Back to Languages
Hausa - Chapter 97
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Lalle ne Mu, Mun saukar da shi (Alƙur'ani) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
Verse 2
To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari
Verse 3
Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu
Verse 4
Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu saboda kowane umurni
Verse 5
Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri