Kuma da yekuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane, a Ranar Haji Babba cewa lallene Allah Barrantacce ne daga masu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tuba to shi ne mafi alheri a gare ku, kuma idan kun juya, to, ku sani lalle ne ku, ba masu buwayar Allah ba ne. Kuma ka bayar da bishara ga waɗanda suka kafirta, da azaba mai raɗaɗi
Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga masu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kome ba, kuma ba su taimaki kowa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjejeyarsu. Lalle ne Allah Yana son masu taƙawa
Kuma idan watanni, masu alfarma suka shige, to, ku yaki mushirikai inda kuka same su, kuma ku kama su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madakata. To, idan sun tuba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewar sa. Wan can fa domin lalle ne su, mutane ne waɗan da ba su sani ba
Yaya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancewa ga mushirikai, face ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sosai gare ku, sai ku tsayu sosai gare su. Lalle ne Allah Yana son masu taƙawa
Yaya, alhali idan sun ci nasara a kanku, ba za su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amana, suna yardar da ku da bakunansu kuma zukatansu suna ƙi? Kuma mafi yawansu fasiƙai ne
Sa'an nan idan sun tuba* kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Muna rarrabe ayoyi daki-daki, ga mutane waɗanda suke sani
Kuma idan suka warware rantsuwoyin amana daga bayan alkawarinsu, kuma suka yi suka a cikin addininku, to, ku yaki shugabannin kafirci. Lalle ne su, babu rantsuwoyin amana a gare su. Tsammanin su suna hanuwa
Shin, ba ku yaƙin mutane, waɗanda suka warware rantsuwoyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma su ne suka fara muku, tun a farkon lokaci? Shin kuna tsoron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsoron Sa, idan kun kasance muminai
Ko kuna zaton* a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihadi ba daga gare ku, kuma su ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da muminai? Kuma Allah ne Mai jarrabawa ga abin da kuke aikatawa
Ba ya kasancewa ga masu shirki su raya masallatan Allah, alhali kuwa suna masu bayar da shaida a kan rayukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓaci, kuma a cikin wuta su madawwama
Abin sani kawai, mai raya masallatan Allah, shi ne wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bayar da zakka, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah. To, akwai tsammanin waɗannan su kasance daga shiryayyu
Shin, kun sanya shayar da mahajjata da rayar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma ya yi jihaɗi a cikin hanyar Allah? Ba su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane Azzalumai
Waɗanda suka yi imani, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi, a cikin hanyar Allah, da dukiyoyinsu, da rayukansu, su ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan su ne masu babban rabo
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masoya, idan sun nuna son kafirci a kan imani*. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗan nan su ne Azzalumai
Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da matanku da danginku da dukiyoyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsoron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya soyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihadi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasiƙai
Lalle ne, haƙiƙa, Allah Ya taimake ku a cikin wurare masu yawa, da Ranar Hunainu,* a lokacin da yawanku ya ba ku sha'awa, sai bai amfanar da ku da kome ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka juya kuna masu bayar da baya
Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan muminai, kuma Ya saukar da rundunoni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗan da suka kafirta: Wancan ne sakamakon kafirai
Ya ku waɗanda suka yi imani! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, saboda haka kada su kusanci Masallaci Mai Alfarma a bayan shekarar su wannan. Kuma idan kun ji tsoron talauci* to, da sannu Allah zai wadata ku daga falalar Sa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima
Ku yaƙi waɗan da* ba su yin imani da Allah kuma ba su imani da Ranar Lahira kumaba su haramta abin da Allah da Manzon Sa suka haramta, kuma ba su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗan da aka bai wa Littafi, har sai sun bayar da jizya daga, hannu, kuma suna ƙasƙantattu
Kuma Yahudawa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasara suka ce: "Masihu ɗan Allah ne." Wancan zancensu ne da bakunansu. Suna kama da maganar waɗanda suka kafirta daga gabani. Allah Ya la'ance su! Yaya aka karkatar da su
Sun riƙi malamansu* (Yahudu) da ruhubanawansu (Nasara) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masihu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba face da su bauta wa Ubangiji Guda. Babu abin bautawa face Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi
Ya waɗanda suka yi imani! Lalle ne masu yawa daga Ahbar* da Ruhbanawa haƙiƙa suna cin dukiyar mutane da ƙarya, kuma suna kangewa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacewar zinariya da azurfa, kuma ba su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushara da azaba mai raɗaɗi
A Ranar da ake ƙona shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga goshinansu da sashinansu da bayayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace domin rayukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna sanyawa a taska
Lallai ne ƙidayayyun watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin Littafin* Allah, a Ranar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu masu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu. Kuma ku yaƙi mushirikai gaba ɗaya, kamar yadda suke yaƙar ku gaba ɗaya. Kuma ku sani cewa lallai ne Allah Yana tare da masu taƙawa
Abin sani kawai, "Jinkirtawa" ƙari ne a cikin kafirci, ana ɓatar da waɗanda suka kafirta game da shi. Suna halattar da wata a wata shekara kuma su haramtar da shi a wata shekara domin su dace da adadin abin da Allah Ya haramta. Saboda haka suna halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawace musu munanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai
Ya ku waɗanda suka yi imani! Mene ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yaƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi* zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rayuwar duniya ne daga ta Lahira? To jin daɗin rayuwar duniya bai zama ba a cikin Lahira, face kaɗan
Idan ba ku fita da yaƙi ba, Allah zai azabta ku da azaba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutane, wasunku (a maimakonku). Kuma ba za ku cutar da Shida kome ba. Kuma Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne
Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Ya taimake shi, a lokacin da waɗanda suka kafirta suka fitar da shi, Yana na biyun biyu, a lokacin da suke cikin kogon dutse, a lokacin da yake cewa da sahibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yana tare da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunoni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kafirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwayi, Mai hikima
Ku fita da yaƙi kuna masu sauƙaƙan kaya da masu nauyi, kuma ku yi jihadi da dukiyoyinku da kuma rayukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani
Da ya kasance* wata siffar duniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, da sun bi ka, kuma amma fagen ya yi musu nisa. Kuma za su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Da mun sami dama, da mun tafi tare da ku." Suna halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yana sanin lalle, haƙiƙa, sumaƙaryata ne
Waɗanda suke yin imanida Allah da Ranar Lahira, ba za su nemi izininka ga yin, jihadida dukiyoyinsu da rayukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga masu taƙawa
Abin sani kawai, waɗanda ba sa imani da Allah, da Ranar Lahira, kuma zukatansu suka yi shakka, su ne ke neman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu suna ta yin kai kawo
Kuma da sun yi nufin fita, da sun yi wani tattali saboda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zaburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tare da masu* zama
Da sun fita a cikinku ba za su ƙare ku da kome ba face da ɓarna, kuma lalle da sun yi gaggawar sanya annamimanci a tsakaninku, suna nema muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahoto saboda su. Kuma Allah ne Masani ga azzalumai
Kuma lalle ne, haƙiƙa sun nemi fitina daga gabani, kuma, suka juya maka al'amari, har gaskiya ta zo,* kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhali suna masu ƙyama
Kuma daga cikinsu* akwai mai cewa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka faɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙiƙa, mai ƙewayewa ce ga kafirai
Idan wani alheri ya same ka, zai ɓata musu rai, kuma idan wata masifa ta same ka sai su ce: "Haƙiƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabani."Kuma sujuya, alhali kuwa suna masu farin ciki
Ka ce: "Shin, kuna dako ne da mu? Face dai da ɗayan abubuwan biyu* masu kyau, alhali kuwa mu, muna dako da ku, AllahYa same ku da wata azaba daga gare Shi, ko kuwa da hannayenmu. To, ku yi dako. Lalle ne mu, tare da ku masu dakon ne
Kuma babu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su face domin su, sun kafirta da Allah da ManzonSa, kuma ba su zuwa ga salla face Luma suna masu kasala, kuma ba su ciyarwa face suna masu ƙyama
Saboda haka, kada dukiyoyinsu su ba ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yana nufin Ya yi musu azaba, da su a cikin rayuwar duniya, kuma rayukansu su fita alhali kuwa suna kafirai
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dukiyoyin sadaka, sai idan an ba su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a ba su ba daga cikinta sai su zamo suna masu fushi
Kuma da dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya ba su, da ManzonSa kuma suka ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kawo mana daga falalarSa kuma ManzonSa (zai ba mu). Lalle ne mu, zuwa ga Allah masu kwaɗayi ne
Abin sani kawai, dukiyoyin sadaka na faƙirai ne da miskinai da masu aiki a kansu, da waɗanda ake lallashin zukatansu, kuma a cikin fansar wuyoyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cutar Annabi, kuma suna cewa "Shi kunne* ne." Ka ce: "Kunnen alheri gare ku, Yana imani da Allah, kuma Yana yarda da muminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi imani daga gare ku."Kuma waɗanda suke cutar Manzon Allah suna da Azaba mai raɗaɗi
Shin, ba su sani ba cewa "Lalle ne wanda ya saɓa wa Allah da ManzonSa, haƙiƙa Yana da wutar Jahannama, Yana madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulakantawa babba
Munafukai suna tsoron a saukar da wata sura a kansu, wadda take ba su labari ga abin da yake cikin zukatansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsoro
Kuma lalle ne, idan ka tambaye,* su haƙiƙa, suna cewa, "Abin sani kawai, mun kasance muna hira kuma muna wasa. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ayoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgili
Kada ku kawo wani uzuri, haƙiƙa, kun kafirta a bayanimaninku. Idan Mun yafe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, za Mu azabta wata ƙungiya saboda, lalle, sun kasance masu laifi
Munafukai maza da munafukai mata, sashensu* daga sashe, suna umurni da abin ƙi kuma suna hani daga alheri. Kuma suna damƙewar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya manta da su. Lalle ne munafukai su ne fasiƙai
Allah ya yi wa'adi ga munafukai maza da munafukai mata da kafirai da wutar Jahannama, suna madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Ya la'ance su, kuma suna da azaba zaunanniya
Kamar waɗanda suke a gabaninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dukiyoyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabaninku suka ji daɗi, da rabonsu, kuma kuka kutsa kamar kutsawarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓaci a duniya da Lahira, kuma waɗannan su ne masu hasara
Shin labarin waɗanda suke a gabaninsu bai je musu ba, mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da mutanen Ibrahim da Ma'abuta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun je musu da ayoyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yana zaluntar su ba, amma sun kasance rayukansu suke zalunta
Kuma mummunai maza da mummunai mata sashensu majiɓincin sashe ne, suna umurni da alheri* kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka, kuma sunaɗa'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwayi, Mai hikima
Kuma Allah Ya yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mata da gidajen Aljanna ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da wuraren zama masu daɗi a cikin gidajen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma
Suna rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhali kuwa lalle ne, haƙiƙa, sun faɗi kalmar kafirci, kuma; sun kafirta a bayan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su samu ba. Kuma ba su zargi kome ba face domin Allah da ManzonSa Ya wadatar da su daga falalarSa. To, idan sun tuba zai kasance mafi alheri gare su, kuma idan sun juya baya, Allah zaiazabta su da azaba mai raɗaɗi a cikin duniya da Lahira, kuma ba su da wani masoyi ko wani mataimaki a cikin kasa
Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kawo mana daga falalarSa, haƙiƙa, munabayar da sadaka, kuma lalle ne muna kasancewa, daga salihai
Sai Ya biyar musu da munafunci a cikin zukatan su har zuwa ga Ranar da suke haɗuwa da Shi saboda saɓa wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma saboda abin da suka kasance suna yi na ƙarya
Waɗanda suke aibanta masu yin alheri daga mummunaia cikin dukiyoyin sadaka, da waɗanda ba su samu face iyakar ƙoƙarinsu, sai sana yi musu izgili. Allah Yana yin izgili gare su. Kuma suna da azaba mai raɗaɗi
Ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu ba, idan ka nema musu gafara sau saba'in, to, Allah ba zai gafarta musu ba. Saboda su, sun kafirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasiƙai
Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bayan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yaƙi a cikin zafi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zafi." Da sun kasance suna fahimta
To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiya daga gare su sa'an nan suka neme ka izni domin su fita, to, ka ce: "Ba za ku fita tare da ni ba har abada, kuma ba za ku yi yaƙi tare da ni ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne ku, kun yarda da zama a farkon lokaci, sai ku zauna tare da mata masu zaman gida
Kuma kada ka yi salla a kan kowa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne su, sun kafirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhali kuwa suna fasiƙai
Kuma kada dukiyoyinsu da ɗiyansu su ba ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yana nufin Ya yi musu azaba da su a cikin duniya, kuma rayukansu su fita alhali kuwa suna kafirai
Kuma idan aka saukar da wata sura cewa; Ku yi imani da Allah kuma ku yi jihadi tare da ManzionSa. Sai mawadata daga gare su su nemi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tare da mazauna
Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi imani tare da shi, sun yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu. Kuma waɗannan suna da ayyukan alheri, kuma waɗan nan su ne masu cin nasara
Kuma masu uzuri daga ƙauyawa zuka zo domin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azaba mai raɗaɗi za ta sami waɗanda suka kafirta daga gare su
Babu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma babu laifi a kan waɗanda ba su samun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasiha* ga Allah da ManzonSa. Kuma babu wani laifi a kan masu kyautatawa. Kuma Allah ne Mai gafara, Mai tausayi
Kuma babu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka domin ka ɗauke su ka ce: "Ba ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka juya alhali kuwa idanunsu suna zubar da hawaye domin baƙin ciki cewa ba su sami abin da suke ciyarwa ba
Abin sani kawai, laifi Yana a kan waɗanda suke neman izininka alhali kuwa su mawadata ne. Sun yarda su kasance tare da mata mamaya (gidaje), kuma Allah Ya danne a kan zukatansu, domin haka su, ba su ganewa
Suna kawo uzurinsu zuwa gare ku idan kun koma zuwa gare su Ka ce: "Kada ku kawo wani uzuri, ba za mu amince muku ba. Haƙiƙa, Allah Ya ba mu labari daga labarunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa
Za su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun juya zuwa gare su, domin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don ko su ƙaranta ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sakamakon abin da suka kasance suna tsirfatawa
¡auyawa ne mafi tsananin* kafirci da munafinci, kuma sune mafi kamanta ga, rashin sanin haddojin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima
Kuma daga ƙauyawa akwai waɗanda* suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tara ce, kuma suna sauraron aukuwar masifa a gare ku, aukuwar mummunar masifa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani
Kuma daga ƙauyawa akawi waɗanda suke yin imanida Allah da Ranar Lahira, kuma suna riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibadodin neman kusanta ne a wurin Allah da addu'o'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibadar neman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Kuma masu tserewa* na farko daga Muhajirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatawa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi masu tattalin gidajen Aljanna; ¡oramu suna gudana a ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma
Kuma daga waɗanda suke a gefenku daga ƙauyawa akwai munafukai,* haka kuma daga mutanen Madnia. Sun goge a kan munafunci, ba ka sanin su, Mu ne Muke sanin su. za Mu yi musu azaba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azaba mai girma
Kuma da waɗansu, sun yi furuci* da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammanin Allah Ya karɓi tuba a kansu. Lallai Allah ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Ka karɓi sadaka daga dukiyoyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'o'inKa natsuwa ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani
Shin, ba su sani ba cewa lallai Allah, ne Yake karɓar tuba daga bayin Sa, kuma Yana karɓar sadakokin su, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai
Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da Manzon Sa da Muminai kuma za a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa
Kuma waɗanda* suka riƙi wani masallaci domin cuta da kafirci da neman rarrabewa a tsakanin muminai da fakewa ga taimakon wanda ya yaƙi Allah da ManzonSa daga gabani, kuma haƙiƙa suna yin rantsuwa cewa, "Ba mu yi nufin komai ba face alheri", alhali kuwa Allah Yana yin shaida cewa, su, haƙiƙa, maƙaryata ne
Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsashinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shi ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza suna son su tsarkaka*. Kuma Allah Yana son masu neman tsarkakuwa
Shin, wanda ya sanya harsashin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alheri ko kuwa wanda ya sanya harsashin gininsa a kan gaɓar rami mai tusgawa? Sai ya rusa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane Azzalumai
Lalle ne, Allah Ya saya* daga mummunai, rayukansu da dukiyoyinsu, da cewa suna da Aljanna, suna yin yaƙi a cikin hanyar Allah, saboda haka suna kashewa ana kashe su. (Allah Ya yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjila da Alƙur'ani. Kuma wane ne mafi cikawa da alkawarinsa daga Allah? Saboda haka ku yi bushara da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma
Masu* tuba, masu bautawa, masu godewa, masu tafiya, masu ruku'i, masu sujada masu umurni da alheri da masu hani daga abin da aka ƙi da masu tsarewaa ga iyakokin Allah. Kuma ka bayar da bushara ga muminai
Ba ya kasancew*a ga Annabi da waɗanda suka yi imani, su yi istigifari ga mushirikai, kuma ko da sun kasance ma'abuta zumunta ne daga bayan sun bayyana a gare su, cewa lalle ne, su, 'yan Jahim ne
Kuma istigifarin Ibrahim ga ubansa bai kasance ba face saboda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lokacin da ya bayyana a gare shi (Ibrahim) cewa lalle ne shi (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙiƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri
Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutane a bayan Ya shiryar da su ba, sai Ya bayyana musu abin da za su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kome, Masani ne
Lalle ne, haƙiƙa, Allah Ya karɓi tubar Anbabi da* Muhajirina da Ansar waɗanda suka bi shi, a cikin sa'ar tsanani, daga baya zukatan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tubarsu. Lalle, Shi ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su
Kuma (Allah) Ya karɓi tuba a kan ukun* nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rayukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton babu wata mafaka daga Allah face (komawa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tubarsu, domin su tabbata a kan tuba. Lalle Allah ne Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai
Ba ya kasancewa* ga mutanen Madina da wanda yake a gefensu, daga ƙauyawa, su saba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rayukansu daga ransa. Wancan, saboda ƙishirwa ba ta samun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma ba su takin wani mataki wanda yake takaitar da kafirai kuma ba su samun wani samu daga maƙiyi face an rubuta musu da shi, ladar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah ba Ya tozarta ladar masu kyautatawa
Kuma ba su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama ko babba, kuma ba su keta wani rafi sai an rubuta musu, domin Allah Ya saka musu da mafi kyawon abin da suka kasance suna aikatawa
Kuma ba ya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaƙi gaba ɗaya.* Saboda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargaɗi ga mutanen su idan sun koma zuwa gare su, tsammanin su, suna yin sauna
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yaƙi waɗanda suke kusantar* ku daga kafirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cewa Allah Yana tare da masu taƙawa
Kuma idan aka saukar* da wata sura, to, daga gare su akwai waɗanda suke cewa: "Wane a cikinku wannan sura ta ƙara masa imani?" To amma waɗanda suka yi imani, kuma su, suna yin bushara (da ita)
Kuma idan haƙiƙa, aka saukar da wata sura, sai sashensu ya yi dubi zuwa ga wani sashe, (su ce): "Shin, wani mutum yana ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su juya. Allah Ya juyar da zukatan su, domin, haƙiƙa su mutane ne, ba su fahimta
Lalle ne, haƙiƙa, Manzo* daga cikinku ya je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne saboda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai