Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske*, sa'an nan kuma waɗanda suka kafirta, da Ubangijinsu suke karkacewa
Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabaninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tana ta zuba, kuma Muka sanya koguna suna gudana daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halaka su saboda zunubansu kuma Muka ƙaga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu
Kuma da Mun sassaukar da wani littafi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle da waɗanda suka kafirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne
Suka ce: "Don me ba a saukar da wani mala'ika ba a gare shi?" to da Mun saukar da mala'ika haƙiƙa da an hukunta al'amarin* sa'an nan kuma ba za a yi musu jinkiri ba
Ka ce: "Na wane ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Ya wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yana tara ku zuwa ga Ranar ¡iyama, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasarar rayukansu, to, su ba za su yi imani ba
Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhali Allah ne) Mai ƙaga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yana ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne ni, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga masu shirki
Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakanina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ani domin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda labari ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙiƙa, kuna shaidar cewa, lalle ne tare da Allah akwai wasu abubuwan bautawa?" Ka ce: "Ba zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautawa Guda kuma lalle ne ni barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirka
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurare gare ka. Kuma Mun sanya abubuwan rufi a kan zukatansu domin kada su fahimce shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kowace aya ba za su yi imani da ita ba har idan sunje maka suna jayayya da kai, waɗanda suka kafirta suna cewa: "Wannan bai zama ba face tatsuniyoyin mutanen farko
Kuma da kana gani, a lokacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Ya kaitonmu! Da ana mayar da mu, kuma ba za mu ƙaryata ba daga ayoyin Ubangijinmu, kuma za mu kasance Daga muminai
A'aha, abin da suka kasance suna ɓoyewa, daga gabani, ya bayyana a gare su. Kuma da an mayar da su, lalle da sun koma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne su, haƙiƙa, maƙaryata ne
Kuma da kana gani, a lokacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Na'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci
Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Ya nadamarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhali kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka ya munana
Lalle ne Muna sani cewa haƙiƙa, abin da suke faɗa yana ɓata maka rai. To, lalle ne su, ba su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzalumai da ayoyin Allah suke musu
Kuma lalle ne, haƙiƙa, an ƙaryata manzanni daga gabaninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cutar da su, har taimakon Mu ya je musu, kuma babu mai musanyawa ga kalmomin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga labarin (annabawan) farko
Kuma idan ya kasance cewa finjirewarsu ta yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyawa, ka nemi wani ɓullo a cikin ƙasa, ko kuwa wani tsani a cikin sama domin ka zo musu da wata aya, (sai ka yi). Kuma da Allah Ya so haƙiƙa da Yatara su a kan shiriya. Saboda haka, kada lalle ka kasance daga jahilai
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da aya ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai iko ne a kan Yasaukar da aya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba
Kuma babu wata dabba a cikin ƙasa kuma babu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa face al'umma ne misalanku. Ba Mu yi sakacin barin kome ba a cikin Littafi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tara su
Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ayoyin Mu, kurame ne kuma bebaye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yana ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya
Ka ce: "Shin, kun gan ku, idan azabar Allah ta zo muku, ko Sa'ar Tashin Kiyama ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance masu gaskiya
To, don me, a lokacin da tsananin Mu ya je musu ba su yi tawalu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙeƙashe kuma shaiɗan ya ƙawata musu abin da suka kasance suna aikatawa
Sa'an nan kuma alokacin da suka manta da abin da aka tunatar da su da shi, sai Muka buɗe, a kansu, ƙofofin dukkan kome, har a lokacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kama su, kwatsam, sai ga su sun yi tsuru tsuru
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hatimi a kan zukatanku, wane abin bauttawa ne, wanin Allah, zai je muku da shi?" Ka duba yadda Muke sarrafaayoyi, Sa'an nan kuma su, suna finjirewa
Kuma ba Mu aikawa da manzanni face masu bayar da bushara, kuma masu gargaɗi. To, wanda ya yi imani kuma yagyara aiki, to, babu tsoro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki
Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskokin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cewa ni mala'ika ne. Ba ni bi, face abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makaho da mai gani suna daidaita? Shin fa, ba ku yin tunani
Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsoron a tara su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masoyi baicin Sa, kuma babu mai ceto, tsammaninsu, suna yin taƙawa
Kuma kada ka kori waɗanda* suke kiran Ubangijinsu safe da maraice, suna nufin yardarSa, babu wani abu daga hisabinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisabinka a kansu, har ka kore su ka kasance daga azzalumai
Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sashensu da sashe, domin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakaninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga masu godiya
Kuma idan waɗanda suke yin imani da ayoyinMu suka je maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cewa lalle ne wanda ya aikata aibi da jahilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tuba daga bayansa, kuma ya gyara, to, lalle Shi, Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zuciyoyinku, (domin in na yi haka) lalle ne, na ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba
Ka ce: "Lalle ne ina kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke neman gaugawarsa, ba ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba face, ga Allah, Yana bayar da labarin gaskiya, kuma shi ne mafi alherin masu rarrabewa
Ka ce: "Lalle ne, da a wurina akwai abin da kuke neman gaugawa da shi, haƙiƙa da an hukunta al'amarin, a tsakanina da tsakaninku, kuma Allah Shi ne Mafi sani ga azzulumai
Kuma a wurin Sa mabudan* gaibi suke, babu wanda yake sanin su face Shi, kuma Yana sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya faɗuwa, face Ya san shi, kuma babu wata ƙwaya a cikin duffan ƙasa, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙeƙasasshe, face yana a cikin wani Littafi mai bayyanawa
Kuma Shi ne wanda Yake karɓar* rayukanku da dare, kuma Yana sanin abin da kuka yaga da rana, sa'an nan Yana tayar da ku a cikinsa, domin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makomarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku labari da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Kuma Shi ne Mai rinjaya bisa ga bayinSa, kuma Yana aikan masu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta je wa ɗayanku, sai manzannin Mu su karɓi ransa alhali su ba su yin sakaci
Ka ce: "Wane ne Yake tsirar da ku daga duhuhuwan tududa ruwa, kuna kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓoye: 'Lalle ne idan Ka tsirar da mu daga wannan (masifa), haƙiƙa, muna kasancewa daga masu godiya
Ka ce: "Shi ne Mai iko a kan Ya aika da wata azaba a kanku daga bisanku, ko kuwa daga ƙarƙashin ƙafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku ƙungiyoyi, kuma Ya ɗanɗana wa sashenku masifar sashe." "Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsammaninsu suna fahimta
Kuma idan ka ga waɗanda suke kutsawa a cikin ayoyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kutsa a cikin wani labari waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunawa tare da mutane azzalumai
Kuma babu wani abu daga hisabinsu (masu kutsawa a cikin ayoyin Allah (a kan masu taƙawa amma akwai tunatarwa (a kansu), tsammaninsu (masu kutsawar) za su yi taƙawa
Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addininsu abin wasa* da wargi alhali rayuwar duniya ta ruɗe su, kuma ka tunatar game da shi (Alƙur'ani): Kada a jefa raia cikin halaka saboda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai ceto; kuma, ko ya daidaita dukan fansa, ba za a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammani saboda abin da suka tsirfanta; suna da wani abin sha daga ruwan zafi, da wata azaba mai raɗaɗi, saboda abin da suka kasance suna yi na kafirci
Ka ce: "Shin, za mu yi kiran abin da ba ya amfaninmu, baicin Allah, kuma ba ya cutar damu, kuma a mayar da mu a kan dugaduganmu, a bayan Allah Ya shiryar da mu kamar wanda shaiɗanu suka kayar da shi a cikin ƙasa, yana mai ɗimuwa, yana da abokaisuna kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"* Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin talikai
Kuma Shi ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Ranar da Yake cewa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancewa. Maganar Sa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Ranar da ake busa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani
Kuma a lokacin da Ibrahima ya ce wa ubansa Azara: "Shin, kana riƙon gumaka abubuwan bautawa? Lalle ni, ina ganin ka kai damuta- nenka, a cikin ɓata bayyananniya
To, a lokacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani tauraro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lokacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son masu faɗuwa
Sa'an nan a lokacin da ya ga wata yana mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lokacin da ya faɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙiƙa, ina kasancewa daga mutane ɓatattu
Sa'an nan a lokacin da ya ga rana tana bayyana, ya ce: "Wannan shi ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lokacin da ta faɗi, ya ce: "Ya mutanena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki
Kuma mutanensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kuna musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhali kuwa Ya shiryai da ni? Kuma ba ni tsoron abin da kuke yin shirki da shi, face idan Ubangijina Ya so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kome da ilmi. Shin, ba za ku yi tunani ba
Kuma yaya nake jin tsoron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsoron cewa lalle ne ku, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sashen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kuna sani
Kuma waccan ita ce hujjar Mu, Mun bayar da ita ga Ibrahima a kan mutanensa. Muna ɗaukaka wanda Muka so da darajoji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani
Kuma Muka ba shi Is'haƙa da Yaƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nuhu Mun shiryar da shi a gabani, kuma daga zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimanu da Ayyuba, da Yusufu da Musa da Haruna, kuma kamar wancan ne Muke saka wa masu kyautatawa
Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littafi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutane) sun kafirta da ita, to, haƙiƙa, Mun wakkala wasu mutane gare ta, ba su zama game da ita kafirai ba
Waɗancan ne Allah Ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijara. Shi (Alƙur'ani) bai zama ba face tunatarwa ga talikai
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lokacin da suka ce: "Allah bai saukar da kome ba ga wani mutum." Ka ce: "Wane ne ya saukar da Littafi wanda Musa ya zo da shi, yana haske da shiriya ga mutane, kuna sanya shi takardu, kuna bayyana su, kuma kuna ɓoye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah,"* sa'an nan ka bar su a cikin sharholiyarsu suna wasa
Kuma wannan Littafi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma domin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin imani da Lahira suna imani da shi (Alƙur'ani), kuma su, a kan sallarsu, suna tsarewa
Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, ko kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhali kuwa ba a yi wahayin kome ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misalin abin da Allah Ya saukar?" Kuma da ka gani, a lokacin da azzalumai suke cikin mayen mutuwa, kuma mala'iku suna masu shimfiɗa hannuwansu, (suna ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau ana saka muku da azabar wulaƙanci saboda abin da kuka kasance kuna faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ayoyinSa kuna yin girman kai
Kuma lalle ne haƙiƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lokaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tare da ku ba, macetanku waɗanda kuka riya cewa lalle ne su, a cikinku masu tarayya ne. Lalle ne, haƙiƙa, kome ya yanyanke a tsakaninku, kuma abin da kuka kasance kuna riyawa ya ɓace daga gare ku
Lalle ne, Allah ne Mai tsagewar ƙwayar hatsi da kwalfar gurtsu. Yana fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai,* wannan ne Allah. To, yaya ake karkatar da ku
Kuma Shi ne Ya ƙaga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajewa. Lalle ne Mun bayyana ayoyi daki-daki, ga mutane waɗanda suke fahimta
Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kome game da shi, sa'an nan Muka fitar da kore daga gare shi, Muna fitar da kwaya ɗamfararriya daga gare shi (koren),* kuma daga dabino daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gonaki na inabobi da zaituni da rummani, masu kama da juna da wasun masu kama da juna. Ku duba zuwa 'ya'yan itacensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ayoyi ga waɗanda suke yin imani
Kuma suka sanya wa Allah abokan tarayya, aljannu, alhali kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'ya'ya, ba da ilmi ba. TsarkinSa ya tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantawa
Mafarin* halittar sammai da ƙasa. Yaya ɗa zai zama a gare Shi alhali kuwa mata ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kome, kuma Shi, game da dukan kome, Masani ne
Lalle ne abubuwan lura sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, domin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yana a kansa, kuma ni, a kanku, ba mai tsaro ba ne
Kuma kada ku zagi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zagi Allah bisa zalunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawata ga kowace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makomarsu take, sa'an nan Ya ba su labari da abin da suka kasance suna aikatawa
Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwoyinsu (cewa) lalle ne idan wata aya ta jemusu, haƙiƙa, suna yin imani da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ayoyi a wurin Allah suke. Kuma mene nezai sanya ku ku sansance cewa, lalle ne su, idan ayoyin sun je, ba za su yi imani ba
Kuma da a ce, lalle Mu Mun saukar da Mala'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tara dukkan kome a kansu, gungu-gungu, ba su kasance suna iya yin imani ba, sai fa idan Allah Ya so, Kuma amma mafi yawansu suna jahiltar haka
Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kowane Annabi maƙiyi; shaiɗanun mutane da aljannu, sashensu yana yin ishara* zuwa sashe da ƙawataccen zance bisa ga ruɗi. Kuma da Ubangijinka Ya so, da ba su aikata shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirawa
Kuma domin zukatan waɗanda ba su yi imani da Lahira ba su karkata saurare zuwa gareshi, kuma domin su yarda da shi, kuma domin su kamfaci abin da suke masu kamfata
Shin fa, wanin Allah nake nema ya zama mai hukunci, alhali kuwa Shi ne wanda Ya saukar muku da Littafi abin rabewadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littafi suna sanin cewa lalleshi (Alƙur'ani) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Saboda haka kada ku kasance daga masu shakka
Kuma mene ne ya same ku, ba za ku ci ba daga abin da aka ambaci sunan Allah a kansa, alhali kuwa, haƙiƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, face fa abin da aka bukatar da ku bisa lalura zuwa gare shi? Kuma lalle ne masu yawa suna ɓatarwa, da son zuciyoyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga masu ta'addi
Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sunan Allah ba a kansa.* Kuma lalle ne shi fasiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗanu, haƙiƙa, suna yin ishara zuwa ga masoyansu, domin su yi jayayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗa'a, lalle ne ku, haƙiƙa, masu shirki ne
Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rayar da shi, kuma Muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi, yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa
Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kowace alƙarya, shugabanni su ne masu laifinta domin su yi makirci a cikinta, alhali kuwa ba su yin makirci face ga rayukansu, kuma ba su sansancewa
Kuma idan wata aya ta je musu sai su ce: "Ba za mu yi imani ba, sai an kawo mana kamar abin da aka kawo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.* Wani wulaƙanci** a wurin Allah da wata azaba mai tsanani za su sami waɗanda suka yi laifi, saboda abin da suka kasance suna yi na makirci
Domin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya buɗa ƙirjinsa domin Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yana takawa* ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyawar ƙazanta a kan waɗanda ba su yin imani
Kuma ranar da yake tara su gaba ɗaya (Yana cewa): "Ya jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutane." Kuma majiɓantansu daga mutane suka ce: "Ya Ubangjinmu! Sashenmu* ya ji daɗi da sashe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kuna madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani
Ya jama'ar aljannu da mutane! Shin, manzanni daga gare ku ba su je muku ba suna labarta ayoyiNa a kanku, kuma suna yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini naku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kawunanmu." Kuma rayuwar duniya ta ruɗe su. Kuma suka yi shaida a kan kawunansu cewa lalle ne su, sun kasance kafirai
Kuma Ubangijinika Wadatacce* ne Ma'abucin rahama. Idan Ya so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bayanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙaga halittarku daga zuriyar wasu mutane na dabam
Ka ce: "Ya ku mutanena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne ni mai aiki ne, sa'an nan da sannu za ku san wanda aƙibar gida za ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzalumai ba za su ci nasara ba
Kuma sun sanya wani rabo ga Allah daga abin da Ya halitta daga shuka da dabbobi, sai suka ce: "Wannan* na Allah ne," da riyawarsu "Kuma wannan na abubuwan shirkinmu ne." Sa'an nan
Kuma kamar wancan ne abubuwan shirkinsu suka ƙawata wa masu yawa, daga masu shirkin; kashewar* 'ya'yansu, domin su halaka su kuma domin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma da Allah Ya so da ba su aikata shi ba. Saboda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirawa
Kuma sukace: "Waɗannan dabbobi da shuka hanannu ne; babu mai ɗanɗanar su face wanda muke so," ga riyawarsu. Da wasu dabbobi an hana bayayyakinsu, da wasu dabbobi ba su ambatar sunan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai saka musu da abin da suka kasance suna ƙirƙirawa
Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbobi keɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan matan aurenmu. Kuma idan ya kasance mushe, to, a cikinsa su abokan tarayya ne, zai saka musu sifantawarsu. Lalle ne Shi, Mai hikima ne, Masani
Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu saboda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasara! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba
Kuma Shi ne Wanda Ya ƙaga halittar gonaki masu rumfuna da wasun masu rumfuna da dabinai da shuka, mai saɓawa ga 'ya'yansa na ci, da zaituni da rummani mai kama da juna da wanin mai kama da juna. Ku ci daga 'ya'yan itacensa, idan ya yi 'ya'yan, kuma ku bayar da hakkinSa a ranar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shi, ba Ya son mafarauta
Kuma daga dabbobi (Ya ƙaga halittar) mai ɗaukar kaya da ƙanana; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyoyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne
Nau'o'i takwas daga tumakai biyu, kuma daga awakai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko matan biyu, ko abin da mahaifar matan biyu suka tattara a kansa? Ku ba ni labari da ilmi, idan kun kasance masu gaskiya
