Back to Languages
Hausa - Chapter 73
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Ya wanda ya lulluɓe
Verse 2
Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) face kaɗan
Verse 3
Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi
Verse 4
Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ani, daki daki
Verse 5
Lalle ne, Mu, za Mu jefa maka magana mai nauyi
Verse 6
Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana
Verse 7
Lalle ne, kana da, a cikin yini, wani tasihi mai tsawo
Verse 8
Kuma ka ambaci sunan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa
Verse 9
Shi ne Ubangijin mafitar rana da mafaɗarta, babu abin bautawa face Shi. Saboda haka ka riƙe Shi wakili
Verse 10
Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗa, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracewa mai kyawo
Verse 11
Kuma ka bar Ni da masu ƙaryatawa, mawadata, kuma ka jinkirta musu kaɗan
Verse 12
Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu maruruwa masu nauyi da Jahim
Verse 13
Da wani abinci mai maƙara da azaba mai raɗaɗi
Verse 14
Ranar da ƙasa ke raurawa, da duwatsu kuma duwatsu su kasance tudun rairayi mai malala
Verse 15
Lalle ne, Mu. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo* mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo** zuwaga Fir'auna
Verse 16
Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kama shi kamu mai tsanani
Verse 17
To, yaya, idan kun kafirta, za ku kare (azabar) wani yini mai mayar da yara (tsofaffi) masu hurhura
Verse 18
Sama za ta tsage a cikinsa, wa'adinsa ya kasance mai aukuwa
Verse 19
Lalle ne, wannan wata tunatarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kama hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa
Verse 20
Lalle ne, Ubangijinka Ya sani cewa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tare da wani ɓangare na waɗanda ke tare da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san ba za ku iya lissafa shi ba, saboda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ani. Ya san wasu daga cikinku, za su yi ciwo, kuma wasu za su yi tafiya cikin ƙasa suna neman falalar Allah da fatauci, kuma wasu za su yi yaƙi a cikin banyar Allah. Saboda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bayar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyawo. Kuma abin da kuka gabatar domin kanku, na alheri, za ku same shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku roƙi Allah gafara; lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai