Back to Languages

Hausa - Chapter 89 - Al-Fajr

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Fajr 89:1

Ina rantsuwa da alfijiri

Verse 2 — Surah Al-Fajr 89:2

Verse 3 — Surah Al-Fajr 89:3

Da (adadi na) cika da (na) mara

Verse 4 — Surah Al-Fajr 89:4

Da dare idan yana shuɗewa

Verse 5 — Surah Al-Fajr 89:5

Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)

Verse 6 — Surah Al-Fajr 89:6

Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Adawa ba

Verse 7 — Surah Al-Fajr 89:7

Iramawa masu sakon* ƙirar jiki

Verse 8 — Surah Al-Fajr 89:8

Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garuruwa (na duniya)

Verse 9 — Surah Al-Fajr 89:9

Da samudawa waɗanda suka fasa duwatsu a cikin Wadi* suka yi gidaje

Verse 10 — Surah Al-Fajr 89:10

Da Fir'auna mai turaku

Verse 11 — Surah Al-Fajr 89:11

Waɗanda suka ƙetare iyakarsu, a cikin garuruwa

Verse 12 — Surah Al-Fajr 89:12

Saboda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu

Verse 13 — Surah Al-Fajr 89:13

Saboda haka Ubangijinka Ya zuba musu bulalar azaba

Verse 14 — Surah Al-Fajr 89:14

Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka

Verse 15 — Surah Al-Fajr 89:15

To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wato Ya girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni

Verse 16 — Surah Al-Fajr 89:16

Kuma idan Ya jarraba shi, wato Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walakanta ni

Verse 17 — Surah Al-Fajr 89:17

A'aha! Bari wannan, ai ba ku girmama maraya

Verse 18 — Surah Al-Fajr 89:18

Ba ku kwaɗaita wa junanku ga (tattalin) abincin matalauci

Verse 19 — Surah Al-Fajr 89:19

Kuma kuna cin dukiyar gado, ci na tarawa

Verse 20 — Surah Al-Fajr 89:20

Kuma kuna son dukiya, so mai yawa

Verse 21 — Surah Al-Fajr 89:21

A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai

Verse 22 — Surah Al-Fajr 89:22

Kuma Ubangijinka Ya zo, alhali mala'iku na jere, sahu- sahu

Verse 23 — Surah Al-Fajr 89:23

Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunani. To, ina fa tunani yake a gare shi

Verse 24 — Surah Al-Fajr 89:24

Yana dinga cewa, "Kaitona, da na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rayuwata

Verse 25 — Surah Al-Fajr 89:25

To, a ranar nan babu wani mai yin azaba irin azabar Allah

Verse 26 — Surah Al-Fajr 89:26

Kuma babu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa

Verse 27 — Surah Al-Fajr 89:27

Ya kai rai mai natsuwa

Verse 28 — Surah Al-Fajr 89:28

Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhali kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a duniya) abar yardarwa (da sakamakon da za a ba ka a Lahira)

Verse 29 — Surah Al-Fajr 89:29

Sabobda haka, ka shiga cikin bayi Na (masu bin umurui a duniya)

Verse 30 — Surah Al-Fajr 89:30

Kuma ka shiga AljannaTa (a Lahira)