[2] Wancan ne Littafi, babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu taƙawa
[3] Waɗanda suke yin imani game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa
[4] Kuma waɗanda suke yin imani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabaninka, kuma game da Lahira suna yin yaƙini
[5] Waɗancan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne masu cin nasara
[6] Lalle ne waɗanda suka kafirta* daidai ne a kansu, shin ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu gargaɗi ba, ba za su yi imani ba
[7] Allah Ya sa hatimi a kan zukatansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yana; kuma suna da wata azaba mai girma
[8] Kuma akwai daga cikin mutane wanda* yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lahira." Alhali kuwa su ba muminai ba ne
[9] Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kansu, kuma ba su sakankancewa
[10] A cikin zukatansu akwai wata cuta. Sai Allah Ya ƙaramusu wata cuta, kuma suna da azaba mai raɗaɗi saboda abin da suka kasance suna yi na ƙarya
[11] Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mu masu kyautatawa kawai ne
[12] To, lalle ne su, sune masu ɓarna, kuma amma ba su san hakan ba
[13] Kuma idan aka ce musu: "ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani," sukan ce: "Za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?" To, lalle ne su, su ne wawaye, kuma amma ba su sani
[14] Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi imani, sukan ce: "Mun yi imani. "Kuma idan sun wofinta zuwa ga shaiɗanunsu,* sukan ce: "Lalle ne muna tare da ku: Mu masu izgili, kawai ne
[15] Allah Yana yin izgili* gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa
[16] Waɗan can su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi riba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba
[17] Misalinsu shi ne kamar misalin wanda ya hura wuta, to, a lokacin da ta haskake abin da yake gefensa (na abin tsoro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, ba su gani
[18] Kurame, bebaye, makafi, saboda haka ba su dawowa
[19] Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsawa da walƙiya: suna sanyawar yatsunsu a cikin kunnuwansu daga tsawarwakin, domin tsoron mutuwa. Kuma Allah Mai kewayewane ga kafirai
[20] Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskaka musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma da Allah Ya so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne
[21] Ya ku mutane! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, ku da waɗanda suke daga gabaninku, tsammaninku ku kare kanku
[22] Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itace game da shi, saboda ku. Saboda haka kada ku sanya wa Allah wasu kishiyoyi, alhali kuwa kuna sane
[23] To idan baku iya yi ba to kuwa bazaku taba iya yin ba to kuji tsoron wutar da makamahinta Mutane ne da Duwatsu kuma an tanadeta ne ga Kafirai
[24] To, idan ba ku aikata (kawo sura) ba, to, ba za ku aikataba, saboda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makamashinta mutane da duwatsu ne, an yi tattalinta domin kafurai
[25] Kuma ka bayar da bishara ga waɗanda suka yi imani. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cewa lallene, suna da gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itace daga gare su,* sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabanin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma suna da, a cikin su, matan aure masu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne
[26] Lalle ne, Allah ba Ya jin kunyar Ya bayyana wani misali, kowane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi imani, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kafirta, sai su ce: "Mene ne Allah Ya yi nufi da wannan* ya zama misali?" na ɓatar da wasu masu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu masu yawada shi, kuma ba Ya ɓatarwa da shi face fasiƙai
[27] Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bayan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sadar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan su ne masu hasara
[28] Yaya kuke kaficewa da Allah, alhali kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rayar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya raya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku
[29] Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita* zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan komai Masani ne
[30] Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya ce ga mala'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halifa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, za Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gode maka, kuma* muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba
[31] Kuma Ya sanar da Adam sunaye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan mala'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sunayen waɗannan, idan kun nasance masu gaskiya
[32] Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Babu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima
[33] Ya ce: "Ya Adam! Ka gaya musu sunayensu." To, a lokacin da ya gaya musu sunayensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku *ba, lalle Ni, Ina sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Ina sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓoyewa
