Back to Languages

Hausa - Chapter 79 - An-Naziat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah An-Naziat 79:1

Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayuka (na kafirai) da ƙarfi

Verse 2 — Surah An-Naziat 79:2

Da masu ɗibar rayuka (na muminai) da sauƙi a cikin nishaɗi

Verse 3 — Surah An-Naziat 79:3

Da masu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo

Verse 4 — Surah An-Naziat 79:4

Sa'an nan, su zama masu gaugawa (da umarnin Allah) kamar suna tsere

Verse 5 — Surah An-Naziat 79:5

Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni

Verse 6 — Surah An-Naziat 79:6

Ranar da mai girgiza abubuwa (busar farko) za ta kaɗa

Verse 7 — Surah An-Naziat 79:7

Mai biyar ta (busa ta biyu) na biye

Verse 8 — Surah An-Naziat 79:8

Wasu zukata, a ranar nan, masu jin tsoro ne

Verse 9 — Surah An-Naziat 79:9

Alhali idanunsu na ƙasƙantattu

Verse 10 — Surah An-Naziat 79:10

Suna cewa "Ashe lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu

Verse 11 — Surah An-Naziat 79:11

Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu

Verse 12 — Surah An-Naziat 79:12

Suka ce: "Waccan kam komawa ce, taɓaɓɓiya

Verse 13 — Surah An-Naziat 79:13

To, ita kam, tsawa guda kawai ce

Verse 14 — Surah An-Naziat 79:14

Sai kawai ga su a bayan ƙasa

Verse 15 — Surah An-Naziat 79:15

Shin, labarin Musa ya zo maka

Verse 16 — Surah An-Naziat 79:16

A lokacin da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwa

Verse 17 — Surah An-Naziat 79:17

Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙetare haddi

Verse 18 — Surah An-Naziat 79:18

Sai ka ce masa, Ko za ka so ka tsarkaka

Verse 19 — Surah An-Naziat 79:19

Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa

Verse 20 — Surah An-Naziat 79:20

Sai ya nuna masa ayar* nan mafi girma

Verse 21 — Surah An-Naziat 79:21

Sai ya ƙaryata, kuma ya saɓa (umurni)

Verse 22 — Surah An-Naziat 79:22

Sa'an nan ya juya baya, yana tafiya da sauri

Verse 23 — Surah An-Naziat 79:23

Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira

Verse 24 — Surah An-Naziat 79:24

Sai ya ce: "Ni ne Ubangijinku mafi ɗaudaka

Verse 25 — Surah An-Naziat 79:25

Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar ƙarshe da ta farko

Verse 26 — Surah An-Naziat 79:26

Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah

Verse 27 — Surah An-Naziat 79:27

Shin, ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta

Verse 28 — Surah An-Naziat 79:28

Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta

Verse 29 — Surah An-Naziat 79:29

Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta

Verse 30 — Surah An-Naziat 79:30

Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta

Verse 31 — Surah An-Naziat 79:31

Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyayarta

Verse 32 — Surah An-Naziat 79:32

Da duwatsu, Ya kafe ta

Verse 33 — Surah An-Naziat 79:33

Domin jiyarwa daɗi a gare ku, kuma ga dabbobinku

Verse 34 — Surah An-Naziat 79:34

To, idan uwar masifu, mafi girma, ta zo

Verse 35 — Surah An-Naziat 79:35

Ranar da mutum zai yi tunanin abin da ya aikata

Verse 36 — Surah An-Naziat 79:36

Kuma, a bayyana Jahim ga mai gani

Verse 37 — Surah An-Naziat 79:37

To, amma wanda ya yi girman kai

Verse 38 — Surah An-Naziat 79:38

Kuma, ya zaɓi rayuwa ta kusa, (wato duniya)

Verse 39 — Surah An-Naziat 79:39

To, lalle ne Jahim, ita ce makoma

Verse 40 — Surah An-Naziat 79:40

Kuma, amma wanda ya ji tsoron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai

Verse 41 — Surah An-Naziat 79:41

To, lalle ne Aljanna ita ce makoma

Verse 42 — Surah An-Naziat 79:42

Suna tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta

Verse 43 — Surah An-Naziat 79:43

Me ya haɗa ka da ambatonta

Verse 44 — Surah An-Naziat 79:44

Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake

Verse 45 — Surah An-Naziat 79:45

Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsoron ta

Verse 46 — Surah An-Naziat 79:46

Kamar su a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin marece ko hantsinsa