Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 94 - Ash-Sharh
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ash-Sharh 94:1
Ba Mu buɗa maka zuciyarka ba (domin ɗaukar haƙuri da fahimta)
Verse 2 — Surah Ash-Sharh 94:2
Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe
Verse 3 — Surah Ash-Sharh 94:3
Wanda ya nauyayi bayanka
Verse 4 — Surah Ash-Sharh 94:4
Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka
Verse 5 — Surah Ash-Sharh 94:5
To, lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauƙi
Verse 6 — Surah Ash-Sharh 94:6
Lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauƙi
Verse 7 — Surah Ash-Sharh 94:7
Saboda haka idan ka ƙare (ibada) sai ka kafu (kana roƙon Allah)
Verse 8 — Surah Ash-Sharh 94:8
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi