Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 71 - Nuh
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Nuh 71:1
Lalle ne Mun aiki Nuhu zuwa ga mutanensa, cewa ka yi gargaɗi ga mutanenka gabanin wata azaba mai raɗaɗi ta zo musu
Verse 2 — Surah Nuh 71:2
Ya ce: "Ya mutanena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanawa
Verse 3 — Surah Nuh 71:3
Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsoron Sa, kuma ku bi ni
Verse 4 — Surah Nuh 71:4
Allah zai gafarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, da kun kasance masana (ga abin da nake faɗa da, kun bar kafirci)
Verse 5 — Surah Nuh 71:5
(Nuhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirayi mutanena, a cikin dare da yini
Verse 6 — Surah Nuh 71:6
To, amma kirana bai ƙare su ba sai da, gudu (daga gare ni)
Verse 7 — Surah Nuh 71:7
Kuma lalle ne ni, ko da yaushe na kiraye su domin Ka gafarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufafinsu, su doge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyakar girman kai
Verse 8 — Surah Nuh 71:8
Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane
Verse 9 — Surah Nuh 71:9
Sa'an nan lalle ne, na yi yekuwa saboda su, kuma na gana da su a cikin asiri
Verse 10 — Surah Nuh 71:10
Shi na ce, 'Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gafara ne
Verse 11 — Surah Nuh 71:11
Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga
Verse 12 — Surah Nuh 71:12
Kuma ya yalwata muku game da dukiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna
Verse 13 — Surah Nuh 71:13
Me ya same ku, ba ku fatar samun natsuwa daga Allah
Verse 14 — Surah Nuh 71:14
Alhali kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin halaye
Verse 15 — Surah Nuh 71:15
Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙoƙi a kan juna ba
Verse 16 — Surah Nuh 71:16
Ya sanya wata a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rana babbar fitila
Verse 17 — Surah Nuh 71:17
Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa
Verse 18 — Surah Nuh 71:18
Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa
Verse 19 — Surah Nuh 71:19
Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya
Verse 20 — Surah Nuh 71:20
Domin ku shiga a cikinta, hanyoyi masu faɗi
Verse 21 — Surah Nuh 71:21
Nuhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne su sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙare shi da kome ba sai da hasara
Verse 22 — Surah Nuh 71:22
Kuma sun yi wani makirci, makirci babba
Verse 23 — Surah Nuh 71:23
Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumakanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwa kuma kada ku bar Yagusa da Yans uƙa da Nasra
Verse 24 — Surah Nuh 71:24
Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutane) masu yawa, kuma kada Ka ƙara wa azzalumai (kome) sai ɓata
Verse 25 — Surah Nuh 71:25
Saboda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sama wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba
Verse 26 — Surah Nuh 71:26
Kuma Nuhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kafirai, wanda ke zama a cikin gida
Verse 27 — Surah Nuh 71:27
Lalle ne, Kai idan Ka bar su, za su ɓatar da bayin Ka, kuma ba za su haifi kowa ba face fajiri mai yawan kafirci
Verse 28 — Surah Nuh 71:28
Ya Ubanginjina! Ka yi mini gafara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai imani, da muminai maza da muminai mata, kuma kada Ka ƙara wa azzalumai kome sai halaka