Back to Languages
Hausa - Chapter 96
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta
Verse 2
Ya hahitta mutum daga gudan jini
Verse 3
Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci
Verse 4
Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami
Verse 5
Ya sanar da mutum abin da bai sani ba
Verse 6
A'aha! Lalle, ne mutum haƙiƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu)
Verse 7
Domin ya ga kansa, ya wadata
Verse 8
Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take
Verse 9
Shin, ka ga wanda ke hana
Verse 10
Bawa idan ya yi salla
Verse 11
Ashe, ka gani, idan (shi bawan) ya kasance a kan shiriya
Verse 12
Ko ya yi umurni da taƙawa
Verse 13
Ashe, ka gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya juya baya
Verse 14
Ashe, bai sani ba cewa Allah Yana gani
Verse 15
A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne za Mu ja gashin makwarkwaɗa
Verse 16
Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi
Verse 17
Sai ya kirayi ƙungiyarsa
Verse 18
Za Mu kirayi zabaniyawa (mala'iku masu girma)
Verse 19
A'aha kada ka bi shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka)