Back to Languages

Hausa - Chapter 77 - Al-Mursalat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Mursalat 77:1

Ina rantsuwa da iskokin da ake sakowa jere, suna bin juna

Verse 2 — Surah Al-Mursalat 77:2

Sa'an nan, su zama iskoki masu ƙarfi suna kaɗawa da ƙarfi

Verse 3 — Surah Al-Mursalat 77:3

Kuma, masu watsa rahama watsawa

Verse 4 — Surah Al-Mursalat 77:4

sa'an nan, da ayoyi* masu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabewa

Verse 5 — Surah Al-Mursalat 77:5

Sa'an nan da mala'iku masu jefa tunatarwa ga Manzanni

Verse 6 — Surah Al-Mursalat 77:6

Domin yanke hamzari ko domin gargadi

Verse 7 — Surah Al-Mursalat 77:7

Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

Verse 8 — Surah Al-Mursalat 77:8

To, idan taurari aka shafe haskensu

Verse 9 — Surah Al-Mursalat 77:9

Kuma, idan sama aka tsage ta

Verse 10 — Surah Al-Mursalat 77:10

Kuma, idan duwatsu aka nike su

Verse 11 — Surah Al-Mursalat 77:11

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lokacin tara su

Verse 12 — Surah Al-Mursalat 77:12

Domin babbar ranar da aka yi wa ajali

Verse 13 — Surah Al-Mursalat 77:13

Domin ranar rarrabewa

Verse 14 — Surah Al-Mursalat 77:14

Kuma, me ya sanar da kai ranar rarrabewa

Verse 15 — Surah Al-Mursalat 77:15

Bone ya tabbata a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 16 — Surah Al-Mursalat 77:16

Ashe, ba Mu halakar da (masu ƙaryataw) na farko ba

Verse 17 — Surah Al-Mursalat 77:17

Sa'an nan, kuma za Mu biyar musu da na ƙarshe

Verse 18 — Surah Al-Mursalat 77:18

Haka nan, Muke aikatawa da masu yin laifi

Verse 19 — Surah Al-Mursalat 77:19

Bone ya tabbata a ranar nan ga masu ƙaryatawa

Verse 20 — Surah Al-Mursalat 77:20

Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba

Verse 21 — Surah Al-Mursalat 77:21

Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce

Verse 22 — Surah Al-Mursalat 77:22

Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna

Verse 23 — Surah Al-Mursalat 77:23

Sa'an nan, Muka nuna iyawar Mu? Madalla da Mu, Masu nuna iyawa

Verse 24 — Surah Al-Mursalat 77:24

Bone ya tabbata a ranar nan ga masu ƙaryatawa

Verse 25 — Surah Al-Mursalat 77:25

Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattara ba

Verse 26 — Surah Al-Mursalat 77:26

Ga rayayyu da matattu

Verse 27 — Surah Al-Mursalat 77:27

Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwatsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai daɗi

Verse 28 — Surah Al-Mursalat 77:28

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 29 — Surah Al-Mursalat 77:29

Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatawa game da shi

Verse 30 — Surah Al-Mursalat 77:30

Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku

Verse 31 — Surah Al-Mursalat 77:31

Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadatarwa daga harshen wuta

Verse 32 — Surah Al-Mursalat 77:32

Lalle ne, ita, tana jifa da tartsatsi kamar soraye

Verse 33 — Surah Al-Mursalat 77:33

Kamar dai su raƙumma ne baƙaƙe

Verse 34 — Surah Al-Mursalat 77:34

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 35 — Surah Al-Mursalat 77:35

Wannan, yini ne da ba za su iya yin magana ba

Verse 36 — Surah Al-Mursalat 77:36

Ba za a yi musu izni ba, balle su kawo hanzari

Verse 37 — Surah Al-Mursalat 77:37

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 38 — Surah Al-Mursalat 77:38

Wannan ranar rarrabewa ce, Mun tattara ku tare da mutanen farko

Verse 39 — Surah Al-Mursalat 77:39

To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita

Verse 40 — Surah Al-Mursalat 77:40

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 41 — Surah Al-Mursalat 77:41

Lalle ne, masu taƙawa suna a cikin inuwowi da maremari

Verse 42 — Surah Al-Mursalat 77:42

Da wasu 'ya'yan itace irin waɗanda suke marmari

Verse 43 — Surah Al-Mursalat 77:43

(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 44 — Surah Al-Mursalat 77:44

Lalle ne, Mu haka Muke saka wa masu kyautatawa

Verse 45 — Surah Al-Mursalat 77:45

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 46 — Surah Al-Mursalat 77:46

(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dadi kaɗan, lalle ne dai ku masu laifi ne

Verse 47 — Surah Al-Mursalat 77:47

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 48 — Surah Al-Mursalat 77:48

Kuma, idan an ce musu: "Ku yi ruku'i; ba za su yi ruku'in (salla) ba

Verse 49 — Surah Al-Mursalat 77:49

Bone ya tabbata, a ranar nan, ga masu ƙaryatawa

Verse 50 — Surah Al-Mursalat 77:50

To, da wane labari (Littafi), waninsa (Alƙur'ani) za su yi imani