Suna tambayar ka* ga ganima. ka ce: "Ganima ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyara abin da yake a tsakaninku, kuma ku yi ɗa'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance Muminai
Abin sani kawai, numinai su ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukatansu su firgita, kuma idan an karanta ayoyinSa a kansu, su ƙara musu wani imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara
Kuma a lokacin* da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cewa lalle ita taku ce: kuma kuna gurin cewa lalle ƙungiya wadda ba ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yana nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmominSa, kuma Ya katse ƙarshen kafirai
Kuma Allah bai sanya shi ba face Domin bishara, kuma domin zukatanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba face daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwayi ne, Mai hikima
A lokacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗomin aminci daga gare Shi, kuma Yana saukar da ruwa* daga sama, a kanku, domin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma domin Ya ɗaure a kan zukatanku, kuma Ya tabbatar da ƙafafu da shi
A lokacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Mala'iku cewa: "Lalle ne Ni, Ina tare da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi imani: Za Ni jefa tsoro a cikin zukatan waɗanda suka kafirta, sai ku yi duka bisa ga wuyoyi kuma ku yi duka daga gare su ga dukkan yatsu
Kuma duka wanda* ya juya musu bayansa a yinin nan, face wanda ya karkata domin koɗayya, ko kuwa wanda ya je domin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya koma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makoma ita
To, ba ku ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa;* kuma amma Allah ne Ya yi jifar. Kuma dominYa jarraba Musulmi da jarrabawa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani
Idan kun yi alfanun cin nasara to lalle nasarar ta je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alheri a gare ku, kuma idan kun koma za Mu koma, kuma jama'arku ba za ta wadatar muku da kome ba, ko da ta yi yawa. Kuma lalle ne cewa Allah Yana tare da muminai
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kiraye ku zuwa ga abin da Yake rayar da ku; Kuma ku sani cewa Allah Yana shamakacewa a tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma lalle ne Shi, a zuwa gare Shi ake tara ku
Ku tuna a lokacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwa a cikin ƙasa kuna tsoron mutane su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafa ku da taimakonSa kuma Ya azurta ku daga abubuwa masu daɗi; Tsammaninku, kuna godewa
Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanya muku mararraba (da tsoro) kuma Ya kankare ƙananan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gafarta muku. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma
Kuma a lokacin da waɗanda* suka kafirta suke yin makirci game da kai, domin su tabbatar da kai, ko kuwa su kashe ka, ko kuwa su fitar da kai, suna makirci kuma Allah Yana mayar musa da makirci kuma Allah ne Mafificin masu makirci
Kuma idan aka karanta, ayoyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji da muna so, haƙiƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba face tatsunayoyin mutanen farko
A lokacin da suka ce: "Ya Allah! Idan wannan ya kasancc shi ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwatsu, a kanmu, daga sama, ko kuwa Kazo mana da wata azaba, mai raɗaɗi
Kuma mene ne a gare su da Allah ba zai yi musu azaba ba, alhali kuwa su, suna kangewa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Babu majiɓintanSa face masu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba
Lalle ne waɗanda suka kafirta, suna ciyar da dukiyoyinsu, domin su kange daga hanyar Allah; to, za a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadama a kansu, sa'an nan kuma a rinjaye su. Kuma waɗanda suka kafirta zuwa ga Jahannama ake tara su
Domin Allah Ya rarrabe mummuna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummunan, sashensa a kan sashe, sa'an nan Ya shirga shi gaba daya, sa'an nan Ya sanya shi a cikin Jahannama. Waɗannan su ne masu hasara
Ka ce wa waɗanda suka kafirta, idan sun hanu, za a gafarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun koma, to, hanyar kafiran farko, haƙiƙa, ta shuɗe
Kuma ku yaƙe su har wata fitina ba za ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatawa Mai gani ne
Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sami* ganima daga wani abu, to, lalle ne Allah Yana da humusinsa kuma da Manzo, kuma da masu zumunta, da marayu da miskinai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi imani da Allah da abin da Muka saukar a kan bawanMu a Ranar Rarrabewa, a Ranar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kowane abu, Mai ikon yi
A lokacin da kuke a gaɓa ta kusa su kuma suna a gaɓa tanesa, kuma ayarin yana a wuri mafi gangarawa daga gare ku, kuma da kun yi wa juna wa'adi, da kun saɓa ga wa'adin; kuma amma domin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatawa. Domin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rayuwa ya rayu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙiƙa, Mai ji Masani
A lokacin da Allah Yake nuna maka su suna kaɗan, a cikin barcinka, kuma da Ya nuna maka su suna da, yawa, lalle ne da kun ji tsoro, kuma lalle ne da kun yi jayayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Ya tsare ku: Lalle Shi ne Masani ga abin da yake a cikin ƙiraza
Kuma a lokacin da Yake nuna muku su, a lokacin da kuka haɗu, a cikin idanunku suna kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu domin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatawa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra
Kuma ku yi ɗa'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yana tare da masu haƙuri
Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidajensu,* suna masu alfahari da yin riya ga mutane, kuma suna kangewa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatawa Mai kewayewa
Kuma a lokacin da Shaiɗan* ya ƙawace musu ayyukansu, kuma ya ce: "Babu marinjayi a gareku a yau daga mutane, kuma ni maƙwabci ne gare ku." To, a lokacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya koma a kan digadigansa, kuma ya ce: "Lalle ne ni barrantacce ne daga gare ku! Ni ina ganin abin da ba ku gani; ni ina tsoron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙuba ne
A lokacin da munafukai da waɗanda suke akwai cuta a cikin zukatansu, suke cewa: "Addinin waɗannan ya ruɗe su" Kuma wanda ya dogara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwayi ne, Mai hikima
Kamar al'adar mutanen Fir'auna da waɗanda suke gabaninsu, sun kafirta da ayoyin Allah, sai Allah Ya kama su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙuba
Wancan ne, domin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutane ba face sun sake abin da yake ga rayukansu, kuma domin lalle Allah ne Mai ji, Masani
Kamar al'adar mutanen Fir'auna da waɗanda suke a gabaninsu, sun ƙaryata game da ayoyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, saboda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutanen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne masu Zalunci
Kuma ku yi tattali, dominsu, abin da kuka sami ikon yi na wani ƙarfi,* kuma da ajiye dawaki, kuna tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, za a cika muku sakamakonsa, kuma ku ba a zaluntar ku
Kuma Ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu. Da ka ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gaba ɗaya, da ba ka sanya soyayya a tsakanin zukatansu ba, kuma amma Allah Ya sanya soyayya a tsakaninsu. Lalle Shi ne Mabuwayi, Mai hikima
Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da muminai a kan yaƙi. Idan mutum ashirin masu haƙuri sun kasance daga gare ku, za su rinjayi metan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dubu daga waɗanda suka kafirta, domin su, mutane ne ba su fahimta
A yanzu Allah Ya sauƙaƙe daga gare ku, kuma Ya sani cewa lalle ne akwai masu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, masu haƙuri, suka kasance daga gare ku, za su rinjayi metan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haƙuri
Ba ya kasancewa* ga wani annabi, kamammu su kasance a gare shi sai (bayan) ya zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kuna nufin sifar duniya kuma Allah Yananufin Lahira. Kuma Allah ne Mabuwayi, Mai hikima
Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannayenku daga kamammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alheri a cikin zukatanku, zai kawo muku mafi alheri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gafara. Kuma Allah ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Lalle ne waɗanda suka yi imani, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsuda rayukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bayar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sashensu waliyyai ne ga sashe. Kuma waɗanda suka yi imani kuma ba su yi hijira* ba, ba ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka neme ku taimako a cikin addini, to taimako ya wajaba a kanku, face a kan mutane waɗanda a tsakaninku da tsakaninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani
Kuma waɗanda suka yi imani kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihadi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bayar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan su ne muminai da gaskiya, sunada gafara da wani Abinci na karamci
Kuma waɗanda suka yi imani daga baya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihadi tare da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abuta zumunta, sashensu ne waliyyan* sashe a cikin Littafin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kome Masani