Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 75 - Al-Qiyamah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Qiyamah 75:1
Ba sai Na yi rantsuwa* da Ranar ¡iyama ba
Verse 2 — Surah Al-Qiyamah 75:2
Ba sai Na yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba
Verse 3 — Surah Al-Qiyamah 75:3
Sin, mutum yana zaton cewa ba za Mu tara ƙasusuwansa ba
Verse 4 — Surah Al-Qiyamah 75:4
Na'am! Masu ikon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓoɓin yatsunsa
Verse 5 — Surah Al-Qiyamah 75:5
Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fajirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa
Verse 6 — Surah Al-Qiyamah 75:6
Yana tambaya: "Yaushe ne Ranar ¡iyama
Verse 7 — Surah Al-Qiyamah 75:7
To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli)
Verse 8 — Surah Al-Qiyamah 75:8
Kuma, wata ya yi husufi (haskensa ya dushe)
Verse 9 — Surah Al-Qiyamah 75:9
Aka tara rana da wata
Verse 10 — Surah Al-Qiyamah 75:10
Mutum zai ce a ran nan "Ina wurin gudu
Verse 11 — Surah Al-Qiyamah 75:11
A'aha! babu mafaka
Verse 12 — Surah Al-Qiyamah 75:12
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a ranar nan, yake
Verse 13 — Surah Al-Qiyamah 75:13
Ana gaya wa mutum, a ranar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar
Verse 14 — Surah Al-Qiyamah 75:14
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne
Verse 15 — Surah Al-Qiyamah 75:15
Kuma ko da ya jefa uzurorinsa (ba za a saurare shi ba)
Verse 16 — Surah Al-Qiyamah 75:16
Kada ka motsar* da harshenka game da shi domin ka yi gaugawar riƙe shi (Alƙur'ani)
Verse 17 — Surah Al-Qiyamah 75:17
Lalle ne, wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi. Mu (tsare maka) karatunsa
Verse 18 — Surah Al-Qiyamah 75:18
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa
Verse 19 — Surah Al-Qiyamah 75:19
sa'an nan, lalle wajibi ne a gare Mu, bayaninsa
Verse 20 — Surah Al-Qiyamah 75:20
A'aha! Ba haka ba kuna son mai gaugawar nan (duniya) ne
Verse 21 — Surah Al-Qiyamah 75:21
Kuna barin ta ƙarshen (Lahira)
Verse 22 — Surah Al-Qiyamah 75:22
Wasu huskoki, a ranar nan, masu annuri ne
Verse 23 — Surah Al-Qiyamah 75:23
Zuwa ga Ubangijinsu masu kallo ne
Verse 24 — Surah Al-Qiyamah 75:24
Wasu huskoki, a ranar nan, masu gintsewa ne
Verse 25 — Surah Al-Qiyamah 75:25
Suna zaton a sako musu masifa mai karya tsatso
Verse 26 — Surah Al-Qiyamah 75:26
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai
Verse 27 — Surah Al-Qiyamah 75:27
kuma aka ce: "Wane ne mai tawada
Verse 28 — Surah Al-Qiyamah 75:28
Kuma ya tabbata cewa rabuwa dai ce
Verse 29 — Surah Al-Qiyamah 75:29
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri
Verse 30 — Surah Al-Qiyamah 75:30
Zuwa ga Ubangijinka, a ranar nan, magargaɗa* take
Verse 31 — Surah Al-Qiyamah 75:31
To, bai gaskata ba, kuma bai yi salla ba
Verse 32 — Surah Al-Qiyamah 75:32
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya juya baya
Verse 33 — Surah Al-Qiyamah 75:33
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutanensa, yana taƙama
Verse 34 — Surah Al-Qiyamah 75:34
Halaka ta tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dacewa
Verse 35 — Surah Al-Qiyamah 75:35
Sa'an nan, wata halaka ta tabbata a gare ka domin ta fi dace wa
Verse 36 — Surah Al-Qiyamah 75:36
Shin, mutum na zaton a bar shi sagaga (wato babu nufin kome game da shi)
Verse 37 — Surah Al-Qiyamah 75:37
Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
Verse 38 — Surah Al-Qiyamah 75:38
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓoɓinsa
Verse 39 — Surah Al-Qiyamah 75:39
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace
Verse 40 — Surah Al-Qiyamah 75:40
Ashe wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rayar da matattu