhariyat 51:43

Kuma ga Samudawa, a lokacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan daɗi har wani ɗan lokaci

Verse 44 — Surah Adh-Dhariyat 51:44

Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, saboda haka tsawa ta kama su, alhali kuwa suna kallo

Verse 45 — Surah Adh-Dhariyat 51:45

Ba su ko samu damar tsayawa ba, kuma ba su kasance masu neman agaji ba

Verse 46 — Surah Adh-Dhariyat 51:46

Da mutanen Nuhu a gabanin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutane ne fasiƙai

Verse 47 — Surah Adh-Dhariyat 51:47

Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhali kuwa lalle Mu ne Masu yalwatawa

Verse 48 — Surah Adh-Dhariyat 51:48

Kuma ƙasa Mun shimfiɗa ta, To, madalla da masu shimfiɗawa, Mu

Verse 49 — Surah Adh-Dhariyat 51:49

Kuma daga kome Mun halitta nau'i biyu, watakila za ku yi tunani

Verse 50 — Surah Adh-Dhariyat 51:50

Saboda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle ni mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

Verse 51 — Surah Adh-Dhariyat 51:51

Kuma kada ku sanya, tare da Allah wani abin bautawa na dabam, lalle ni, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

Verse 52 — Surah Adh-Dhariyat 51:52

Kamar haka dai wani Manzo bai je wa waɗanda ke gabaninsu ba face sun ce: "Mai sihiri ne ko mahaukaci

Verse 53 — Surah Adh-Dhariyat 51:53

shin, suna yi wa juna wasiyya da shi ne? A'a, su dai mutane ne masu girman kai

Verse 54 — Surah Adh-Dhariyat 51:54

Sai ka juya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne

Verse 55 — Surah Adh-Dhariyat 51:55

Kuma ka tunatar, domin tunatarwa tana amfanin muminai

Verse 56 — Surah Adh-Dhariyat 51:56

Kuma Ban halitta aljannu da mutane ba sai domin su bauta Mini

Verse 57 — Surah Adh-Dhariyat 51:57

Ba Ni nufln (samun) wani arziki daga gare su, Ba Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni

Verse 58 — Surah Adh-Dhariyat 51:58

Lalle Allah, Shi ne Mai azurtawa, Mai ikon yi, Mai cikakken ƙarfi

Verse 59 — Surah Adh-Dhariyat 51:59

To, lalle waɗanda suka yi zalunci suna da masaki (na ɗiban zunubi) kamar masakin abokansu, saboda haka kada su yi Mini gaggawa

Verse 60 — Surah Adh-Dhariyat 51:60

Saboda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kafirta, daga ranar su wadda aka yi musu alkawari