[34] Kuma a lokacin da Muka ce ga mala'iku: "Ku yi sujada ga Adam," Sai suka yi sujada, face Ibilisa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kafirai
[35] Kuma muka ce: "Ya Adam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadata, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itaciyar, har ku kasance daga azzalumai
[36] Sai Shaiɗan ya talalaɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sashenku na maƙiyi ga sashe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin daɗi zuwa ga wani lokaci
[37] Sai Adam ya karɓi wasu kalmomi daga Ubangjjinsa, saboda haka ya karɓi tuba a kansa. Lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai
[38] Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, babu tsoro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki
[39] Kuma waɗan da suka kafirta, kuma suka ƙaryata game da ayoyinMu, waɗannan su ne abokan Wuta; su a cikinta madawwama ne
[40] Ya Bani Isra'Ila*! Ku tuna ni'imaTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsoro Na
[41] Kuma, ku yi imani da abin da na saukar, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku, kuma kada ku kasance farkon kafiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ayoyiNa. Kuma ku ji tsoroNa, Ni kaɗai
[42] Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓoye gaskiya, alhali kuwa kuna sane
[43] Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bayar da zakka; kuma ku yi ruku'i tare da masu yin ruku'i
[44] Shin, kuna umurnin mutane da alheri, kuma ku manta da kanku alhali kuwa kuna karatun littafi? Shin, baza ku hankalta ba
[45] Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙiƙa, mai girma ce face fa a kan masu tsoron Allah
[46] Waɗanda suka tabbata cewa lalle ne su masu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne su a gareshi masu komawa ne
[47] ku Bani Isra'Ila! Ku tuna ni'imaTa a kanku, kuma kuma ni na fifita ku akan sauran Talikai
[48] Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai ba ya Wadatar da wani rai da kome, kuma ba a karɓar ceto daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma ba su zama ana taimakon su ba
[49] Kuma a lokacin da muka tsirar da ku daga mutanen Fir'auna, su na taya muku muguntar azaba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rayar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku
[50] Kuma a lokacin da Muka raba teku saboda ku, sai Muka tsirar da ku kuma Muka nutsar da mutanen Fir'auna, alhali kuwa ku kuna kallo
[51] Kuma a lokacin da muka yi wa'adi ga Musa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bayansa, alhali ku, kuna masu zalunci (da bauta masa)
[52] Sa'an nan kuma muka yafe muku daga bayan wancan, tsammaninku, kuna godewa
[53] Kuma a lokacin da Muka baiwa Musa Littafi da rarrabewa, tsammaninku, kuna shiryuwa
[54] Kuma a lokacin da Musa ya ce ga mutanensa: "Ya mutanena! Lalle ne ku, kun zalunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kawunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai
[55] Kuma a lokacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi imani ba dominka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsawar nan ta kamaku, alhali kuwa kuna kallo
[56] Sa'an nan kuma Muka tayar da ku daga bayan mutuwarku, tsammaninku, kuna godewa
[57] Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga masu daɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zalunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zalunta
[58] Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku, kuma za mu ƙara wa masu kyautatawa
[59] Sai waɗan da suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zalunci da azaba daga sama saboda abin da suka kasance suna yi na fasiƙanci
[60] Kuma a lokacin da Musa ya nemi shayarwa domin mutanensa, Muka ce; "Ka doki dutsen da sandarka." Sai marmaro goma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙiƙa, kowaɗanne mutane sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna masu ɓarna
[61] Kuma a lokacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka roƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna neman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alheri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka roƙa. "Kuma Muka doka musu walaƙanci da talauci. Kuma suka koma da wani fushi daga Allah. Wancan saboda lalle su, sun kasance suna kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe Aannabawa, bada hakki ba. Wancan, saboda saɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙetarewar haddi
[62] Lalle ne waɗanda suka yi imani, da waɗanda suka tuba*, da Nasara da Makarkata, wana ya yi imani da Allah da Yinin Lahira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijararsu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba
[63] Kuma a lokacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gareku: "Ku kama abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammaninku ku karekanku
[64] Sa'an nan kuma kuka juya daga bayan wancan, to, ba domin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙiƙa, da kun kasance daga masu hasara
