Back to Languages
Hausa - Chapter 53
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Ina rantsuwa da tauraron, a lokacin da ya faku
Verse 2
Ma'abucinku bai ɓata ba, kuma bai ƙetare haddi ba
Verse 3
Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa
Verse 4
(Maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa
Verse 5
(Mala'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi
Verse 6
Ma'abucin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita
Verse 7
Alhali kuwa yana a sararin sama mafi daukaka
Verse 8
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurowa
Verse 9
Har ya kasance gwargwadon zira'i biyu, ko kuma abin da ya fi kusa
Verse 10
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bawan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa)
Verse 11
Zuciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba
Verse 12
Shin, za ku yi masa musu a kan abin da yake gani
Verse 13
Kuma lalle ya gan shi, haƙiƙatan, a wani lokacin saukarsa
Verse 14
A wurin da magaryar tuƙewa take
Verse 15
A inda taken, nan Aljannar makoma take
Verse 16
Lokacin da abin da yake rufe magaryar tuƙewa ya rufe ta
Verse 17
Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba
Verse 18
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ayoyin Ubangijinsa
Verse 19
Shin, kun ga Lata da uzza
Verse 20
Da (wani gunki wai shi) Manata, na ukunsu
Verse 21
Ashe, ku ne da ɗa namiji Shi (Allah) kuma da ɗiya mace
Verse 22
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe
Verse 23
Waɗannan ba kome ba ne face sunaye, waɗanda kuka ambace su da su, ku da uwayenku. Allah bai saukar da wani dalili game da su ba. (Kafirai) ba su biyar kome face zato da abin da rayukansu ke so, Alhali kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta je musu (sai suka bar ta suka koma wa zaton)
Verse 24
Ko (an fai cewa) mutum zai sami abin da yake guri
Verse 25
To, Lahira da duniya na Allah kawai ne (wanda ya neme su daga wani, ya yi kuskure)
Verse 26
Akwai mala'iku da yawa a cikin sammai cetonsu ba ya wadatar da kome face bayan Allah Ya yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda
Verse 27
Lalle waɗannan da ba su yin imani da Lahira, haƙiƙa suna kiran mala'iku da sunan mace
Verse 28
Kuma ba su da wani ilmi game da shi, ba su bin kome face zato alhali kuwa lalle zato ba ya amfanar da kome daga gaskiya
Verse 29
Saboda haka sai ka kau da kai daga wanda ya juya baya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kome ba face rayuwar kusa (duniya)
Verse 30
Wannan ita ce iyakar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nemi shiriya
Verse 31
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa na Allah kawai ne, domin Ya saka wa waɗanda suka munana da abin da suka aikata, kuma Ya saka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau
Verse 32
Waɗanda ke nisantar manyan zunubai da abubuwan alfasha, face ƙananan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gafara ne, Shi ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lokacin da Ya ƙaga halittarku daga ƙasa, kuma a lokacin da kuke tayuna a cikin cikannan uwayenku. Saboda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shi ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa
Verse 33
Shin, ka ga wannan da ya juya baya
Verse 34
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa
Verse 35
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Saboda haka yana ganin gaibin
Verse 36
Ko kuwa ba a ba shi labari ba ga abin da yake a cikin Littafan Musa
Verse 37
Da Ibrahim wanda ya cika alkawari
Verse 38
Cewa wani rai mai kayan laifi ba ya ɗaukar kayan laifin wani
Verse 39
Kuma mutum ba shi da kome face abin da ya aikata
Verse 40
Kuma lalle, aikinsa za a gan shi
Verse 41
Sa'an nan a saka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni
Verse 42
Kuma lalle, makomar zuwa Ubangijinka kawai take
Verse 43
Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kuka
Verse 44
Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya kashe, kuma Ya rayar
Verse 45
Kuma lalle Shi ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace
Verse 46
Daga wani ɗigon ruwa guda a lokacin da ake jefa shi a cikin mahaifa
Verse 47
Kuma a kansa ne ƙaga halitta ta biyu take
Verse 48
Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya azurta, kuma Ya wadatar
Verse 49
Kuma lalle, Shi, Shi ne Ubangijin Shi'ira
Verse 50
Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya halaka Adawa na farko
Verse 51
Da Samudawa, sa'an nan bai rage su ba
Verse 52
Da mutanen Nuhu a gabanin haka, lalle su sun kasance mafi zalunci kuma mafi girman kai
Verse 53
Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kayar da su
Verse 54
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su
Verse 55
To, da wace daga ni'imomin Ubangijinka kake *yin shakka
Verse 56
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin masu gargaɗi na farko
Verse 57
Makusanciya* fa, ta yi kusa
Verse 58
Babu wani rai, banda Allah, mai iya bayani gare ta
Verse 59
Shin, kuma daga wannan *labari kuke mamaki
Verse 60
Kuma kuna yin dariya, kuma ba ku yin kuka
Verse 61
Alhali kuna masu wasa
Verse 62
To, ku yi tawali'u *ga Allah, kuma ku bauta (masa)