Back to Languages

Hausa - Chapter 68 - Al-Qalam

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Qalam 68:1

N. Na rantse da alƙalami da abin da (marubuta) suke rubutawa

Verse 2 — Surah Al-Qalam 68:2

Kai, saboda ni'imar Ubangijinka, ba mahaukaci kake ba

Verse 3 — Surah Al-Qalam 68:3

Kuma, lalle, haƙiƙa kana da ladar da ba ta yankewa

Verse 4 — Surah Al-Qalam 68:4

Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan halayen kirki, manya

Verse 5 — Surah Al-Qalam 68:5

Don haka, za ka gani, su kuma za su gani

Verse 6 — Surah Al-Qalam 68:6

Ga wanenku hauka take

Verse 7 — Surah Al-Qalam 68:7

Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga masu shiryuwa

Verse 8 — Surah Al-Qalam 68:8

Saboda haka kada ka bi masu ƙaryatawa

Verse 9 — Surah Al-Qalam 68:9

Suna fatar ka sassauta, su kuma su sassauta

Verse 10 — Surah Al-Qalam 68:10

Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walakantacce

Verse 11 — Surah Al-Qalam 68:11

Mai zunɗe, mai yawo da gulma

Verse 12 — Surah Al-Qalam 68:12

Mai hana alheri mai zalunci, mai zunubi

Verse 13 — Surah Al-Qalam 68:13

Mai girman kai, bayan haka kuma la'imi (ba ya son alheri)

Verse 14 — Surah Al-Qalam 68:14

Saboda ya kasance mai dukiya da ɗiya

Verse 15 — Surah Al-Qalam 68:15

Idan ana karanta masa ayoyin Mu, sai ya ce: "Tatsuniyoyin mutanen farko ne

Verse 16 — Surah Al-Qalam 68:16

Za Mu yi masa alama a kan hanci

Verse 17 — Surah Al-Qalam 68:17

Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi masu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle za su girbe amfaninta, suna masu asubanci

Verse 18 — Surah Al-Qalam 68:18

Kuma (suka yi niyya), ba su ko togewa

Verse 19 — Surah Al-Qalam 68:19

Wani mai kewayawa daga Ubangijinka ya kewaya a kanta, (ya ƙone ta,) alhali suna barci

Verse 20 — Surah Al-Qalam 68:20

Sai ta wayi gari (baƙa ƙirin) kamar dare

Verse 21 — Surah Al-Qalam 68:21

Sai suka kirayi juna, suna masu yin asubanci

Verse 22 — Surah Al-Qalam 68:22

Cewa ku yi sammako ga amfanin gonarku, idan kun kasance masu girbewa

Verse 23 — Surah Al-Qalam 68:23

Sai suka tafi suna shawara a ɓoye (suna cewa)

Verse 24 — Surah Al-Qalam 68:24

Lalle kada wani miskini ya shigar muku ita a yau

Verse 25 — Surah Al-Qalam 68:25

Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rowa, matuƙar iyawarsu

Verse 26 — Surah Al-Qalam 68:26

Lokacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)

Verse 27 — Surah Al-Qalam 68:27

Ba haka ba, mu dai, an hana mu ne

Verse 28 — Surah Al-Qalam 68:28

Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, ya kamata ku tsarkake Allah

Verse 29 — Surah Al-Qalam 68:29

Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzalumai

Verse 30 — Surah Al-Qalam 68:30

Sai suka fuskanci juna, suna zargin kansu

Verse 31 — Surah Al-Qalam 68:31

Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mu ne muka kasance masu ƙetare iyaka

Verse 32 — Surah Al-Qalam 68:32

Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da ya fi ta. Lalle, mu (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, masu kwaɗayi ne

Verse 33 — Surah Al-Qalam 68:33

Haka dai azabar* take, kuma lalle ne azabar Lahira ta fi girma, in da sun kasance za su iya ganewa

Verse 34 — Surah Al-Qalam 68:34

Lalle ne masu taƙawa na da a wurin Ubangijinsu, gidajen Aljanna na ni'ima

Verse 35 — Surah Al-Qalam 68:35

Shin ko za Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar masu laifi

Verse 36 — Surah Al-Qalam 68:36

Me ya same ku, yaya kuke yin hukunci (da haka)

Verse 37 — Surah Al-Qalam 68:37

Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantawa

Verse 38 — Surah Al-Qalam 68:38

Cewa kuna da, a cikinsa lalle (duk) abin da rayukanku suka zaɓa

Verse 39 — Surah Al-Qalam 68:39

Ko kuna (riƙe) da wasu rantsuwoyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Ranar ¡iyama, cewa lalle ne kuna da abin da kuke hukunta wa kanku

Verse 40 — Surah Al-Qalam 68:40

Ka tambaye su, wane, a cikinsu, ke lamuncewa ga samun wannan (hukuncin)

Verse 41 — Surah Al-Qalam 68:41

Ko suna da abokan tarewa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kawo abokan tarayyarsu, idan sun kasance masu gaskiya

Verse 42 — Surah Al-Qalam 68:42

Ranar da za a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai ba za su iyawa ba

Verse 43 — Surah Al-Qalam 68:43

Su fito da idanu ƙasƙantattu, wulakanci yana rufe su. Lalle ne a da sun kasance ana kiran su zuwa, yin sujudar, alhali kuwa suna lafiya lau, (suka ƙi yi)

Verse 44 — Surah Al-Qalam 68:44

Saboda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna labari (Alƙur'ani). Za Mu yi musu istidraji daga inda ba su sani ba

Verse 45 — Surah Al-Qalam 68:45

Ina jinkirta musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne

Verse 46 — Surah Al-Qalam 68:46

Ko kana tambayar su wata la'ada ne, saboda haka su, daga wannan tarar, suke jin an nauyaya musu

Verse 47 — Surah Al-Qalam 68:47

Ko kuma suna da ilmin gaibu ne, wato suna yin rubutun (abin da suke faɗa daga gare shi) ne

Verse 48 — Surah Al-Qalam 68:48

Saboda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abucin kifi, alokacin da ya yi kira, alhali yana cike da hushi

Verse 49 — Surah Al-Qalam 68:49

Ba domin ni'ima daga wajen Ubangijinsa ta riske shi ba, lalle ne da an jefa shi a cikin wofintacciyar ƙasa, alhali yana abin zargi

Verse 50 — Surah Al-Qalam 68:50

Sai Ubangijinsa Ya zaɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutanen kirki

Verse 51 — Surah Al-Qalam 68:51

Kuma lalle, ne waɗanda suka kafirta suna yin kamar su kayar da kai sabo da kallonsu (kallon mamaki), a lokacin da suke jin karatun Alƙur'ani, kuma suna cewa, "Lalle ne shi mahaukaci ne

Verse 52 — Surah Al-Qalam 68:52

Shi (Alƙur'ani) bai kasance ba, face abin tunatarwa ne ga duka duniya