Back to Languages

Hausa - Chapter 98 - Al-Bayyinah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Bayyinah 98:1

Waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu

Verse 2 — Surah Al-Bayyinah 98:2

Wani Manzo* daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki

Verse 3 — Surah Al-Bayyinah 98:3

A cikinsu akwai wasu littafai masu ƙima da daraja

Verse 4 — Surah Al-Bayyinah 98:4

Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su saɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu

Verse 5 — Surah Al-Bayyinah 98:5

Kuma ba a umarce su da kome ba face bauta wa Allah suna masu tsarkake addinin gare Shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bayar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai

Verse 6 — Surah Al-Bayyinah 98:6

Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin talikai

Verse 7 — Surah Al-Bayyinah 98:7

Lalle ne waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta

Verse 8 — Surah Al-Bayyinah 98:8

Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa