Back to Languages

Hausa - Chapter 90 - Al-Balad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Balad 90:1

Ba sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba

Verse 2 — Surah Al-Balad 90:2

Alhali kai kana mai sauka a cikin wannan gari

Verse 3 — Surah Al-Balad 90:3

Da mahaifi da abin da ya haifa

Verse 4 — Surah Al-Balad 90:4

Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala

Verse 5 — Surah Al-Balad 90:5

Ko yana zaton babu wani mai iya samun iko, a kansa

Verse 6 — Surah Al-Balad 90:6

Yana cewa "Na* halakarda dukiya mai yawa

Verse 7 — Surah Al-Balad 90:7

Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba

Verse 8 — Surah Al-Balad 90:8

Shin, ba Mu sanya masa idanu biyu ba

Verse 9 — Surah Al-Balad 90:9

Da harshe, da leɓɓa biyu

Verse 10 — Surah Al-Balad 90:10

Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyoyi* biyu ba

Verse 11 — Surah Al-Balad 90:11

To, don mene ne bai shiga Aƙaba ba

Verse 12 — Surah Al-Balad 90:12

Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake ce wa Aƙaba

Verse 13 — Surah Al-Balad 90:13

Ita ce fansar wuyan bawa

Verse 14 — Surah Al-Balad 90:14

Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abucin yunwa

Verse 15 — Surah Al-Balad 90:15

Ga maraya ma'abucin zumunta

Verse 16 — Surah Al-Balad 90:16

Ko kuwa wani matalauci ma'abucin turɓaya

Verse 17 — Surah Al-Balad 90:17

Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi imani, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi

Verse 18 — Surah Al-Balad 90:18

Waɗannan ne ma'abuta albarka

Verse 19 — Surah Al-Balad 90:19

Kuma waɗanda suka kafirta da ayoyin Mu, su ne ma'abuta shu'umci

Verse 20 — Surah Al-Balad 90:20

A kansu akwai wata wuta abar kullewa