Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 74 - Al-Muddaththir
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Muddaththir 74:1
Ya wanda ya lulluɓa da mayafi
Verse 2 — Surah Al-Muddaththir 74:2
Ka tashi domin ka yi gargaɗi
Verse 3 — Surah Al-Muddaththir 74:3
Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi
Verse 4 — Surah Al-Muddaththir 74:4
Kuma tutafinka, sai ka tsarkake su
Verse 5 — Surah Al-Muddaththir 74:5
Kuma gumaka, sai ka ƙaurace musu
Verse 6 — Surah Al-Muddaththir 74:6
Kada ka yi kyauta kana neman ƙari
Verse 7 — Surah Al-Muddaththir 74:7
Kuma saboda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
Verse 8 — Surah Al-Muddaththir 74:8
To, idan aka yi busa a cikin ƙaho
Verse 9 — Surah Al-Muddaththir 74:9
To, wannan, a ranar nan, yini ne mai wuya
Verse 10 — Surah Al-Muddaththir 74:10
A kan kafirai, ba mai sauƙi ba ne
Verse 11 — Surah Al-Muddaththir 74:11
Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai
Verse 12 — Surah Al-Muddaththir 74:12
Kuma Na sanya masa dukiya shimfiɗaɗɗiya
Verse 13 — Surah Al-Muddaththir 74:13
Da ɗiya halartattu
Verse 14 — Surah Al-Muddaththir 74:14
Kuma Na shimfiɗa? masa kome shimfiɗawa
Verse 15 — Surah Al-Muddaththir 74:15
Sa'an nan, yana kwaɗayin in yi masa ƙari
Verse 16 — Surah Al-Muddaththir 74:16
Faufau! Lalle ne, shi ya kasance, ga ayoyin Mu, mai tsaurin kai
Verse 17 — Surah Al-Muddaththir 74:17
Za Ni kallafa masa wahala mai hauhawa
Verse 18 — Surah Al-Muddaththir 74:18
Lalle ne, Shi, ya yi tunani, kuma ya ƙaddara (abin da zai faɗa game da Alƙur'ani)
Verse 19 — Surah Al-Muddaththir 74:19
Saboda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara
Verse 20 — Surah Al-Muddaththir 74:20
Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara
Verse 21 — Surah Al-Muddaththir 74:21
Sa'an nan, ya yi tunani
Verse 22 — Surah Al-Muddaththir 74:22
Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk
Verse 23 — Surah Al-Muddaththir 74:23
Sa'an nan, ya juya baya, kuma ya bunƙasa
Verse 24 — Surah Al-Muddaththir 74:24
Sai ya ce: "Wannan abu dai ba kome ba ne face wani sihiri, wanda aka ruwaito
Verse 25 — Surah Al-Muddaththir 74:25
Wannan maganar mutum dai ce
Verse 26 — Surah Al-Muddaththir 74:26
Za Ni ƙona shi da Saƙar
Verse 27 — Surah Al-Muddaththir 74:27
Kuma me ya sanar da kai abin da ake cewa Saƙar
Verse 28 — Surah Al-Muddaththir 74:28
Ba ta ragewa, kuma ba ta bari
Verse 29 — Surah Al-Muddaththir 74:29
Mai nacewa ga jiki ce (da (ƙuna)
Verse 30 — Surah Al-Muddaththir 74:30
A kanta akwai (matsara) goma sha tara
Verse 31 — Surah Al-Muddaththir 74:31
Kuma ba Mu sanya ma'abuta wuta (wato matsaranta) ba, face mala'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (goma sha tara) ba, face domin fitina ga waɗanda suka kafirta domin waɗanda aka bai wa littafi su sami yaƙini kuma waɗanda suka yi imani su ƙara imani, kuma waɗanda aka bai wa littafi da muminai ba za su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kafirai su ce: "Me Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misali?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma babu wanda ya san mayaƙan Ubangijinka face Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba face wata tunatarwa ce ga mutum
Verse 32 — Surah Al-Muddaththir 74:32
A'aha! Ina rantsuwa da wata
Verse 33 — Surah Al-Muddaththir 74:33
Da dare a lokacin da ya juyar da baya
Verse 34 — Surah Al-Muddaththir 74:34
Da safiya idan ta waye
Verse 35 — Surah Al-Muddaththir 74:35
Ita (wutar) ɗayan manyan masifu? ce
Verse 36 — Surah Al-Muddaththir 74:36
Mai gargaɗi ce ga mutum
Verse 37 — Surah Al-Muddaththir 74:37
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabata ko ya jinkirta
Verse 38 — Surah Al-Muddaththir 74:38
Kowane rai ga abin da ya aikata jingina ce
Verse 39 — Surah Al-Muddaththir 74:39
Face mutanen dama
Verse 40 — Surah Al-Muddaththir 74:40
A cikin Aljanna suna tambayar juna
Verse 41 — Surah Al-Muddaththir 74:41
Game da masu laifi
Verse 42 — Surah Al-Muddaththir 74:42
(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar
Verse 43 — Surah Al-Muddaththir 74:43
Suka ce: "Ba mu kasance muna a cikin masu salla ba
Verse 44 — Surah Al-Muddaththir 74:44
Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalauta ba
Verse 45 — Surah Al-Muddaththir 74:45
Kuma mun kasance muna kutsawa tare da masu kutsawa
Verse 46 — Surah Al-Muddaththir 74:46
Mun kasance muna ƙaryata ranar sakamako
Verse 47 — Surah Al-Muddaththir 74:47
Har gaskiya (wato mutuwa) ta zo mana
Verse 48 — Surah Al-Muddaththir 74:48
Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba
Verse 49 — Surah Al-Muddaththir 74:49
Haba! Me ya same su, suka zama masu bijirewa daga wa'azin gaskiya
Verse 50 — Surah Al-Muddaththir 74:50
Kamar dai su, jakuna firgitattu ne
Verse 51 — Surah Al-Muddaththir 74:51
Sun gudu daga zaki
Verse 52 — Surah Al-Muddaththir 74:52
A'aha! Kowane mutum daga cikinsu yana son a zo masa da takardu (da sunansa) ana watsawa
Verse 53 — Surah Al-Muddaththir 74:53
A'aha! Kai dai, ba su jin tsoron Lahira
Verse 54 — Surah Al-Muddaththir 74:54
A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tunatarwa ce
Verse 55 — Surah Al-Muddaththir 74:55
Domin wanda ya so, ya tuna
Verse 56 — Surah Al-Muddaththir 74:56
Kuma ba za su tuna ba face idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gafara