Back to Languages

Hausa - Chapter 70 - Al-Maarij

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Maarij 70:1

Wani mai tambaya ya yi tambaya game da azaba, mai aukuwa

Verse 2 — Surah Al-Maarij 70:2

Ga kafirai, ba ta da mai tunkuɗewa

Verse 3 — Surah Al-Maarij 70:3

Daga Allah Mai matakala

Verse 4 — Surah Al-Maarij 70:4

Mala'iku da Ruhi (Jibrila) suna takawa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shekara dubu hamsin ne

Verse 5 — Surah Al-Maarij 70:5

Saboda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyawo

Verse 6 — Surah Al-Maarij 70:6

Lalle ne su, suna ganin ta mai nisa

Verse 7 — Surah Al-Maarij 70:7

Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa

Verse 8 — Surah Al-Maarij 70:8

Ranar da sama za ta kasance kamar narkakkar azurfa

Verse 9 — Surah Al-Maarij 70:9

Kuma duwatsu su zama kamar saɓin sufi

Verse 10 — Surah Al-Maarij 70:10

Kuma aboki ba ya tambayar inda wani aboki yake

Verse 11 — Surah Al-Maarij 70:11

Ana sanya su, su gajuna, mai laifi na gurin da zai iya yin fansa, daga azabar ranar nan, da ɗiyansa

Verse 12 — Surah Al-Maarij 70:12

Da matarsa da ɗan'uwansa

Verse 13 — Surah Al-Maarij 70:13

Da danginsa, masu tattara shi

Verse 14 — Surah Al-Maarij 70:14

Da wanda ke a cikin duniya duka gaba ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsirar da shi

Verse 15 — Surah Al-Maarij 70:15

A'aha! Lalle ne fa, ita ce Laza

Verse 16 — Surah Al-Maarij 70:16

Mai twale fatar goshi

Verse 17 — Surah Al-Maarij 70:17

Tana kiran wanda ya juya baya (daga addini) kuma ya kau da kai

Verse 18 — Surah Al-Maarij 70:18

Ya tara (dukiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka

Verse 19 — Surah Al-Maarij 70:19

Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi

Verse 20 — Surah Al-Maarij 70:20

Idan sharri ya shafe shi, ya kasa haƙuri

Verse 21 — Surah Al-Maarij 70:21

Kuma idan alheri ya shafe shi, ya yi rowa

Verse 22 — Surah Al-Maarij 70:22

Verse 23 — Surah Al-Maarij 70:23

Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, masu dawwama ne

Verse 24 — Surah Al-Maarij 70:24

Kuma waɗanda a cikin dukiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne

Verse 25 — Surah Al-Maarij 70:25

Ga (matalauci) mai roƙo da wanda aka hana wa roƙon

Verse 26 — Surah Al-Maarij 70:26

Da waɗannan da ke gaskata ranar sakamako

Verse 27 — Surah Al-Maarij 70:27

Da waɗannan saboda azabar Ubangijinsu, suna jin tsoro

Verse 28 — Surah Al-Maarij 70:28

Lalle ne, azabar Ubangijinsu ba wadda ake iya amincewaba ce

Verse 29 — Surah Al-Maarij 70:29

Da waɗanda suke, ga farjojinsu, masu tsarewa ne

Verse 30 — Surah Al-Maarij 70:30

Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dama suka mallaka. To lalle ne sukam ba waɗanda ake zargi ba ne

Verse 31 — Surah Al-Maarij 70:31

To, duk wanda ya nemi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan su ne masu ƙetare iyaka

Verse 32 — Surah Al-Maarij 70:32

Kuma da waɗannan da suke ga amanoninsu da alkawarinsu masu tsarewa ne

Verse 33 — Surah Al-Maarij 70:33

Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, masu dagewa ne

Verse 34 — Surah Al-Maarij 70:34

Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, masu tsarewa ne

Verse 35 — Surah Al-Maarij 70:35

Waɗannan, a cikin gidajen Aljanna, waɗanda ake girmamawa ne

Verse 36 — Surah Al-Maarij 70:36

Me ya sami waɗanda suka kafirta, a wajenka, suna gaugawar (gudu)

Verse 37 — Surah Al-Maarij 70:37

Daga jihar dama, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a

Verse 38 — Surah Al-Maarij 70:38

Shin kowane mutum daga cikinsu yana neman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)

Verse 39 — Surah Al-Maarij 70:39

A'aha! Lalle Mu, Mun halitta su, daga abin da suka sani

Verse 40 — Surah Al-Maarij 70:40

Saboda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wuraren ɓullowar rana da wuraren faɗuwarta ba, lalle Mu, Masu iyawa ne

Verse 41 — Surah Al-Maarij 70:41

Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alheri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjaya ba

Verse 42 — Surah Al-Maarij 70:42

Saboda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wasa, har su haɗu da ranarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita)

Verse 43 — Surah Al-Maarij 70:43

Ranar da suke fitowa daga kaburbura da gaugawa, kamar su, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugawa

Verse 44 — Surah Al-Maarij 70:44

Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa)