Back to Languages

Hausa - Chapter 91 - Ash-Shams

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ash-Shams 91:1

Ina rantsuwa da rana da hantsinta

Verse 2 — Surah Ash-Shams 91:2

Kuma da wata idan ya bi ta

Verse 3 — Surah Ash-Shams 91:3

Da yini a lokacin da ya bayyana ta

Verse 4 — Surah Ash-Shams 91:4

Da dare a lokacin da ya ke rufe ta

Verse 5 — Surah Ash-Shams 91:5

Da sama da abin da ya gina ta

Verse 6 — Surah Ash-Shams 91:6

Da ƙasa da abin da ya shimfiɗa ta

Verse 7 — Surah Ash-Shams 91:7

Da rai da abin da ya daidaita shi

Verse 8 — Surah Ash-Shams 91:8

Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fajircinsa da shiryuwarsa

Verse 9 — Surah Ash-Shams 91:9

Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sami babban rabo

Verse 10 — Surah Ash-Shams 91:10

Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya taɓe

Verse 11 — Surah Ash-Shams 91:11

Samudawa sun ƙaryata (Annabinsu), domin girman kansu

Verse 12 — Surah Ash-Shams 91:12

A lokacin da mafi shaƙawarsu ya tafi (wurin soke rakumar salihu)

Verse 13 — Surah Ash-Shams 91:13

Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsoratar da ku ga raƙumar Allah da ruwan shanta

Verse 14 — Surah Ash-Shams 91:14

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka soke ta. Saboda haka Ubangijinsu Ya darkake su, saboda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azabar ga mai laifi da maras laifi)

Verse 15 — Surah Ash-Shams 91:15

Kuma ba ya tsoron aƙibarta (ita halakawar)