Back to Languages

Hausa - Chapter 81 - At-Takwir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah At-Takwir 81:1

Idan rana aka shafe haskenta

Verse 2 — Surah At-Takwir 81:2

Kuma idan taurari suka gurɓace (wani ya shiga a cikin wani)

Verse 3 — Surah At-Takwir 81:3

Kuma idan duwatsu aka tafiyar da su

Verse 4 — Surah At-Takwir 81:4

Kuma idan raƙuma masu cikunna* aka sake su wawai, ba ga kowa ba

Verse 5 — Surah At-Takwir 81:5

Kuma idan dabbobin daji aka tattara su

Verse 6 — Surah At-Takwir 81:6

Kuma idan tekuna aka mayar da su wuta

Verse 7 — Surah At-Takwir 81:7

Kuma idan rayuka aka haɗa* su da jikunkunansu

Verse 8 — Surah At-Takwir 81:8

Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta

Verse 9 — Surah At-Takwir 81:9

Saboda wane laifi ne aka kashe ta

Verse 10 — Surah At-Takwir 81:10

Idan takardun ayyuka aka watsa su (ga masu su)

Verse 11 — Surah At-Takwir 81:11

Kuma idan sama aka feɗe ta

Verse 12 — Surah At-Takwir 81:12

Kuma idan Jahim aka hura ta

Verse 13 — Surah At-Takwir 81:13

Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita

Verse 14 — Surah At-Takwir 81:14

Rai ya san abin da ya halartar (a ranar nan)

Verse 15 — Surah At-Takwir 81:15

To, ba sai Na yi rantsuwa da taurari matafa* ba

Verse 16 — Surah At-Takwir 81:16

Masu gudu suna ɓuya

Verse 17 — Surah At-Takwir 81:17

Da dare idan ya bayar da baya

Verse 18 — Surah At-Takwir 81:18

Da safiya idan ta yi lumfashi

Verse 19 — Surah At-Takwir 81:19

Lalle ne shi (Alƙur'ani) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah

Verse 20 — Surah At-Takwir 81:20

Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi

Verse 21 — Surah At-Takwir 81:21

Wanda ake yi wa ɗa'a (wato shugaban mala'iku) ne a can, amintacce

Verse 22 — Surah At-Takwir 81:22

Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne

Verse 23 — Surah At-Takwir 81:23

Kuma lalle ne, ya gan shi* a cikin sararin sama mabayyani

Verse 24 — Surah At-Takwir 81:24

Kuma shi, ga gaibi* ba mai rowa ba ne

Verse 25 — Surah At-Takwir 81:25

Kuma shi (Alƙur'ani) ba maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce

Verse 26 — Surah At-Takwir 81:26

Shin, a ina za ku tafi

Verse 27 — Surah At-Takwir 81:27

Lalle ne shi (Alƙur'ani), ba kome ba ne face gargaɗi ga talikai

Verse 28 — Surah At-Takwir 81:28

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu

Verse 29 — Surah At-Takwir 81:29

Kuma ba za ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Ya yarda