Back to Languages

Hausa - Chapter 7 - Al-Araf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Araf 7:1

Verse 2 — Surah Al-Araf 7:2

Littafi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, domin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunatarwa ne ga muminai

Verse 3 — Surah Al-Araf 7:3

Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunawa

Verse 4 — Surah Al-Araf 7:4

Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azabarMu ta je mata da dare ko kuwa suna masu ƙailula

Verse 5 — Surah Al-Araf 7:5

Sa'an nan babu abin da yake da'awarsu, a lokacin da azabarMu ta je musu, face suka ce: "Lalle ne mu muka kasance masu zalunci

Verse 6 — Surah Al-Araf 7:6

Sa'an nan lalle ne Muna tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Muna tambayar Manzannin

Verse 7 — Surah Al-Araf 7:7

Sa'an nan haƙiƙa Muna ba su labari da ilmi kuma ba Mu kasance masu fakowa ba

Verse 8 — Surah Al-Araf 7:8

Kuma awo a ranar nan ne gaskiya. To, wanda sikelansasuka yi nauyi, to, waɗannan su ne masu cin nasara

Verse 9 — Surah Al-Araf 7:9

Kuma wanda sikelansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, saboda abin da suka kasance, da ayoyinMu, suna yi na zalunci

Verse 10 — Surah Al-Araf 7:10

Kuma lalle ne haƙiƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abubuwan rayuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke godewa

Verse 11 — Surah Al-Araf 7:11

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun halitta ku sa'an nan kuma Mun suranta ku, sa'an nan kumaMun ce wa mala'iku: "Ku yi sujada ga Adam." Sai suka yi sujada face Iblis, bai kasance daga masuyin sujadar ba

Verse 12 — Surah Al-Araf 7:12

Ya ce: "Mene ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alokacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Ni ne mafifici daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhali kuwa Ka halitta shi daga laka

Verse 13 — Surah Al-Araf 7:13

Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; domin ba, ya kasancewa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kana daga masu ƙasƙanci

Verse 14 — Surah Al-Araf 7:14

Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga ranar da ake tayar* da su

Verse 15 — Surah Al-Araf 7:15

Ya ce: "Lalle ne, kana daga waɗanda aka yi wa jinkiri

Verse 16 — Surah Al-Araf 7:16

Ya ce: "To ina rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, ina zaune musu tafarkinKa madaidaici

Verse 17 — Surah Al-Araf 7:17

Sa'an nan kuma haƙiƙa, Ina je musu daga gaba gare su, kuma daga baya gare su, kuma daga jihohin damansu da jihohin hagunsu; Kuma ba za ka sami mafi yawansu masu godiya ba

Verse 18 — Surah Al-Araf 7:18

Ya ce: "Ka fita daga gare ta kana abin zargi korarre. Lalle ne wanda ya bi ka daga gare su, haƙiƙa, za Ni cika jahannama daga gare ku, gaba ɗaya

Verse 19 — Surah Al-Araf 7:19

Kuma ya Adam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itaciya, har ku kasance daga Azzalumai

Verse 20 — Surah Al-Araf 7:20

Sai Shaiɗan ya sanya musu waswasi domin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hana ku daga wannan itaciya ba face domin kada ku kasance mala'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama

Verse 21 — Surah Al-Araf 7:21

Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne ni, a gare ku, haƙiƙa, daga masu nasiha ne

Verse 22 — Surah Al-Araf 7:22

Sai ya saukar da su da ruɗi. Sa'an nan a lokacin da suka ɗanɗani itaciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga suna liƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hana ku ba daga waccan itaciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne

Verse 23 — Surah Al-Araf 7:23

Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba Ka gafarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙiƙa, Muna kasancewa daga masu hasara

Verse 24 — Surah Al-Araf 7:24

Ya ce: "Ku sauka, sashenku zuwa ga sashe yana maƙiyi, kuma kuna da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin daɗi zuwa ga wani lokabi

Verse 25 — Surah Al-Araf 7:25

Ya ce: "A cikinta kuke rayuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku

Verse 26 — Surah Al-Araf 7:26

Ya ɗiyan Adam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa* a kanku, tana rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawa. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alheri. Wancan daga ayoyin Allah ne, tsammaninsu suna tunawa

Verse 27 — Surah Al-Araf 7:27

Ya ɗiyan Adam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyayenku, biyu daga Aljanna, yana fizge tufarsu daga gare su, domin ya nuna musu al'aurarsu. Lalle ne shi, yana ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda ba ku ganin su. Lalle ne Mu, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda ba su yin imani

Verse 28 — Surah Al-Araf 7:28

Kuma idan suka aikata alfasha* su ce: "Mun sami ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah ba Ya umurni da alfasha. Shin kuna faɗar abin da ba ku da saninsa ga Allah

Verse 29 — Surah Al-Araf 7:29

Ka ce: "Ubangjina Ya yi umurni da adalci; kuma ku tsayar da fuskokinku a wurin kowane masallaci, kuma ku roƙe Shi, kuna masu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fara halittarku kuke komawa

Verse 30 — Surah Al-Araf 7:30

Wata ƙungiya (Allah) Ya shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata ta wajaba a kansu; lalle ne su, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma suna zaton, lalle su, masu shiryuwa ne

Verse 31 — Surah Al-Araf 7:31

Ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kowane masallaci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shi (Allah), ba Ya son masu ɓarna

Verse 32 — Surah Al-Araf 7:32

Ka ce: "Wane ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar saboda bayinSa, da masu daɗi daga abinci?" Ka ce: "Su, domin waɗanda suka yi imani suke a cikin rayuwar duniya, suna keɓantattu a Ranar Kiyama. "Kamar wannan ne Muke bayyana ayoyi, daki-daki, ga mutanen da suke sani

Verse 33 — Surah Al-Araf 7:33

Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Ya hana abubuwanalfasha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓoyu, da zunubi da rarraba jama'a, ba da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalili ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah

Verse 34 — Surah Al-Araf 7:34

Kuma ga kowace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, ba za a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma ba za su gabace shi ba

Verse 35 — Surah Al-Araf 7:35

Ya ɗiyan Adam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su je muku, suna gaya muku ayoyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, babu tsoro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki

Verse 36 — Surah Al-Araf 7:36

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan su ne abokan wuta, su, a cikinta madawwama ne

Verse 37 — Surah Al-Araf 7:37

To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, ko kuwa ya ƙaryata game da ayoyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littafi yana samunsu, har a lokacin da ManzanninMu suka je musu, suna karɓar rayukansu, su ce: "Ina abin da kuka kasance kuna kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cewa lalle su, sun kasance kafirai

Verse 38 — Surah Al-Araf 7:38

Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙiƙa, sun shige daga gabaninku, daga aljannu da mutane, a cikin Wuta. A ko da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski juna, a cikinta, gaba ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kawo musu azaba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kowane* akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba

Verse 39 — Surah Al-Araf 7:39

Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, ba ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azaba saboda abin da kuka kasance kuna tarawa

Verse 40 — Surah Al-Araf 7:40

Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, ba za a bubbuɗe musu kofofin sama ba, kuma ba su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allura, kuma kamar wannan ne Muke saka wa masu laifi

Verse 41 — Surah Al-Araf 7:41

Suna da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke saka wa azzalumai

Verse 42 — Surah Al-Araf 7:42

Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, ba Mu ƙallafa wa rai face iyawarsa, Waɗannan ne abokan Aljanna, su, a cikinta, madawwma ne

Verse 43 — Surah Al-Araf 7:43

Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirazansu, daga ƙiyayya, ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance muna iya shiryuwa ba, ba domin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙiƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun je mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cewa: "Waccan Aljlnna an gadar da ku ita, saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 44 — Surah Al-Araf 7:44

Kuma 'yan Aljanna suka kirayi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sami abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sami abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yekuwa, cewa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzalumai

Verse 45 — Surah Al-Araf 7:45

Waɗanda suke kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta ta zama karkatacciya,. kuma su, game da Lahira, kafirai ne

Verse 46 — Surah Al-Araf 7:46

Kuma a tsakaninsu akwai wani shamaki,* kuma a kan A'araf akwai wasu maza suna sanin kowa da alamarsu; Kuma suka kirayi abokan Aljamia cewa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhali kuwa su, suna tsammani

Verse 47 — Surah Al-Araf 7:47

Kuma idan an juyar da gannansu wajen abokan wuta, su ce: "Ya Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu tare da mutane Azzalumai

Verse 48 — Surah Al-Araf 7:48

Kuma abokan A'araf suka kirayi wasu maza, suna sanin su da alamarsu, suka ce: "Tarawar dukiyarku da abin da kuka kasance kuna yi na girman kai, bai wadatar ba daga barinku

Verse 49 — Surah Al-Araf 7:49

Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah ba zai same su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, babu tsoro akanku, kuma ba ku zama kuna baƙin ciki ba

Verse 50 — Surah Al-Araf 7:50

Kuma 'yan wuta suka kirayi 'yan Aljanna cewa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa ko kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramta su a kan kafirai

Verse 51 — Surah Al-Araf 7:51

Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wasa, kuma rayuwar duniya ta ruɗe su." To, a yau Muna mantawa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ayoyinMu suna musu

Verse 52 — Surah Al-Araf 7:52

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun je musu da Littafi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yana shiriya da rahama ga mutane waɗanda suke yin imani

Verse 53 — Surah Al-Araf 7:53

Shin, suna jira, face fassararsa, a ranar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabani, suna cewa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun je da gaskiya. To, shin, muna da wasu masu ceto, su yi ceto gare mu, ko kuwa a mayar da mu, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatawa?" Lalle ne sun yi hasarar rayukansu, kuma abin da suka kasance suna ƙirƙirawa ya ɓace musu

Verse 54 — Surah Al-Araf 7:54

Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yana sanya dare ya rufa yini, yana neman sa da gaggawa, kuma rana da wata da taurari horarru ne da umurninSa. To, Shi ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu ta bayyana

Verse 55 — Surah Al-Araf 7:55

Ku kirayi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓoye: lalle ne Shi, ba Ya son masuwuce iyaka

Verse 56 — Surah Al-Araf 7:56

Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bayan gyaranta. Kuma ku kiraye shi saboda tsoro da tsammani; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga masu kyautatawa

