Back to Languages

Hausa - Chapter 67

Translation by Abubakar Mahmood Jummi

Verse 1

(Allah), Wanda gudanar da mulki yake ga hannun Sa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai iko ne a kan kome

Verse 2

Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba ku, Ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawon aiki, Shi ne Mabuwayi, Mai gafara

Verse 3

Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙoƙi a kan juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sake dubawa, ko za ka ga wata ɓaraka

Verse 4

Sa'an nan ka sake maimaita, dubawa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa ba

Verse 5

Kuma lalle Mun ƙawata samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azabar Sa'ir

Verse 6

Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azabar Jahannama, ta munana ga zamanta makomarsu

Verse 7

Idan an jefa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙara, tana tafasa

Verse 8

Tana kusa ta tsage domin hushi, ko da yaushe aka jefa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba

Verse 9

Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, ba ku cikin kome sai ɓata babba

Verse 10

Kuma suka ce: "Da mun zamo muna saurare, ko muna da hankali, da ba mu kasance a cikin 'yan sa'ir ba

Verse 11

Wato su yi iƙrari da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ir

Verse 12

Lalle waɗanda ke tsoron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gafara da wani sakamako mai girma

Verse 13

Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza

Verse 14

Ashe, wanda Ya yi halitta ba zai iya saninta ba, alhali kuwa shi Mai tausasawa ne, kuma Mai labartawa

Verse 15

Shi, (Allah), Ya sanya muku ƙasa horarriya, sai ku tafi cikin sasanninta, kuma ku ci daga arzikin Sa, kuma zuwa gare shi ne tashin yake

Verse 16

Shin ko kun amince cewa wanda ke cikin sama, ba zai iya shafe ƙasa tare da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza

Verse 17

Ko kun amince cewa wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To, za ku san yadda (aƙibar) gargaɗi Na take

Verse 18

Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yaya (aƙibar) gargaɗi Na ta kasance

Verse 19

Ba za su yi dubi ba zuwa ga tsuntsaye a kansu, masu sanwa, kuma suna fiffikawa, babu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kome

Verse 20

Wane ne wanda zai zame muku mayaƙin da zai taimake ku, wanda ba (Allah) ba, Mai rahama? Kafirai ba su a cikin kome face ruɗu

Verse 21

Wane ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikin Sa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tashin hankali

Verse 22

Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa ya fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya

Verse 23

Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunani, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku

Verse 24

Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasa, kuma zuwa gare Shi ne ake tashin ku

Verse 25

Kuma suna cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance masu gaskiya ne ku

Verse 26

Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)

Verse 27

To, lokacin da suka gan ta (azabar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kafirta suka munana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatawa

Verse 28

Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni ni da wanda ke tare da ni, ko kuma, Ya yi mana rahama, to, wane ne zai tserar da kafirai daga wata azaba mai raɗaɗi

Verse 29

Ka ce: "Shi ne Mai rahama mun yi imani da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka za ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya

Verse 30

Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wayi gari faƙaƙƙe, to, wane ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga