Back to Languages

Hausa - Chapter 84 - Al-Inshiqaq

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Inshiqaq 84:1

Verse 2 — Surah Al-Inshiqaq 84:2

Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin sauraron

Verse 3 — Surah Al-Inshiqaq 84:3

Kuma idan ƙasa aka miƙe ta

Verse 4 — Surah Al-Inshiqaq 84:4

Kuma ta jefar da abin da yake a cikinta, ta wofinta daga kome

Verse 5 — Surah Al-Inshiqaq 84:5

Kuma ta saurari Ubangijinta, aka wajabta mata yin sauraren

Verse 6 — Surah Al-Inshiqaq 84:6

Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne

Verse 7 — Surah Al-Inshiqaq 84:7

To, amma wanda aka bai wa littafinsa da damansa

Verse 8 — Surah Al-Inshiqaq 84:8

To, za a yi masa hisabi, hisabi mai sauƙi

Verse 9 — Surah Al-Inshiqaq 84:9

Kuma ya juya zuwa ga iyalinsa (a cikin Aljanna), yana mai raha

Verse 10 — Surah Al-Inshiqaq 84:10

Kuma amma wanda aka bai wa littafinsa, daga wajen bayansa

Verse 11 — Surah Al-Inshiqaq 84:11

To, za shi dinga kiran halaka

Verse 12 — Surah Al-Inshiqaq 84:12

Verse 13 — Surah Al-Inshiqaq 84:13

Lale ne shi, ya kasance (a duniya) cikin iyalinsa yana mai raha

Verse 14 — Surah Al-Inshiqaq 84:14

Lalle ne ya yi zaton ba zai komo ba

Verse 15 — Surah Al-Inshiqaq 84:15

Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi

Verse 16 — Surah Al-Inshiqaq 84:16

To, ba sai Na rantse da shafaƙi ba

Verse 17 — Surah Al-Inshiqaq 84:17

Da dare, da abin da ya ƙunsa

Verse 18 — Surah Al-Inshiqaq 84:18

Da wata idan (haskensa) ya cika

Verse 19 — Surah Al-Inshiqaq 84:19

Lalle ne kuna hawan wani hali daga wani hali

Verse 20 — Surah Al-Inshiqaq 84:20

To, me ya same su, ba su yin imani

Verse 21 — Surah Al-Inshiqaq 84:21

Kuma idan an karanta Alkur'ani a kansu, ba su yin tawali'u

Verse 22 — Surah Al-Inshiqaq 84:22

Ba haka ba! waɗanda suka kafirta, sai ƙaryatawa suke yi

Verse 23 — Surah Al-Inshiqaq 84:23

Alhali Allah Shi ne Mafi sani ga abin a suke tarawa

Verse 24 — Surah Al-Inshiqaq 84:24

Saboda haka, ka yi musu bushara da azaba mai raɗaɗi

Verse 25 — Surah Al-Inshiqaq 84:25

Face waɗanda suka yi imani, suka aikata ayyukan ƙwarai, suna da wani sakamako wanda ba ya yankewa