Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 93 - Ad-Duhaa
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ad-Duhaa 93:1
Ina rantsuwa da hantsi
Verse 2 — Surah Ad-Duhaa 93:2
Da dare a lokacin da ya rufe (da duhunsa)
Verse 3 — Surah Ad-Duhaa 93:3
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙi kaba
Verse 4 — Surah Ad-Duhaa 93:4
Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko
Verse 5 — Surah Ad-Duhaa 93:5
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta ba ka kyauta sai ka yarda
Verse 6 — Surah Ad-Duhaa 93:6
Ashe, bai same ka maraya ba, sa'an nan Ya yi maka makoma
Verse 7 — Surah Ad-Duhaa 93:7
Kuma Ya same ka ba ka da shari'a, sai Ya shiryar da kai
Verse 8 — Surah Ad-Duhaa 93:8
Kuma Ya same ka matalauci, sai Ya wadata ka
Verse 9 — Surah Ad-Duhaa 93:9
Saboda haka, amma maraya, to, kada ka rinjaye shi
Verse 10 — Surah Ad-Duhaa 93:10
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsawa
Verse 11 — Surah Ad-Duhaa 93:11
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (domin godiya)