Back to Languages

Hausa - Chapter 55

Translation by Abubakar Mahmood Jummi

Verse 1

(Allah) Mai rahama

Verse 2

Ya sanar da Alƙur'ani

Verse 3

Ya halitta mutum

Verse 4

Ya sanar da shi bayani (magana)

Verse 5

Rana da wata a kan lissafi suke

Verse 6

Kuma tsirrai masu yaɗo da itace suna tawalu'i

Verse 7

Kuma sama Ya ɗaukaka ta, Kuma Ya aza sikeli

Verse 8

Domin kada ku karkatar da sikelin

Verse 9

Kuma ku daidaita awo da adalci, kuma kada ku rage sikelin

Verse 10

Kuma ƙasa Ya aza ta domin talikai

Verse 11

A cikinta akwai 'ya'yan itacen marmari da dabino mai kwasfa

Verse 12

Da ƙwaya mai soshiya da ƙamshi

Verse 13

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangjinku *kuke ƙaryatawa

Verse 14

Ya halitta mutum daga ƙekasasshen yumɓu kumar kasko

Verse 15

Kuma ya halitta aljani daga bira daga wuta

Verse 16

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 17

Ubangjin mafita biyu na rana, kuma Ubangijin mafaɗa biyu na rana

Verse 18

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 19

Ya garwaya teku biyu (ruwan daɗi da na zartsi) suna haɗuwa

Verse 20

A tsakaninsu akwai shamaki, ba za su ƙetare haddi ba

Verse 21

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 22

Lu'ulu'u da murjani na fita daga gare su

Verse 23

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 24

Kuma Yana da manyan jirage, waɗanda ake ƙagawa a cikin teku kamar manyan duwatsu

Verse 25

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 26

Dukkan wanda ke kanta* mai ƙarewa ne

Verse 27

Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa

Verse 28

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 29

wanda ke a cikin sammai da ƙasa yana roƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani

Verse 30

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 31

Za mu ɗauki lokaci saboda ku, ya ku *masu nauyin halitta biyu

Verse 32

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 33

Ya jama'ar aljannu da mutane! Idan kuna iya zarcewa daga sasannin sammai da ƙasa to ku zarce. Ba za ku iya zarcewaba face da wani dalili

Verse 34

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 35

Ana sako wani harshe daga wata wuta a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, ba za ku nemi taimako ba

Verse 36

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 37

Sa'an nan idan sama ta tsage kuma ta zama ja kamar jar fata

Verse 38

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 39

To, a ran nan ba za a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani

Verse 40

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 41

za a iya sanin masu laifi da alamarsu, saboda haka sai a kama kwarkaɗarsu da sawayensu

Verse 42

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 43

Wannan Jahannama ce wadda masu laifi ke ƙaryatawa game da ita

Verse 44

Suna kewaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa

Verse 45

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 46

Kuma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga Ubangijinsa yana da Aljanna biyu

Verse 47

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 48

Masu rassan itace

Verse 49

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 50

A cikinsu akwai maremari biyu suna gudana

Verse 51

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 52

A cikinsu akwai nau'i biyu daga kowane 'ya'yan itacen marmari

Verse 53

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 54

Suna gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufafin alharini mai kauri ne kuma nunannun 'ya'yan itacen Aljannar biyu kusakusa suke

Verse 55

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 56

A cikinsu akwai mata masu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani

Verse 57

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 58

Kamar dai su yaƙutu ne da murjani

Verse 59

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 60

Shin, kyautatawa na da wani sakamako? (A'aha) face kyautatawa

Verse 61

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 62

Kuma baicinsu akwai waɗansu gidajen Aljanna biyu

Verse 63

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 64

Masu duhun inuwa

Verse 65

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 66

A cikinsu akwai maremari biyu masu kwararar ruwa

Verse 67

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 68

A cikinsu akwai 'ya'yan itacen marmari da dabino darummani

Verse 69

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 70

A cikinsu, akwai wasu mata masu kyawun halaye, masu kyaun halitta

Verse 71

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 72

Masu farin idanu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimomi

Verse 73

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 74

Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani

Verse 75

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 76

Suna gincire a kan wasu matasai masu koren launi da katifun Abkara kyawawa

Verse 77

To, saboda wanne daga ni'imomin Ubangijinku, kuke ƙaryatawa

Verse 78

Sunan Ubangjinka, Mai girman Jalala da Karimci, ya tsarkaka