Kuma daga raƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shanu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko matan biyu Ya hana, ko abin da mahaifar matan biyu suka tattara a kansa? Ko kun kasance halarce ne a lokacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, domin ya ɓatar da mutane ba da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah ba Ya shiryar da mutane Azzalumai
Ka ce: "Ba ni samu,* a cikin abin da aka yo wahayi zuwa gare Ni, abin haramtawa a kan wani mai ci wanda yake cin sa face idan ya kasance mushe ko kuwa jini abin zubarwa ko kuwa naman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, ko kuwa fasiƙanci wanda aka kururuta, domin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larura ta kama shi, ba mai fita jama'a ba, kuma ba mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Kuma a kan waɗanda suka tuba (Yahudu) Mun haramta *dukan mai akaifa, kuma daga shanu da bisashe Mun haramta musu kitsattsansu face abin da bayukansu suka ɗauka, ko kuwa kayan ciki, ko kuwa abin da ya garwaya da ƙashi wannan ne Muka saka musu saboda zaluncinsu, kuma Mu, haƙiƙa, Masu gaskiya ne
Waɗanda suka yi shirki* za su ce: "Da Allah Ya so da ba mu yi shirki ba, kuma da ubanninmu ba su yi ba, kuma da ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutanen da suke a gabaninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azabarMu. Ka ce: "Shin, kuna da wani ilmi a wurinku domin ku fito mana da shi? Ba ku bin kome face zato kuma ba ku zama ba face ƙiri-faɗi kawai kuke yi
Ka ce: "Ku kawo shaidunku, waɗanda suke bayar da shaidar cewa Allah ne Ya haramta wannan." To idan sun kawo shaida kada ka yi shaida tare da su. Kuma kada ka bi son zuciyoyin waɗanda suka ƙaryata, game da ayoyinMu, da waɗanda ba su yin imani da Lahira, alhali kuwa su daga Ubangijinsu suna karkacewa
Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin kome da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatawa, kuma kada ku kashe ɗiyanku saboda talauci, Mu ne Muke azurta ku, ku da su, kuma kada ku kusanci abubuwa alfasha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓoyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, face da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammaninku, kuna hankalta
Kada ku kusanci dukiyar maraya face da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mudu da sikeli da adalci, ba Mu kallafa wa rai face iyawarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi adalci, kuma ko da ya kasance ma'abucin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammaninku, kuna tunawa
Kuma lalle wannan ne tafarkiNa, yana madaidaici: Sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi, su rarrabu da ku daga barin hanyaTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammaninku, kuna yin taƙawa
Sa'an nan kuma Mun bai wa Musa Littafi, yana cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabewa, daki-daki, ga kowane abu, da shiriya da rahama, tsammaninsu,* suna yin imani da haɗuwa da Ubangijinsu
(Domin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littafi a kan ƙungiya* biyu daga gabaninmu, kuma lalle ne mu, mun kasance, daga karatunsu, haƙiƙa, gafilai
Ko kuwa ku ce: "Da dai lalle mu an saukar da Littafi a kanmu, haƙiƙa, da mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, ta zo muku, da shiriya da rahama. To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙaryata game da ayoyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Za Mu saka wa waɗanda suke finjirewa daga barin ayoyinMu da mugunyar azaba, saboda abin da suka kasance suna yi na hinjirewa
Shin, suna jiran (wani abu), face dai mala'iku* su je musu ko kuwa Ubangijinka Ya je, ko kuwa sashen ayoyin Ubangijinka ya je. A ranar da sashen ayoyin Ubangijinka yake zuwa, imanin rai wanda bai kasance ya yi imanin ba a gabani, ko kuwa ya yi tsiwirwirin wani alheri, ba ya amfaninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mu, masu jira ne
Lalle ne waɗanda* suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kome: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya ba su labari game da abin da suka kasance suna aikatawa
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yana da goma ɗin misalansa. Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to, ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su
Ka ce: "Lalle ni, Ubangijina Ya shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addini, ƙimantawa (ga abubuwa), mai aƙidar Ibrahim, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirki ba
Ka ce: "Shin wanin Allah nake nema ya zama Ubangiji, alhali kuwa Shi ne Ubangijin dukan kome? Kuma wani rai ba ya yin tsirfa face domin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, ba ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma komawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kuna saɓa wa juna
Kuma Shi ne wanda Ya sanya ku masu maye wa junaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji; domin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya ba ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggawar uƙkuba ne, kuma lalle ne Shi, haƙiƙa, Mai gafara ne, Mai jin ƙai