[65] Kuma lalle ne, haƙiƙa, kun san waɗanda suka ƙetare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu
[66] Muka sanya ta (mas'alar) azaba, domin abin da yake gaba gareta, da yake a bayanta, kuma wa'azi ga masu taƙawa
[67] Kuma a lokacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata saniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina neman tsari daga Allah da in kasance daga jahilai
[68] Suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mece ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita saniya ce; ba tsofuwa ba, ba kuma budurwa ba, tsakatsaki ce a tsakanin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku
[69] Suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta
[70] Suka ce: "Ka roƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shanu suna yi mana kama da juna, kuma mu, idan Allah Ya so, haƙiƙa, shiryuwa ne
[71] Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cewa: "Ita wata saniya ce; ba horarra ba tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lafiyayya ce: babu wani sofane a cikinta." Suka ce: "Yanzu ka zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba za su aikata ba
[72] Kuma a lokacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa juna laifi a cikinsa,* kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓoyewa ne
[73] Sai Muka ce: "Ku doke shi da wani sashenta." Kamar wancan ne Allah Yake rayar da matattu, kuma Ya nuna muku ayoyinSa, tsammaninku kuna hankalta
[74] San nan kuma zukatanku, suka ƙeƙashe daga bayan wancan. Saboda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwatsu, haƙika, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙiƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙiƙa, daga gare su, haƙiƙa, akwai da yake faɗowa domin tsoron Allah, kuma Allah bai zama gafili ba daga barin abin da kuke aikatawa
[75] Shin kuna tsammanin za su yi imani saboda ku, alhali kuwa, haƙiƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bayan sun gane ta, alhali su, suna sane
[76] Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi imani sukan ce: "Mun yi imani," kuma idan sashensu ya wofinta zuwa ga sashe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne domin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, ba ku hankalta
[77] Shin, kuma ba su sanin cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa
[78] Kuma daga cikin su akwai ummiyyai, ba su da sanin Littafi, face tatsuniyoyi, kuma su ba kome suke yi ba face suna yin zato
[79] To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubuta littafi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, domin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubutawa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sana'antawa
[80] Kuma suka ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba, face, 'yan kwanuka ƙidayayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai saɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah
[81] Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mugun abu, kuma laifinsa ya kewaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, su a cikinta madawwama ne
[82] Kuma waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, su a cikinta madawwama ne
[83] Kuma a lokacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isra'ila*: "Kada ku bauta wa kowa face Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marayu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutane, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka, sa'an nan kuka juya baya, face kaɗan daga gare ku, alhali kuwa kuna masu bijirewa
[84] Lokacin da Muka riƙi alkawarinku; ba za ku zubar da jininku ba, kuma ba za ku fitar da kanku daga gidajenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhali kuwa kuna bayar da shaida (a kanku)
[85] Sa'an nan kuma, ga ku, ya waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidajensu, kuna taimakon juna a kansu da zunubi da zalunci kuma idan kamammu suka je muku kuna fansarsu alhali kuwa shi fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna imani da sashen Littafin ne, kuma ku kafirta da sashe? To, mene ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku face wulakanci* a cikin rayuwar duniya? Kuma a Ranar ¡iyama ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatawa
[86] Waɗan nan su ne waɗan da suka sayi rayuwar duniya da Lahira, domin haka ba za a sauƙaƙa azaba ba daga kansu, kuma su, ba ataimakonsu
[87] Kuma lalle ne, haƙiƙa, Munbai wa Musa Littafi, kuma Mun biyar daga bayansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Isa ɗan Maryama hujjoji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Ruhi mai tsarki*. Shinfa, ko da yaushe wani manzo ya je muku tare da abin da rayukanku ba su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashewa
[88] Kuma suka ce: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah Ya la'ane su, domin kafircinsu kadan kwarai suke yin imani
[89] Kuma a lokacin da wani Littafi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatawa ga abin da yake tare da su, alhali kuwa sun kasance daga gabanin haka suna fatar taimako* da shi a kan waɗanda suka kafirta. To, a lokacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kafirta da shi. Saboda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kafirai
