Back to Languages

    Hausa - Chapter 88

    Translation by Abubakar Mahmood Jummi

    Verse 1

    Lalle ne labarin (¡iyama) mai rufe mutane da tsoronta ya zo maka

    Verse 2

    Wasu huskoki a ranar nan ƙasƙantattu ne

    Verse 3

    Masu aikin wahala ne, masu gajiya

    Verse 4

    Za su shiga wata wuta mai zafi

    Verse 5

    Ana shayar da su daga wani marmaro mai zafin ruwa

    Verse 6

    Ba su da wani abinci face dai daga danyi

    Verse 7

    Ba ya sanya ƙiba, kuma ba zai wadatar daga yunwa ba

    Verse 8

    Wasu huskoki a ranar nan masu ni'ima ne

    Verse 9

    Game da aikinsu, masu yarda ne

    Verse 10

    (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya

    Verse 11

    Ba za su ji yasassar magana ba, a cikinta

    Verse 12

    A cikinta akwai marmaro mai gudana

    Verse 13

    A cikinta akwai gadaje maɗaukaka

    Verse 14

    Da kofuna ar'aje

    Verse 15

    Da filoli* jere

    Verse 16

    Da katifu shimfiɗe

    Verse 17

    Ashe to ba za su dubawa ba ga raƙuma yadda aka halitta su

    Verse 18

    Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta

    Verse 19

    Da zuwa ga duwatsu yadda aka kafa su

    Verse 20

    Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗa ta

    Verse 21

    saboda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai

    Verse 22

    Ba ka zama mai ikon tanƙwasawa a kansu ba

    Verse 23

    Face dai duk wanda ya juya baya, kuma ya kafirta

    Verse 24

    To, Allah zai yi masa azaba, azabar nan da take mafi girma

    Verse 25

    Lalle ne, zuwa gare Mu komowarsu take

    Verse 26

    Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisabi

    Unexpected Application Error!

    Unexpected token '<', "<!DOCTYPE "... is not valid JSON

    SyntaxError: Unexpected token '<', "<!DOCTYPE "... is not valid JSON