Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 83 - Al-Mutaffifin
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Mutaffifin 83:1
Bone ya tabbata ga masu naƙƙasawa
Verse 2 — Surah Al-Mutaffifin 83:2
Waɗanda suke idan suka auna daga mutane suna cika mudu
Verse 3 — Surah Al-Mutaffifin 83:3
Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikeli, suna ragewa
Verse 4 — Surah Al-Mutaffifin 83:4
Ashe! Waɗancan ba su tabbata cewa lalle su, ana tayar da su ba
Verse 5 — Surah Al-Mutaffifin 83:5
Domin yini mai girma
Verse 6 — Surah Al-Mutaffifin 83:6
Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta
Verse 7 — Surah Al-Mutaffifin 83:7
Haƙiƙa lalle ne littafin fajirai dahir, yana a cikin Sijjin
Verse 8 — Surah Al-Mutaffifin 83:8
Kuma, me ya sanar da kai abin da ake ce wa Sijjin
Verse 9 — Surah Al-Mutaffifin 83:9
Wani ittafi ne rubutacce
Verse 10 — Surah Al-Mutaffifin 83:10
Bone ya tabbata a ranar nan ga masu ƙaryatawa
Verse 11 — Surah Al-Mutaffifin 83:11
Waɗanda suke ƙaryatawa game da ranar sakamako
Verse 12 — Surah Al-Mutaffifin 83:12
Babu mai ƙaryatawa gare shi face dukan mai ƙetare haddi mai yawan zunubi
Verse 13 — Surah Al-Mutaffifin 83:13
Idan ana karatun ayoyinmu, a kansa, sai ya ce: tatsuniyoyin mutanen farko ne
Verse 14 — Surah Al-Mutaffifin 83:14
A'aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu
Verse 15 — Surah Al-Mutaffifin 83:15
A'aha! Haƙiƙa, lalle ne su daga Ubangijinsu, ranar nan, waɗanda ake shamakancewa ne
Verse 16 — Surah Al-Mutaffifin 83:16
Sa'an nan, lalle ne, su masu shiga cikin Jahim ne
Verse 17 — Surah Al-Mutaffifin 83:17
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatawa game da shi
Verse 18 — Surah Al-Mutaffifin 83:18
A'aha! Haƙiƙa lalle ne littafin masu ɗa'a yana a cikin Illiyyina
Verse 19 — Surah Al-Mutaffifin 83:19
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cewa Illiyyuna
Verse 20 — Surah Al-Mutaffifin 83:20
Wani littafi ne rubutacce
Verse 21 — Surah Al-Mutaffifin 83:21
Muƙarrabai* suke halarta shi
Verse 22 — Surah Al-Mutaffifin 83:22
Lalle ne, masu ɗa'a ga Allah tabbas suna cikin ni'ima
Verse 23 — Surah Al-Mutaffifin 83:23
A kan karagu, suna ta kallo
Verse 24 — Surah Al-Mutaffifin 83:24
Kana sani a cikin fuskokinsu, akwai kwarjinin ni'ima
Verse 25 — Surah Al-Mutaffifin 83:25
Ana shayar da su daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta
Verse 26 — Surah Al-Mutaffifin 83:26
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, masu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nema
Verse 27 — Surah Al-Mutaffifin 83:27
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnim yake
Verse 28 — Surah Al-Mutaffifin 83:28
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi
Verse 29 — Surah Al-Mutaffifin 83:29
Lalle ne, waɗanda suka kafirta sun kasance (a duniya) suna yi wa waɗanda suka yi imani dariya
Verse 30 — Surah Al-Mutaffifin 83:30
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe
Verse 31 — Surah Al-Mutaffifin 83:31
Kuma idan suka juya zuwa ga iyalansu, sai su tafi suna kakaci
Verse 32 — Surah Al-Mutaffifin 83:32
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne
Verse 33 — Surah Al-Mutaffifin 83:33
Alhali kuwa, ba a aike su ba domin su zama masu tsaro a kansu
Verse 34 — Surah Al-Mutaffifin 83:34
To, yau fa (a Lahira] waɗanda suka yi imani, su ke yi wa kafirai dariya
Verse 35 — Surah Al-Mutaffifin 83:35
A kan karagu, suna ta kallo
Verse 36 — Surah Al-Mutaffifin 83:36
Shin an saka ma kafirai abin da suka kasance suna aikatawa