Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 92 - Al-Layl
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Layl 92:1
Ina rantsuwa da dare a lokacin da yake rufewa
Verse 2 — Surah Al-Layl 92:2
Da yini a lokacin da yake kuranyewa
Verse 3 — Surah Al-Layl 92:3
Da abin da ya halitta namiji da mace
Verse 4 — Surah Al-Layl 92:4
Lalle ne ayyukanku, dabam-dabam suke
Verse 5 — Surah Al-Layl 92:5
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa
Verse 6 — Surah Al-Layl 92:6
Kuma ya gaskata kalma* mai kyawo
Verse 7 — Surah Al-Layl 92:7
To, za Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi
Verse 8 — Surah Al-Layl 92:8
Kuma amma wanda ya yi rowa, kuma ya wadatu da kansa
Verse 9 — Surah Al-Layl 92:9
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyawo
Verse 10 — Surah Al-Layl 92:10
To, za Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani
Verse 11 — Surah Al-Layl 92:11
Kuma dukiyarsa ba ta wadatar masa da kome ba, a lokacin da ya gangara (a wuta)
Verse 12 — Surah Al-Layl 92:12
Lalle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya
Verse 13 — Surah Al-Layl 92:13
Kuma lalle ne Lahira da duniya Namu ne
Verse 14 — Surah Al-Layl 92:14
Saboda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka
Verse 15 — Surah Al-Layl 92:15
Babu mai shigarta sai mafi Tabewa
Verse 16 — Surah Al-Layl 92:16
Wanda ya ƙaryata, kuma ya juya baya
Verse 17 — Surah Al-Layl 92:17
Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta
Verse 18 — Surah Al-Layl 92:18
Wanda yake bayar da dukiyarsa, alhali yana tsarkaka
Verse 19 — Surah Al-Layl 92:19
Alhali babu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake neman sakamakonta
Verse 20 — Surah Al-Layl 92:20
Face dai neman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka
Verse 21 — Surah Al-Layl 92:21
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da za a ba shi)