Verse 57 — Surah Al-Araf 7:57

Kuma Shi ne wanda Yake aika iskoki, suna bishara gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizagizai masu nauyi,* sai Mu kora su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itice. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammaninku, kuna tunani

Verse 58 — Surah Al-Araf 7:58

Kuma gari mai kyau, tsirinsa yana fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya munana, (tsirinsa) ba ya fita, face da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ayoyi domin mutane waɗan da suke godewa

Verse 59 — Surah Al-Araf 7:59

Lalle ne, haƙiƙa Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta waAllah! Ba ku da wani abin bautawa waninSa. Lalle ne ni, ina yimuku tsoron azabar wani Yini mai girma

Verse 60 — Surah Al-Araf 7:60

Mashawarta* daga mutanensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙiƙa, Muna ganin ka a cikin ɓata bayyananniya

Verse 61 — Surah Al-Araf 7:61

Ya ce: "Ya mutanena! Babu ɓata guda gare ni, kuma amma ni Manzo ne daga ubangijin halittu

Verse 62 — Surah Al-Araf 7:62

Ina iyar muku da saƙonnin Ubangijina; kuma ina yi muku nasiha, kuma ina sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba

Verse 63 — Surah Al-Araf 7:63

Shin, kuna mamakin cewa ambato ya zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, domin ya yi muku gargaɗi, kuma domin ku yi taƙawa, kuma tsammaninku ana jin ƙanku

Verse 64 — Surah Al-Araf 7:64

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsirar da shi da waɗanda suke tare da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ayoyinMu. Lalle ne su, sun kasance wasu mutane ɗimautattu

Verse 65 — Surah Al-Araf 7:65

Kuma zuwa ga Adawa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah! Ba ku da wani abin bauta wa, waninSa. Shin fa, ba za ku yi taƙawa ba

Verse 66 — Surah Al-Araf 7:66

Mashawarta waɗanda suka kafirta daga mutanensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙiƙka, Muna ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mu, haƙiƙa, Muna zaton ka daga maƙaryata

Verse 67 — Surah Al-Araf 7:67

Ya ce: "Ya mutanena! Babu wata wauta a gare ni, kuma amma ni, Manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 68 — Surah Al-Araf 7:68

Ina iyar muku da saƙonnin Ubangijina, kuma ni, gare ku, mai nasiha ne amintacce

Verse 69 — Surah Al-Araf 7:69

Shin, kuma kun yi mamaki cewa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, domin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tuna a lokacin da Ya sanya ku masu mayewa daga bayan mutanen Nuhu, kuma Ya ƙara muku zati a cikin halitta. Saboda haka ku tuna ni'imomin Allah; tsammaninku kuna cin nasara

Verse 70 — Surah Al-Araf 7:70

Suka ce: "Shin, ka zo mana ne domin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance suna bauta wa? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan ka kasance daga masu gaskiya

Verse 71 — Surah Al-Araf 7:71

Ya ce: "Haƙiƙa azaba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kuna jayayya da ni a cikin wasu sunaye waɗanda ku ne kuka yi musu sunayen, ku da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tare da ku mai jira ne

Verse 72 — Surah Al-Araf 7:72

To, sai Muka tsirar da shi, shi da waɗanda suke tare da shi saboda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu, kuma ba su kasance muminaiba

Verse 73 — Surah Al-Araf 7:73

Kuma zuwa ga Samudawa ɗan'uwansu, Salihu, ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah; ba ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙiƙa hujja bayyananniya ta zo muku daga Ubangijinku! wannan raƙumar Allah ce, a gare ku, wata aya ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shafe ta da wata cuta har azaba mai raɗaɗi ta kama ku

Verse 74 — Surah Al-Araf 7:74

Kuma ku tuna a lokacin da Ya sanya ku mamaya daga bayan Adawa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kuna riƙon manyan gidaje daga tuddanta, kuma kuna sassaƙar ɗakuna daga duwatsu; saboda haka ku tuna ni'imomin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna masu fasadi

Verse 75 — Surah Al-Araf 7:75

Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar*, ga waɗanda suka yi imani daga gare su: "Shin, kuna sanin cewaSalihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mu, da abin daaka aiko shi, masu imani ne

Verse 76 — Surah Al-Araf 7:76

Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi imani da shi kafirai ne

Verse 77 — Surah Al-Araf 7:77

Sai suka soke raƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Ya Salihu! Ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan ka kasance daga manzanni

Verse 78 — Surah Al-Araf 7:78

Sai tsawa ta kama su, saboda haka suka wayi gari a cikin gidansu guggurfane

Verse 79 — Surah Al-Araf 7:79

Sai ya juya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutanena! Lalle ne, haƙiƙa, na iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma na yi muku nasiha kuma amma ba ku son masu nasiha

Verse 80 — Surah Al-Araf 7:80

Da Luɗu, a lokacin daya ce wa mutanensa: "Shin, kuna je wa alfasha, babu kowa da ya gabace ku da ita daga halittu

Verse 81 — Surah Al-Araf 7:81

Lalle ne ku, haƙiƙa kuna je wa maza da sha'awa, baicin mata; A'a, ku mutane ne maɓarnata

