Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 69 - Al-Haqqah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Haqqah 69:1
Kiran gaskiya
Verse 2 — Surah Al-Haqqah 69:2
Mene ne kiran gaskiya
Verse 3 — Surah Al-Haqqah 69:3
Kuma me ya sanar da kai abin da ake cewa kiran gaskiya
Verse 4 — Surah Al-Haqqah 69:4
Samudawa da Adawa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dukar zuciya
Verse 5 — Surah Al-Haqqah 69:5
To, amma Samudawa to, an halakasu da tsawa mai tsanani
Verse 6 — Surah Al-Haqqah 69:6
Kuma amma Adawa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙetare haddi
Verse 7 — Surah Al-Haqqah 69:7
(Allah) Ya hore ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da juna, saboda haka, kana ganin mutane a cikinta kwance. Kamar su ƙiraruwan dabino ne, waɗanda suka faɗi
Verse 8 — Surah Al-Haqqah 69:8
To, ko kana ganin abin da ya yi saura daga cikinsu
Verse 9 — Surah Al-Haqqah 69:9
Kuma Fir'auna ya zo da waɗanda ke gabaninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, saboda laifi
Verse 10 — Surah Al-Haqqah 69:10
Domin sun saɓa wa manzon Ubangijinsu, saboda haka ya kama su da wani irin kamu mai ƙaruwar (tsanani)
Verse 11 — Surah Al-Haqqah 69:11
Lalle ne, Mu, a lokacin da ruwa ya ƙetare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan
Verse 12 — Surah Al-Haqqah 69:12
Domin Mu sanya shi, gare ku abin tunawa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi)
Verse 13 — Surah Al-Haqqah 69:13
To, idan an yi busa a cikin ƙaho, busa ɗaya
Verse 14 — Surah Al-Haqqah 69:14
Kuma aka ɗauki ƙasa da duwatsu, kuma aka niƙa su niƙawa ɗaya
Verse 15 — Surah Al-Haqqah 69:15
A ran nan, mai aukuwa za ta auku
Verse 16 — Surah Al-Haqqah 69:16
Kuma sama za ta tsage, domin ita a ran nan, mai rauni ce
Verse 17 — Surah Al-Haqqah 69:17
Kuma mala'iku (su bayyana) a kan sasanninta, kuma wasu (mala'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan ranar
Verse 18 — Surah Al-Haqqah 69:18
A ranar nan za a bijira ku (domin hisabi), babu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓoyewa
Verse 19 — Surah Al-Haqqah 69:19
To, amma wanda aka bai wa littafinsa a damansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina
Verse 20 — Surah Al-Haqqah 69:20
Lalle ne ni, na tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisabina ne
Verse 21 — Surah Al-Haqqah 69:21
Saboda haka, shi yana cikin wata rayuwa yardadda
Verse 22 — Surah Al-Haqqah 69:22
A cikin Aljanna maɗaukakiya
Verse 23 — Surah Al-Haqqah 69:23
Nunannun 'ya'yan itacenta makusanta ne (ga mai son ɗiba)
Verse 24 — Surah Al-Haqqah 69:24
(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, saboda abin da kuka gabatar a cikin kwanukan da suka shige
Verse 25 — Surah Al-Haqqah 69:25
Kuma wanda aka bai wa littafinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kawo mini littafina ba
Verse 26 — Surah Al-Haqqah 69:26
Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisabina ba
Verse 27 — Surah Al-Haqqah 69:27
In da dai ita, ta kasance mai halaka ni gaba ɗaya ce
Verse 28 — Surah Al-Haqqah 69:28
Dukiyata ba ta wadatar da ni ba
Verse 29 — Surah Al-Haqqah 69:29
Ikona ya ɓace mini
Verse 30 — Surah Al-Haqqah 69:30
(Sai a ce wa mala'iku) "Ku kama shi, sa'an nan ku sanya shi a cikin ƙuƙumi
Verse 31 — Surah Al-Haqqah 69:31
Sa'an nan, a cikin Jahim, ku ƙona shi
Verse 32 — Surah Al-Haqqah 69:32
Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zira'i saba'in, sai ku sanya shi
Verse 33 — Surah Al-Haqqah 69:33
Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin imani da Allah, Mai girma
Verse 34 — Surah Al-Haqqah 69:34
Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bayar da) abincin matalauci
Verse 35 — Surah Al-Haqqah 69:35
Saboda haka, a yau, a nan, ba ya da masoyi
Verse 36 — Surah Al-Haqqah 69:36
Kuma babu wani abinci, sai daga (itacen) gislin
Verse 37 — Surah Al-Haqqah 69:37
Babu mai cin sa sai masu ganganci
Verse 38 — Surah Al-Haqqah 69:38
To, ba sai Na yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba
Verse 39 — Surah Al-Haqqah 69:39
Da abin da ba ku iya gani
Verse 40 — Surah Al-Haqqah 69:40
Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne
Verse 41 — Surah Al-Haqqah 69:41
Kuma shi ba maganar wani mawaƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai za ku gaskata
Verse 42 — Surah Al-Haqqah 69:42
Kuma ba maganar boka ba ne. Kaɗan ƙwarai za ku iya tunawa
Verse 43 — Surah Al-Haqqah 69:43
Abin saukarwa ne daga Ubangijin halitta duka
Verse 44 — Surah Al-Haqqah 69:44
Kuma da (Muhammadu) ya faɗi wata magana, ya jingina ta gare Mu
Verse 45 — Surah Al-Haqqah 69:45
Da Mun kama shi da dama
Verse 46 — Surah Al-Haqqah 69:46
sa'an nan, lalle ne, da Mun katse masa laka
Verse 47 — Surah Al-Haqqah 69:47
Kuma daga cikinku babu wasu masu iya kare (azabar Mu) daga gare shi
Verse 48 — Surah Al-Haqqah 69:48
Kuma lalle ne shi (Alƙur'ani) tanatarwa ce ga masu taƙawa
Verse 49 — Surah Al-Haqqah 69:49
Kuma lalle, ne Mu, wallahi Muna sane da cewa daga cikinku alwwai masu ƙaryatawa
Verse 50 — Surah Al-Haqqah 69:50
Kuma lalle ne shi (Alƙarani) wallahi baƙin ciki ne ga kafirai
Verse 51 — Surah Al-Haqqah 69:51
Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini
Verse 52 — Surah Al-Haqqah 69:52
Saboda haka, ka tsarkake sunan Ubangjinka, mai girma