Back to Languages

Hausa - Chapter 82 - Al-Infitar

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Infitar 82:1

Verse 2 — Surah Al-Infitar 82:2

Kuma idan taurari suka watse

Verse 3 — Surah Al-Infitar 82:3

Kuma idan tekuna aka facce su

Verse 4 — Surah Al-Infitar 82:4

Kuma idan kaburbura aka tone su

Verse 5 — Surah Al-Infitar 82:5

Rai ya san abin da ya gabatar, da abin da ya jinkirtar

Verse 6 — Surah Al-Infitar 82:6

Ya kai mutum! Me ya ruɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci

Verse 7 — Surah Al-Infitar 82:7

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaita ka, Ya kuma tsakaita ka

Verse 8 — Surah Al-Infitar 82:8

A cikin kowace irin sura Ya so Ya gina ka a kanta

Verse 9 — Surah Al-Infitar 82:9

A'aha, ba haka ba, kuna ƙaryatawa game da sakamako

Verse 10 — Surah Al-Infitar 82:10

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara

Verse 11 — Surah Al-Infitar 82:11

Masu daraja, marubuta

Verse 12 — Surah Al-Infitar 82:12

Suna sanin abin da kuke aikatawa

Verse 13 — Surah Al-Infitar 82:13

Lalle ne, masu ɗa'a ga Allah, dahir, suna cikin ni'ima

Verse 14 — Surah Al-Infitar 82:14

Kuma lalle ne, fajirai, dahir, suna cikin Jahim

Verse 15 — Surah Al-Infitar 82:15

Za su shige ta a ranar sakamako

Verse 16 — Surah Al-Infitar 82:16

Ba za su faku daga gare ta ba

Verse 17 — Surah Al-Infitar 82:17

Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako

Verse 18 — Surah Al-Infitar 82:18

Sa'an nan, me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako

Verse 19 — Surah Al-Infitar 82:19

Rana ce da wani rai ba ya iya mallakar kome domin wani rai al'amari, a ranar nan, ga Allah (ɗai) yake