Verse 82 — Surah Al-Araf 7:82

Kuma babu abin da ya kasance jawabin mutanensa, face ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne su, wasumutane ne masu da'awar tsarki

Verse 83 — Surah Al-Araf 7:83

Sai Muka tsirar da shi, shi da iyalansa, face matarsa, ta kasance daga masu wanzuwa

Verse 84 — Surah Al-Araf 7:84

Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka duba yadda aƙibar masu laifi ta kasance

Verse 85 — Surah Al-Araf 7:85

Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah; ba ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku ta zo muku! Sai ku cika mudu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutane kayansu, kuma kada ku yi fasadi a cikin ƙasa a bayan gyaranta. Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance muminai

Verse 86 — Surah Al-Araf 7:86

Kuma kada ku zauna ga kowane tafarki kuna ƙyacewa, kuma kuna kangewa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi imani da shi, kuma kuna neman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lokacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku duba yadda aƙibar masu fasadi ta kasance

Verse 87 — Surah Al-Araf 7:87

Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi imani da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi imani ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakaninmu; kuma Shi ne Mafi alherin masu hukunci

Verse 88 — Surah Al-Araf 7:88

Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutanensa, suka ce: "Lalle ne, Muna fitar da kai, Ya Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Imani tare da kai, daga alƙaryarmu; ko kuwa lalle ku komo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma ko da mun kasance masu ƙi

Verse 89 — Surah Al-Araf 7:89

Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun koma a cikin addininku a bayan lokacin da Allah ya tsirar da mu daga gare shi, kuma ba ya kasancewa a gare mu, mu koma a cikinsa, face idan Alah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Ya yalwaci dukan kome ga ilmi. Ga Allah muka dogara. Ya Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakaninmu da tsakanin mutanenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alherin masu hukunci

Verse 90 — Surah Al-Araf 7:90

Kuma mashawarta waɗanda suka kafirta daga mutanensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙiƙa ku, a lokacin nan, masu hasara ne

Verse 91 — Surah Al-Araf 7:91

Sai tsawa ta kama su, saboda haka suka wayi gari, a cikin gidan su, suna guggurfane

Verse 92 — Surah Al-Araf 7:92

Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance su nemasu hasara

Verse 93 — Surah Al-Araf 7:93

Sai ya juya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutanena! Haƙiƙa, na iyar muku da saƙonnin Ubangijina, kuma na yi muku nasiha! To, yaya zan yi baƙin ciki a kan mutane kafirai

Verse 94 — Surah Al-Araf 7:94

Kuma ba Mu aika wani Annabi* a cikin wata alƙarya ba, face Mun kama mutanenta da azaba da cuta, tsammaninsu suna yin ƙasƙantar da kai

Verse 95 — Surah Al-Araf 7:95

Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummuna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cuta da azaba sun shafi ubanninmu." (sai su koma wa kafirci). Sai Mu kama su kwatsam! alhali kuwa su, ba su sansancewa

Verse 96 — Surah Al-Araf 7:96

Kuma da lalle mutanen alƙaryu sun yi imani kuma suka yi taƙawa da haƙiƙa Mun buɗe albarkoki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kama su da abin da suka kasance suna tarawa

Verse 97 — Surah Al-Araf 7:97

Shin, mutanen alƙaryu sun amince wa azabar Mu ta je musu da dare, alhali kuwa suna barci

Verse 98 — Surah Al-Araf 7:98

Ko kuwa mutanen alƙaryu sun amince wa azabarMu ta je musu da hantsi, alhali kuwa suna wasa

Verse 99 — Surah Al-Araf 7:99

Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, babu mai amince wa makarun Allah face mutane masu hasara

Verse 100 — Surah Al-Araf 7:100

Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gadon ƙasa ba daga bayan mutanenta cewa da Muna so, da Mun same su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukatansu, sai su zama ba su ji

Verse 101 — Surah Al-Araf 7:101

Waɗancan alƙaryu Muna gaya maka daga labaransu, kuma lalle ne, haƙiƙa manzanninMu sun je musu da hujjoji bayyanannnu; to, ba su kasance suna yin imanida abin da suka ƙaryata daga gabani ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufewa a kan zukatan kafirai

Verse 102 — Surah Al-Araf 7:102

Kuma ba Mu sami wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sami mafi yawansu, haƙiƙa, fasiƙai

Verse 103 — Surah Al-Araf 7:103

Sa'an nan kuma Mun aika Musa,* daga bayansu, da ayoyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zalunci game da su. To, dubi yadda aƙibar maɓarnata take

Verse 104 — Surah Al-Araf 7:104

Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne ni, manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 105 — Surah Al-Araf 7:105

Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kome ga Allah face gaskiya. Lalle ne, na zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Bani Isra'ila tareda ni

Verse 106 — Surah Al-Araf 7:106

Ya ce: "Idan ka kasance ka zo da wata aya, to, ka kawo ta, idan ka kasance daga masu gaskiya

Verse 107 — Surah Al-Araf 7:107

Sai ya jefa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyanan ne

Verse 108 — Surah Al-Araf 7:108

Kuma ya fizge hannun sa, sai ga shi fari ga masu dubi

Verse 109 — Surah Al-Araf 7:109

Mashawarta daga mutanen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙiƙa, matsafi ne mai ilmi

Verse 110 — Surah Al-Araf 7:110

Yana son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mene ne kuke shawartawa

Verse 111 — Surah Al-Araf 7:111

Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shi da ɗan'uwansa, kuma ka aika da masu gayyar mutane a cikin garuruwa

Verse 112 — Surah Al-Araf 7:112

Su zo maka da duka matsafi, mai ilmi

Verse 113 — Surah Al-Araf 7:113

Kuma matsafa suka je wa fir'auna suka ce: "Lalle ne, shin, Muna da ijara, idan mun kasance mu ne marinjaya

Verse 114 — Surah Al-Araf 7:114

Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kuna a cikin makusanta

Verse 115 — Surah Al-Araf 7:115

Suka ce: "Ya Musa! Ko dai ka jefa, ko kuwa mu kasance, mu ne, masu jefawa

Verse 116 — Surah Al-Araf 7:116

Ya ce: "Ku jefa." To a okacin da suka jefa, suka sihirce idanun mutane kuma suka tsoratar da su; Kuma suka je da tsafi mai girma

Verse 117 — Surah Al-Araf 7:117

Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa: "Ka jefa sandarka." Sai ga ta tana laƙumar abin da suke ƙarya da shi

Verse 118 — Surah Al-Araf 7:118

Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatawa ya ɓaci

Verse 119 — Surah Al-Araf 7:119

Sai aka rinjaye su a can, kuma suka juya suna ƙasƙantattu

Verse 120 — Surah Al-Araf 7:120

Kuma aka jefar da matsafan, suna masu sujada

Verse 121 — Surah Al-Araf 7:121

Suka ce: "Mun yi imani da Ubangijin halittu

Verse 122 — Surah Al-Araf 7:122

Ubangijin Musa da Haruna

Verse 123 — Surah Al-Araf 7:123

Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi imani da shi a gabanin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙiƙa, makirci ne kuka makirta a cikin birni, domin ku fitar da mutanensa daga gare shi; To, da sannu za ku sani

Verse 124 — Surah Al-Araf 7:124

Lalle ne, ina karkatse hannayenku da ƙafafunku daga saɓani, sa'an nan kuma, haƙiƙa, ina tsire, ku gaba ɗaya

Verse 125 — Surah Al-Araf 7:125

Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, masu juyawa ne

Verse 126 — Surah Al-Araf 7:126

Kuma ba ka zargin kome daga gare mu face domin mun yi imani da ayoyin Ubangijinmu a lokacin da suka zo mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana muna Musulmai

Verse 127 — Surah Al-Araf 7:127

Kuma mashawarta daga mutanen Fir'auna suka ce: "Shin, za ka bar Musa da mutanensa domin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumakanka?" Ya ce: "Za mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu raya matansu; kuma lalle ne mu, a bisa gare su, marinjaya ne

Verse 128 — Surah Al-Araf 7:128

Musa ya ce wa mutanensa:* "Ku nemi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda Yake so daga bayinSa, kuma aƙiba ta masu taƙawa ce

Verse 129 — Surah Al-Araf 7:129

Suka ce: "An cutar da mu daga gabanin ka zo mana, kuma daga bayan da ka zo mana." Ya ce: "Akwai tsammanin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya duba yadda kuke aikatawa

Verse 130 — Surah Al-Araf 7:130

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun kama mutanen Fir'auna da tsananin shekaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itace; Tsammaninsu suna tunawa

Verse 131 — Surah Al-Araf 7:131

Sa'an nan idan wani alheri ya je musu, sai su ce: "Masifa ta same su, sai su yi shu'umci da Musa da wanda yake tare da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu ba su sani

Verse 132 — Surah Al-Araf 7:132

Kuma suka ce: "Ko me ka zo mana da shi daga aya, domin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, saboda kai, masu imani ba

Verse 133 — Surah Al-Araf 7:133

Sai Muka aika a kansu da cikowa, da fara, da ƙwarƙwata da kwaɗi, da jini; ayoyi abubuwan rarrabewa*; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutane masu laifi

Verse 134 — Surah Al-Araf 7:134

Kuma a lokacin da masifa ta auku a kansu, sukan ce: "Ya Musa! Ka roƙa mana Ubangijinka, saboda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azabar daga barinmu, haƙiƙa Muna imani saboda kai, kuma muna sakin Bani Isra'ila tire da kai

Verse 135 — Surah Al-Araf 7:135

To, a lokacin da Muka kuranye azaba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke masu iske shi ne, sai ga su suna warwarewa

Verse 136 — Surah Al-Araf 7:136

Sai Muka yi azabar ramuwa, daga gare su, saboda haka Muka nutsar da su a cikin teku, domin lalle ne su, sun ƙaryata game da ayoyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gafilai

Verse 137 — Surah Al-Araf 7:137

Kuma Muka gadar da mutanen, waɗanda sun kasance ana raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Bani Isra'ila, saboda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutanensa suka kasance suna sana'antawa, da abin da suka kasance suna shimfiɗawa

