Back to Languages

Hausa - Chapter 76 - Al-Insan

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Insan 76:1

Lalle ne, wata mudda ta zamani ta zo a kan mutum, bai kasance kome ba wanda ake ambata

Verse 2 — Surah Al-Insan 76:2

Lalle ne, Mu Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, saboda haka Muka sanya shi mai ji mai gani

Verse 3 — Surah Al-Insan 76:3

Lalle ne, Mu, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai godiya, kuma ko ya zama mai kafirci

Verse 4 — Surah Al-Insan 76:4

Lalle ne, Mu, Mun yi tattali, domin kafirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ir

Verse 5 — Surah Al-Insan 76:5

Lalle ne, mutanen kirki za su sha daga finjalin giya abin gaurayarta ya kasance kafur ne

Verse 6 — Surah Al-Insan 76:6

Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa

Verse 7 — Surah Al-Insan 76:7

Suna cikawa da alwashin (da suka bakanta), kuma suna tsoron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne

Verse 8 — Surah Al-Insan 76:8

Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukatarsa, ga matalauci da maraya da kamamme

Verse 9 — Surah Al-Insan 76:9

(Suna cewa): "Muna ciyar da ku ne domin neman yardar Allah kawai, ba mu nufin samun wani sakamako daga gare ku, kuma ba mu nufin godiya

Verse 10 — Surah Al-Insan 76:10

Lalle ne, mu muna tsoro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsewa, mai murtukewa

Verse 11 — Surah Al-Insan 76:11

Saboda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annurin huska da farin ciki

Verse 12 — Surah Al-Insan 76:12

Kuma Ya saka musu saboda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufafin alharini

Verse 13 — Surah Al-Insan 76:13

Suna masu zaman ginciri,* a cikinta, a kan karagu, ba su ganin rana a cikinta, kuma ba su ganin jaura

Verse 14 — Surah Al-Insan 76:14

Kuma, inuwoyinta suna kusa, a kansu, an hore nunannun 'ya'yan itacenta, horewa

Verse 15 — Surah Al-Insan 76:15

Kuma ana kewayawa a kansu da finjalai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau

Verse 16 — Surah Al-Insan 76:16

¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukata

Verse 17 — Surah Al-Insan 76:17

Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne

Verse 18 — Surah Al-Insan 76:18

Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil

Verse 19 — Surah Al-Insan 76:19

Kuma wasu yara samarin dindindin na kewayawa, a kansu, idan ka gan su, za ka zaci su lu'ulu'u ne wanda aka watsa

Verse 20 — Surah Al-Insan 76:20

Kuma idan ka ga wannan wurin, to, ka ga wata irin ni'ima da mulki babba

Verse 21 — Surah Al-Insan 76:21

Tufafinsu na sama na alhari ni ne, kore da mai walƙiya, kuma an ƙawace su da mundaye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shayar da su abin sha mai tsarkakewar (ciki)

Verse 22 — Surah Al-Insan 76:22

(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin godewa

Verse 23 — Surah Al-Insan 76:23

Lalle, Mu ne Muka saukar da Alƙur'ani a gare ka, saukarwa

Verse 24 — Surah Al-Insan 76:24

Saboda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kafirci

Verse 25 — Surah Al-Insan 76:25

Kuma ka ambaci sunan Ubangijinka, safe da maraice

Verse 26 — Surah Al-Insan 76:26

Daga dare, sai ka yi sujuda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi dare mai tsawo

Verse 27 — Surah Al-Insan 76:27

Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugawa (duniya) kuma suna bari, a bayansu, wani yini mai nauyi

Verse 28 — Surah Al-Insan 76:28

Mu ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanya su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa

Verse 29 — Surah Al-Insan 76:29

Lalle ne, wannan wata tunatarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa

Verse 30 — Surah Al-Insan 76:30

Kuma, ba za ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Ya kasance Masani' Mai hikima

Verse 31 — Surah Al-Insan 76:31

Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzalumai, Ya yi musu tattalin wata azaba mai raɗaɗi