Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 72 - Al-Jinn
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Jinn 72:1
Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saururi (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mu mun ji wani abin karantawa (Alƙui'ani), mai ban mamaki
Verse 2 — Surah Al-Jinn 72:2
Yana nuni zuwa ga hanyar ƙwarai, saboda haka mun yi imani da shi ba za mu koma bauta wa Ubangijinmu tare da kowa ba
Verse 3 — Surah Al-Jinn 72:3
Kuma lalle ne shi girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mata ba, kuma bai riƙi ɗa ba
Verse 4 — Surah Al-Jinn 72:4
Kuma lalle ne shi, wawanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah
Verse 5 — Surah Al-Jinn 72:5
Kuma lalle ne mu, mun yi zaton mutum da aljani ba za su iya faɗar ƙarya ba ga Allah
Verse 6 — Surah Al-Jinn 72:6
Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutane, sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, saboda haka suka ƙara musu girman kai
Verse 7 — Surah Al-Jinn 72:7
Kuma lalle ne su, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah ba zai aiko kowa ba
Verse 8 — Surah Al-Jinn 72:8
Kuma lalle ne mu mun nemi (hawan) sama, sai muka, same ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yulaye
Verse 9 — Surah Al-Jinn 72:9
Kuma lalle ne mu, mun kasance muna zama daga gareta, a wuraren zama domin saurare. To wanda ya yi saurare a yanzu, zai sami yula, mai dako dominsa
Verse 10 — Surah Al-Jinn 72:10
Kuma lalle ne mu ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Ya yi nufin shiriya a gare su ne
Verse 11 — Surah Al-Jinn 72:11
Kuma lalle ne mu, akwai salaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka ba mun kasance ƙungiyoyi dabam-dabam
Verse 12 — Surah Al-Jinn 72:12
Kuma lalle ne mu mun tabbata ba za mu buwayi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma ba za mu buwaye Shi da gudu ba
Verse 13 — Surah Al-Jinn 72:13
Kuma lalle ne mu, a lokacin da muka ji shiriya, mun yi imani da ita. To wanda ya yi iimani da Uhangijinsa, ba zai ji tsoron nakkasa ba, kuma ba zai ji tsoron zalunci ba
Verse 14 — Surah Al-Jinn 72:14
Kuma lalle ne mu akwai a cikinmu, waɗanda suka miƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya miƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa
Verse 15 — Surah Al-Jinn 72:15
Kuma amma karkatattu sai suka kasance makamashi ga Jahannama
Verse 16 — Surah Al-Jinn 72:16
Kuma da sun tsayu* sosai a kan hanya, da lalle Mun shayar da su ruwa mai yawa
Verse 17 — Surah Al-Jinn 72:17
Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azaba mai hauhawa
Verse 18 — Surah Al-Jinn 72:18
Kuma lalle ne wuraren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kowa tare da Allah (da su, a cikinsu)
Verse 19 — Surah Al-Jinn 72:19
Kuma, lalle ne shi, a lokacin da bawan Allah* ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa
Verse 20 — Surah Al-Jinn 72:20
Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma ba zan tara kowa da Shi ba
Verse 21 — Surah Al-Jinn 72:21
Ka ce: "Lalle ne, ni ba ni mallakar wata cuta gare ku, kuma ba ni mallakar wani alheri
Verse 22 — Surah Al-Jinn 72:22
Ka ce: "Lalle ne, ni kowa ba ya iya cetona daga Allah, kuma ba zan iya samun mafaka ba daga gare Shi
Verse 23 — Surah Al-Jinn 72:23
Face iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya saɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna masu dawwama a cikinta, har abada
Verse 24 — Surah Al-Jinn 72:24
Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, za su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi
Verse 25 — Surah Al-Jinn 72:25
Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya masa dogon ajali
Verse 26 — Surah Al-Jinn 72:26
Shi ɗai ne Masanin fake saboda haka, ba Ya bayyana gaibinsa ga kowa
Verse 27 — Surah Al-Jinn 72:27
Face ga wanda Ya yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya* gadi a gaba gare shi da baya gare shi
Verse 28 — Surah Al-Jinn 72:28
Domin Ya san lalle, sun iyar da saƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Ya kewaye su da sani, kuma Ya lissafe dukan kome da ƙididdiga