Verse 138 — Surah Al-Araf 7:138

Kuma Muka ƙetarar da Bani Isra'ila ga teku, sai suka je a kan wasu mutane waɗanda suna lizimta da ibada a kan wasu gumaka, nasu suka ce: "Ya Musa! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abubuwan bautawa "* Ya ce: "Lalle ne ku, mutane ne kuna jahilta

Verse 139 — Surah Al-Araf 7:139

Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance suna aikatawa ƙarya ne

Verse 140 — Surah Al-Araf 7:140

Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nema muku ya zama abin bautawa, alhali kuwa Shi (Allah) Ya fifita ku a kan halittu

Verse 141 — Surah Al-Araf 7:141

Kuma a lokacin da Muka tsirar da ku daga mutanen Fir'auna, suna taya muku mugunyar azaba. suna karkashe ɗiyanku maza, kuma suna rayar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabawa daga Ubangijinku,* Mai girma

Verse 142 — Surah Al-Araf 7:142

Kuma Muka yi wa'adi ga Musa da dare talatin* kuma Muka cika su da goma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Musa ya ce wa ɗan'uwansa, Haruna: "Ka maye mini a cikin mutanena, kuma ka gyara, kuma kada ka bi hanyar masu fasadi

Verse 143 — Surah Al-Araf 7:143

Kuma a lokacin da Musa ya je ga mikatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Musa ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nuna mini in yi dubi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Ba za ka gan Ni ba, kuma amma ka duba zuwa ga dutse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, za ka gan Ni." Sa'an nan a lokacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dutsen, Ya sanya shi niƙaƙƙe. Kuma Musa ya faɗi somamme. To, a lokacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai

Verse 144 — Surah Al-Araf 7:144

Ya ce: "Ya Musa! Lalle ne Ni, Na zaɓe ka bisa ga mutane da manzanciNa, kuma da maganaTa. Saboda haka ka riƙi abin da Na ba ka, kuma ka kasance daga masu godiya

Verse 145 — Surah Al-Araf 7:145

Kuma Muka rubuta masa a cikin alluna daga kowane abu, wa'azi da rarrabewa ga dukan kowane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutanenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu;* za Ni nuna muku gidan fasiƙai

Verse 146 — Surah Al-Araf 7:146

Za Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa. Kuma idan sun ga dukan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, ba za su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun ƙaryata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gafilai

Verse 147 — Surah Al-Araf 7:147

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu da gamuwa da Lahira, ayyukansu sun ɓaci. Shin, ana saka musu, face da abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 148 — Surah Al-Araf 7:148

Kuma mutanen Musa suka riƙi maraƙi*, jikin mutane, yana ruri, daga bayan tafiyarsa, daga kayan ƙawarsu. Shin, ba su gani ba, cewa lalle ne shi, ba ya yi musu magana, kuma ba ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance masu zalunci

Verse 149 — Surah Al-Araf 7:149

Kuma a lokacin da suka yi nadama, kuma suka ga cewalalle ne su haƙiƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙiƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gafarta mana, lalle ne muna kasancewa daga masu hasara

Verse 150 — Surah Al-Araf 7:150

Kuma a lokacin da Musa ya koma zuwa ga mutanensa, yana mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bayana! Shin, kun nemi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Ya ɗan'uwata! Lalle ne mutanen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, saboda haka kada ka darantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tare da mutane Azzalumai

Verse 151 — Surah Al-Araf 7:151

Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, ni da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhali kuwa Kai ne Mafi rahamar masu rahama

Verse 152 — Surah Al-Araf 7:152

Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walakanci a cikin rayuwar duniya, za su same su: Kuma kamar wancan ne Muke saka wa masu ƙirƙira ƙarya

Verse 153 — Surah Al-Araf 7:153

Kuma waɗanda suka aikata miyagun ayyuka, sa'an nan suka tuba daga bayansu kuma sukayi imani, lalle ne Ubangijinka daga bayansu, haƙiƙa, Mai gafarane, Mai jin ƙai

Verse 154 — Surah Al-Araf 7:154

Kuma a lokacin da fushin ya kwanta daga barin Musa, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke su, ga Ubangijinsu, masu jin tsoro ne

Verse 155 — Surah Al-Araf 7:155

Kuma Musa ya zaɓi mutanensa, namiji saba'in domin miƙatinMu. To, a lokacin da tsawa ta kama su, ya ce: "Ya Ubangijina! Da Ka so, da Ka halakar da su daga gabani, su da ni. Shin za Kahalaka mu, saboda abin da wawayen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba face fitinarKa Kana ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kana shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gafarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhali kuwa Kai ne Mafi alherin masu gafara

Verse 156 — Surah Al-Araf 7:156

Kuma Ka rubuta mana alheri a cikin wannan duniya, kuma a cikin Lahira. Lalle ne mu, mun tuba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzabaTa Ina samu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kome. Sa'an nan za Ni rubuta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma suna bayar da zakka, da waɗanda suke, game da ayoyin Mu muminai ne

Verse 157 — Surah Al-Araf 7:157

Waɗanda suke suna bin Manzo*, Annabi, Ummiyyi wanda suke samun sa rubuce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjila.yana umurnin su da alheri, kuma yana hana su daga barin abin da ba a so; kuma yana halatta musu abu- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar munana a kansu. Kuma yana kayar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi imani da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tare da shi, waɗan- nan ne masu cin nasara

Verse 158 — Surah Al-Araf 7:158

Ka ce: "Ya ku mutane!* Lalle ne ni manzon Allah nezuwa gare ku, gaba ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shi ne da mulkin sammai da ƙasa; Babu wani abin bautawa face Shi, Yana rayarwa, kuma Yana matarwa, sai ku yi imani daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominSa; ku bi shi, tsammaninku, kuna shiryuwa

Verse 159 — Surah Al-Araf 7:159

Kuma daga mutanen* Musa akwai al'umma, suna shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin adalci

Verse 160 — Surah Al-Araf 7:160

Kuma Muka yayyanka su sibɗi goma sha biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Musa a lokacin da mutanensasuka neme shi, ga shayarwa, cewa: "Ka doki dutsen* da sandarka."Sai marmaro goma sha biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kowaɗanne mutane sun san mashayarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga masu daɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zalunce Mu ba; kuma amma rayukansu suke zalunta

Verse 161 — Surah Al-Araf 7:161

Kuma a lokacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya*, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kofa kuna masu sujada; Mu gafarta muku laifuffukanku, kuma za Mu ɗara wa masu kyautatawa

Verse 162 — Surah Al-Araf 7:162

Sai waɗanda suka yi zalunci daga gare su, suka musanya magana* watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azaba a kansu, daga sama, saboda abin da suka kasance suna yi na zalunci

Verse 163 — Surah Al-Araf 7:163

Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga teku, a lokacin da suke ƙetare haddi a cikin Asabar, a lokacin da kifayensu, suke je musu a ranar Asabar* ɗinsu jere. Kuma a ranar da ba su yi Asabar ba, ba su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance suna yi na fasiƙanci

Verse 164 — Surah Al-Araf 7:164

Kuma a lokacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutane waɗanda Allah Yake Mai halaka su ko kuwa Mai yi musu azaba, azaba mai tsanani?" Suka ce: "Domin neman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammaninsu, suna yin taƙawa

Verse 165 — Surah Al-Araf 7:165

To, a lokacin da suka manta da abin da aka tunatar da su da shi, Mun tsirar da waɗanda suke hani daga cuta, kuma Muka kama waɗanda suka yi zalunci, da azaba mai tsanani domin abin da suka kasance suna yi, na fasiƙanci

Verse 166 — Surah Al-Araf 7:166

Sa'an nan a lokacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu

Verse 167 — Surah Al-Araf 7:167

Kuma a lokacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, za Ya aika a kansu (Yahud), zuwa, Ranar¡iyama, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azaba, lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Mai gaggawar uƙuba ne, kuma shi haƙiƙa, Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 168 — Surah Al-Araf 7:168

Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummomi, daga gare su akwai salihai, kuma daga gare su akwai wanda ba haka ba. Muka jarrabe su da abubuwan alheri da na musifa; Tsammaninsu, suna komowa

Verse 169 — Surah Al-Araf 7:169

Sai wasu' yan baya suka maye daga bayansu, sun gaji Littafin, suna karɓar sifar* wannan ƙasƙantacciya, suna cewa: "Za a gafarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littafi ba a kansu cewa kada su faɗa ga Allah, face gaskiya, alhali kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lahira ne mafi alheriga wanda ya yi taƙawa? Shin, ba za ku hankalta ba

Verse 170 — Surah Al-Araf 7:170

Kuma waɗanda suke riƙewa da laittafi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mu, ba Mu tozarta ladar masu gyarawa

Verse 171 — Surah Al-Araf 7:171

Kuma a lokacin da muka ɗaukaka dutse* sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shi, mai faɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kawo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammaninku kuna yin taƙawa

Verse 172 — Surah Al-Araf 7:172

Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Adam, daga bayayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rayukansu, (Ya ce): "Shin, ba Ni ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Ranar Kiyama: Lalle ne mu, daga wannan, gafalallu ne

Verse 173 — Surah Al-Araf 7:173

Ko kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mu, mun kasance zuriya daga bayansu. Shin fa, Kana halaka mu, saboda abin da masu ɓatawa suka aikata

Verse 174 — Surah Al-Araf 7:174

Kuma kamar haka Muke rarrabe ayoyi, daki-daki; tsammaninsu, suna komowa

Verse 175 — Surah Al-Araf 7:175

Ka karanta a kansu labarin wanda Muka kawo masa* ayoyinMu, sai ya saɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku

Verse 176 — Surah Al-Araf 7:176

Kuma da Mun so, da Mun ɗaukaka shi da su, kuma amma shi, ya nemi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zuciyarsa. To, misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, ko kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misalin mutane waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu: Ka jeranta karatun labarun; tsammaninsu suna tunani

Verse 177 — Surah Al-Araf 7:177

Tir da zama misali, mutanen da suka ƙaryata game da ayoyinMu, kuma kansu suka kasance suna zalunta

Verse 178 — Surah Al-Araf 7:178

Wanda* Allah Ya shiryar, to, shi ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan su ne masu hasara

Verse 179 — Surah Al-Araf 7:179

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun halitta saboda Jahannama, masu yawa daga aljannu da mutane, suna da zukata, ba su fahimta da su, kuma suna da idanu, ba su gani da su, kuma suna da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisashe suke. A'a, su ne mafi ɓacewa; Waɗancan su ne gafalallu

Verse 180 — Surah Al-Araf 7:180

Kuma Allah Yana da sunaye masu kyau.* Sai ku roƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhadi a cikin sunayenSa: za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 181 — Surah Al-Araf 7:181

Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, suna shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin adalci

Verse 182 — Surah Al-Araf 7:182

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ayoyinMu, za Mu yi musu istidraji daga inda ba su sani ba

Verse 183 — Surah Al-Araf 7:183

Kuma Ina yi musu jinkiri, lalle ne kaidiNa, mai ƙarfi ne

Verse 184 — Surah Al-Araf 7:184

Shin, ba su yi tunini ba, cewa babu wata hauka ga ma'abucinsu?* shi bai zama ba face mai gargaɗi mai bayyanawa

Verse 185 — Surah Al-Araf 7:185

Shin, ba su yi dubi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kome, kuma akwai tsammani kasancewar ajalinsu, haƙiƙa, ya kusanta? To, da wane labari a bayansa suke yin imani

Verse 186 — Surah Al-Araf 7:186

Wanda Allah Ya ɓatar to babu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yana barin su, a cikin ɓatarsu suna ɗimuwa

Verse 187 — Surah Al-Araf 7:187

Suna tambayar ka* daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Babu mai bayyana ta ga lokacinta face shi Ta yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Ba za ta zo muku ba face kwatsam." suna tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani

Verse 188 — Surah Al-Araf 7:188

Ka ce: "Ba ni mallaka wa raina wani amfani, kuma haka ban tunkuɗe wata cuta, faceabin da Allah Ya so. Kuma da na kasance ina sanin gaibi, da lalle ne, na yawaita daga alheri kuma cuta ba za ta shafe ni ba, ni ban zama ba fice mai gargaɗi, kumamai bayar da bishara ga mutane waɗanda suke yin imani

Verse 189 — Surah Al-Araf 7:189

Shi ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare* ta, ma'auranta, domin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lokacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shuɗe dashi. Sa'an nan a lokacin da ya yi nauyi, sai suka roƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka ba mu abin ƙwarai, haƙiƙa, za mu kasance dagamasu godiya

Verse 190 — Surah Al-Araf 7:190

To, a lokacin da Ya ba su abin ƙwarai, suka sanya Masa abokan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Ya tsarkaka daga abin da suke yi na shirki

Verse 191 — Surah Al-Araf 7:191

Shin, suna shirki da abin da ba ya halittar kome, kuma sune ake halittawa

Verse 192 — Surah Al-Araf 7:192

Kuma ba su iya bayar da taimako gare su, kuma kansu ma, ba su iya taimaka

Verse 193 — Surah Al-Araf 7:193

Kuma idan kun kiraye su zuwa ga shiriya, ba za su bi ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kiraye su, ko kuwa ku masu kawaici ne

Verse 194 — Surah Al-Araf 7:194

Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bayi ne misalanku: to, ku kiraye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance masu gaskiya

Verse 195 — Surah Al-Araf 7:195

Shin suna da ƙafafu da suke yin tafia da su? Ko suna da hannaye da suke damƙa da su? Ko suna da idanu da suke gani da su? Ko suna da kunnuwa da suke saurare da su? Ka ce: "Ku kirawo abubuwan* shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurara mini

Verse 196 — Surah Al-Araf 7:196

Lalle ne, Majiɓincina Allah ne Wanda Ya saukar da Littafi kuma Shi ne Yake jiɓintar salihai

Verse 197 — Surah Al-Araf 7:197

Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, ba su iya taimakon ku, kuma kansu ma, ba su iya taimaka

Verse 198 — Surah Al-Araf 7:198

Kuma idan ka kiraye su zuwa ga shiriya, ba za su ji ba, kuma kana ganin su, suna dubi zuwa gare ka, alhali kuwa su, ba su gani

Verse 199 — Surah Al-Araf 7:199

Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alheri, Kuma ka kau da kai daga jahilai

Verse 200 — Surah Al-Araf 7:200

Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nemi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai ji ne, Masani

Verse 201 — Surah Al-Araf 7:201

Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tashin hankali daga Shaiɗan ya shafe su, sai su tuna (Allah) sai ga su, sun zama masu basira

Verse 202 — Surah Al-Araf 7:202

Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) suna taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma ba su taƙaitawa

Verse 203 — Surah Al-Araf 7:203

Kuma idan ba ka je musu da wata aya ba, su ce: "Don me ba ka ƙaga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, ina biyar abin da aka yo wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abubuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutane waɗanda suke yin imani

Verse 204 — Surah Al-Araf 7:204

Kuma idan an karanta* Alƙur'ani sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammaninku, ana yi muku rahama

Verse 205 — Surah Al-Araf 7:205

Kuma ka ambaci* Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsoro, kuma komabayan bayyanawa na magana, da safe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu

Verse 206 — Surah Al-Araf 7:206

Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka ba su yin girman kai ga bauta Masa, kuma suna tsarake shi da tasbihi, kuma a gare shi suke yin sujada