Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 78 - An-Naba
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah An-Naba 78:1
A kan me suke tambayar juna
Verse 2 — Surah An-Naba 78:2
A kan muhimmin labari mai girma (Alƙur'ani)
Verse 3 — Surah An-Naba 78:3
Wanda suke saɓa wa juna a cikinsa
Verse 4 — Surah An-Naba 78:4
A'aha! Za su sani
Verse 5 — Surah An-Naba 78:5
Kuma, a'aha! Za su sani
Verse 6 — Surah An-Naba 78:6
Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba
Verse 7 — Surah An-Naba 78:7
Da duwatsu turaku (ga riƙe ƙasa)
Verse 8 — Surah An-Naba 78:8
Kuma, Mun halitta ku maza da mata
Verse 9 — Surah An-Naba 78:9
Kuma, Muka sanya barcinku hutawa
Verse 10 — Surah An-Naba 78:10
Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura
Verse 11 — Surah An-Naba 78:11
Kuma, Muka sanya yini (yazama) lokacin neman abinci
Verse 12 — Surah An-Naba 78:12
Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai masu ƙarfi
Verse 13 — Surah An-Naba 78:13
Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rana)
Verse 14 — Surah An-Naba 78:14
Kuma, Muka saukar daga cikakkun giragizai, ruwa mai yawan zuba
Verse 15 — Surah An-Naba 78:15
Domin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi
Verse 16 — Surah An-Naba 78:16
Da itacen lambuna masu lillibniya
Verse 17 — Surah An-Naba 78:17
Lalle ne, ranar rarrabewa ta kasance abin ƙayyade wa lokaci
Verse 18 — Surah An-Naba 78:18
Ranar da za a yi busa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a
Verse 19 — Surah An-Naba 78:19
Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙofofi
Verse 20 — Surah An-Naba 78:20
Kuma, aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance ƙura
Verse 21 — Surah An-Naba 78:21
Lalle ne, Jahannama ta kasance madakata
Verse 22 — Surah An-Naba 78:22
Ga masu ƙetare iyakoki, ta zama makoma
Verse 23 — Surah An-Naba 78:23
Suna, masu zama a cikinta, zamunna
Verse 24 — Surah An-Naba 78:24
Ba su ɗanɗanawar wani sanyi a cikinta, kuma ba su ɗanɗana abin sha
Verse 25 — Surah An-Naba 78:25
Face tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini
Verse 26 — Surah An-Naba 78:26
Sakamako mai dacewa
Verse 27 — Surah An-Naba 78:27
Lalle ne, su, sun kasance ba su fatar sauƙin wani hisabi
Verse 28 — Surah An-Naba 78:28
Kuma, suka ƙaryata game da ayoyin Mu, ƙaryatawa
Verse 29 — Surah An-Naba 78:29
Alhali, kowane abu Mun ƙididdige shi, a rubuce
Verse 30 — Surah An-Naba 78:30
Saboda haka, ku ɗanɗana domin haka, ba za Mu ƙara muku kome ba face azaba
Verse 31 — Surah An-Naba 78:31
Lalle ne, masu taƙawa na da wani wurin samun babban rabo
Verse 32 — Surah An-Naba 78:32
Lambuna da inabobi
Verse 33 — Surah An-Naba 78:33
Da yan Mata tsaraikun Juna
Verse 34 — Surah An-Naba 78:34
Da hinjalan giya cikakku
Verse 35 — Surah An-Naba 78:35
Ba su jin yasassar magana, a cikinta, kuma ba su jin ƙaryatawa
Verse 36 — Surah An-Naba 78:36
Domin sakamako daga Ubangijinka, kyauta mai yawa
Verse 37 — Surah An-Naba 78:37
Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakaninsu, Mai rahama, ba su da ikon yin wata magana daga gare Shi
Verse 38 — Surah An-Naba 78:38
Ranar da Ruhi da mala'iku za su tsaya a cikin safu, ba su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai
Verse 39 — Surah An-Naba 78:39
Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makoma zuwa ga Ubangijinsa
Verse 40 — Surah An-Naba 78:40
Lalle ne, Mu, Mun yi muku gargaɗin azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, da dai na zama turɓaya