Back to Languages

Hausa - Chapter 85 - Al-Buruj

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Buruj 85:1

Ina rantsuwa da sama mai taurarin lissafin shekara

Verse 2 — Surah Al-Buruj 85:2

Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa

Verse 3 — Surah Al-Buruj 85:3

Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa

Verse 4 — Surah Al-Buruj 85:4

An la'ani mutanen rami

Verse 5 — Surah Al-Buruj 85:5

Wato wuta wadda aka hura

Verse 6 — Surah Al-Buruj 85:6

A lokacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune

Verse 7 — Surah Al-Buruj 85:7

Alhali su, bisa ga abin da suke aikatawa ga muminai, suna halarce

Verse 8 — Surah Al-Buruj 85:8

Kuma ba su tuhumce su ba, face kawai domin sun yi imani da Allah Mabuwayi, wanda ake godewa

Verse 9 — Surah Al-Buruj 85:9

Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kome halarce Yake

Verse 10 — Surah Al-Buruj 85:10

Lalle ne waɗanda suka fitini muminai maza da muminai mata, sa'an nan ba su tuba ba to, suna da azabar Jahannama, kuma suna da azabar gobara

Verse 11 — Surah Al-Buruj 85:11

Lalle ne waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, suna da gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashin gidajen. Wancan abu fa shi ne rabo babba

Verse 12 — Surah Al-Buruj 85:12

Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai

Verse 13 — Surah Al-Buruj 85:13

Lalle ne Shi, Shi ne Mai ƙaga halitta, kuma Ya mayar da ita (bayan mutuwa)

Verse 14 — Surah Al-Buruj 85:14

Kuma Shi ne Mai gafara, Mai bayyana soyayya

Verse 15 — Surah Al-Buruj 85:15

Mai Al'arshi mai girma

Verse 16 — Surah Al-Buruj 85:16

Mai aikatawa ga abin da Yake nufi

Verse 17 — Surah Al-Buruj 85:17

Ko labarin rundanoni ya zo maka

Verse 18 — Surah Al-Buruj 85:18

Fir'auna da samudawa

Verse 19 — Surah Al-Buruj 85:19

A'aha! waɗanda suka kafirta suna cikin ƙaryatawa

Verse 20 — Surah Al-Buruj 85:20

Alhali, Allah daga bayansu, Mai kewaye su ne (da sanin Sa)

Verse 21 — Surah Al-Buruj 85:21

A'aha! Shi Alƙur'ani ne mai girma

Verse 22 — Surah Al-Buruj 85:22

A cikin Allo tsararre