[90] Tir, da abin da suka sayi rayukansu da shi; watau su kafirta da abin da Allah Ya saukar saboda zalunci;* kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bayinsa. Sai suka komo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kafirai akwai azaba mai wulaƙantarwa
[91] Kuma idan aka ce musu: "Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna imani da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kafircewa da abin da ke bayansa, alhali kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tare da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabawan Allah gabanin wannan, idan kun kasance masu bayar da gaskiya
[92] Kuma lalle ne haƙiƙa Musa ya zo muku da hujjoji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi* (daga bayansa, alhali kuwa kuna masu zalunci)
[93] Kuma a lokacin da Muka riƙi* alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kawo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu saboda kafircinsu. Ka ce: "Tir da abin da imaninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance masu imani
[94] Ka ce: "Idan Gidan Lahira ya kasance saboda ku ku ne kadai, a wurin Allah babu sauran mutane, to, ku yi burin mutuwa, idan kun kasance masu gaskiya
[95] Kuma ba za su yi gurinta ba har abada saboda abin da hannayensu, suka gabatar. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai
[96] Kuma lalle ne, za ka same su mafiya kwaɗayin mutane a kan rayuwa, kuma su ne mafiya kwaɗayin rayuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son da za a rayar da shi shekara dubu, kuma ba ya zama mai nisantar da shi daga azaba domin an rayar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatawa
[97] Ka ce: Wanda ya* kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zuciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatawa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishara ga muminai
[98] Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da mala'ikunSa da manzanninSa da Jibirila da Mika'ila to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kafirai
[99] Kuma lalle ne haƙiƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ayoyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kafirta da su face fasikai
[100] Shin, kuma a ko da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jifa da shi? A'a, mafi yawansu ba su yin imani
[101] Kuma a lokacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatawa ga abin da yake tare da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littafi, suka yar da Littafin (Alƙur'anin) Allah a bayan bayansu, kamar dai su ba su sani ba
[102] Kuma suka bi abin da shaiɗanu* ke karantawa a kan mulkin Sulaimanu, kuma Sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma Shaidanun, su ne suka yi kafirci, suna karantar da mutane sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan mala'iku biyu a Babila, Haruta da Maruta. Kuma ba su sanar da kowa ba balle su ce: "Mu fitina kawai ne, saboda haka kada ka kafirta," balle har su yi ta neman ilmin abin da suke rarrabewa tsakanin mutum da matarsa da shi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) ba su zama masu cutar da kowa da shi ba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilmin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, ba ya da wani rabo a cikin Lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi, da sun kasance suna sani
[103] Kuma da lalle ne su, sun yi imani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alheri, da sun kasance suna sani
[104] Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku ce: 'Ra'ina'* kuma ku ce: 'Jinkirta mana', kuma ku saurara. Kuma kafirai suna da azaba mai raɗaɗi
[105] Waɗanda suka kafirta daga Ma'abuta Littafi, ba su son a saukar da wani alheri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai ma ba su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abucin falala mai girma ne
[106] Abin da Muka shafe* daga aya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, za Mu zo da mafi Alheri daga gare ta ko kuwa misalinta. Ashe, ba ka sani ba, cewa lalle ne, Allah a kan dukkan kome Mai ikon yi ne
[107] Shin ba ka sani ba, cewa lalle ne Allah, Shi ne da mulkin sammai da ƙasa kuma ba ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma ba ku da wani mataimaki
[108] Ko kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Musa a gabanin haka? Kuma wanda ya musanya kafirci da imani, to, lalle ne ya ɓace tsakar hanya
[109] Masu yawa daga Ma'abuta Littafi suna gurin da sun mayar da ku, daga bayan imaninku, kafirai, saboda hasada daga wurin rayukansu, daga bayan gaskiya ta bayyana a gare su. To, ku yafe, kuma ku kau da kai, sai Allah Ya zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kome Mai ikon yi ne
[110] Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka. Kuma abin da kuka gabatar domin kanku daga alheri, za ku same shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne
[111] Kuma suka ce: "Babu mai shiga Aljanna face waɗanda suka zama Yahudu ko Nasara." Waɗancan tatsuniyoyinsu ne. Ka ce: "Ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya
[112] Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhali kuwa yana mai kyautatawa, to, yana da ijararsa, a wurin Ubangijinsa, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba
[113] Kuma Yahudawa suka ce: "Nasara ba su zamana a kan kome ba,"* kuma Nasara suka ce: "Yahudawa ba su zamana a kan komeba," alhali kuwa su, suna karatun Littafi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu saboda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakaninsu a Ranar ¡iyama, a cikin abin da suka kasance suna saɓawa juna a cikinsa
[114] Kuma wane ne mafi zalunci* daga wanda ya hana masallatan Allah, domin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan ba ya kasancewa a gare su su shige su face suna masu tsoro. Suna da, a cikin duniya wani wulakanci, kuma suna da, a cikin Lahira, Azaba mai girma
[115] Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma saboda haka, inda duk aka juyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadaci ne, Mai ilmi
[116] Kuma suka ce: "Allah Ya riƙi* ɗa." Tsarki ya tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, masu ƙanƙan da kai ne
[117] Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa
[118] Kuma waɗanda ba su da sani suka ce: "Don me Allah ba Ya yi mana magana, ko wata aya ta zo mana?"* Kamar wancan ne waɗanda suke a gabaninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukatansu sun yi kama da juna. Lalle ne, Mun bayyana ayoyi ga mutane masu sakankancewa
[119] Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bayar da bishara, kuma mai gargaɗi, kuma ba za a tambaye ka ba, game da abokan Wuta
[120] Kuma Yahudu ba za su yarda da kome daga gare ka ba, kuma Nasara ba za su yarda ba, sai ka bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zuciyoyinsu a bayan abin da ya zo maka na ilmi, ba ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma babu wani mataimaki
[121] Waɗanda Muka bai wa Littafi suna karatunsa a kan haƙƙin karatunsa, waɗannan suna imani da shi (Alƙur'ani). Kuma wanda ya kafirta da shi, to, waɗannan su ne masu hasara
[122] Ya Bani Isra'ila! Ku* tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Ni, Na fifita ku a kan talikai
[123] Ku ji tsoron wani yini, (a cikinsa) wani rai ba ya tunkuɗe wa wani rai kome kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani ceto ba ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba
[124] Kuma a lokacin da Ubangijin Ibrahim Ya jarrabe shi da wasu kalmomi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Ni, Mai sanya ka shugaba domin mutane ne." Ya ce: "Kuma daga zuriyata." Ya ce: "AlkawariNa ba zai samu azzalumai ba
[125] Kuma a lokacin da Muka sanya ¦akin ya zama makoma ga mutane, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙami Ibrahim, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrahim, da Isma'ila da cewa: "Ku tsarkake ¦akiNa domin masu ɗawafi da masu lizimta da masu ruku'i, masu sujada
[126] Kuma a lokacin da lbrahim ya ce: "Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutanensa, daga 'ya'yan itacen, wanda ya yi imani, daga gare su, da Allah da Ranar Lahira." Allah Ya ce: "Wanda ya kafirta ma Ina jiyar da shi daɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tilasta shi zuwa ga azabar Wuta. Kuma makomar, ta munana
[127] Kuma a lokacin da Ibrahim yake ɗaukaka harsashin gini ga ¦akin, da Isma'ila (suna cewa:) "Ya Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani
[128] Ya Ubangijnmu! Ka sanya mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamawa zuwa gare Ka, Kuma Ka nuna mana wuraren ibadar hajjinmu, kuma Ka karɓi tuba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tuba, Mai rahama
[129] Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo* daga gare su, yana karanta musu ayoyinKa, kuma yana karantar da su Littafin** da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwayi Mai hikima
[130] Kuma wane ne yake gudu daga aƙidar Ibrahim, face wanda ya jahilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun zaɓe shi, a cikin duniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lahira, haƙiƙa, yana daga salihai
[131] lokacin da Ubangijisa ya ce da shi ka mika wuya sai ya ce na mika wuya ga Ubangijin Talikai
[132] Kuma lbrahim ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙubu (ya yi wasiyya, suka ce:) "Ya ɗiyana! Lalle ne, Allah Ya zaɓa muku addini don haka kada ku mutu, lalle, face kuna Musulmi
[133] Ko kun* kasance halarce a lokacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙubu, a lokacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mene ne za ku bauta wa daga bayana?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrahim da lsma'ila da Is'haƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi masu miƙa wuya ne
[134] Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta, Kuma ba za a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatawa
[135] Kuma suka ce: "Ku kasance* Yahudawa ko Nasara, kwa shiryu."Ka ce: "A'a aƙidar Ibrahim dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirki ba
[136] Ku* ce: "Mun yi imani da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrahim da Isma'ila da Is'haka da Ya'aƙubu da jikoki, da abin da aka bai wa Musa da Isa, da abin da aka bai wa annabawa daga Ubangijinsu, ba mu rarrabewa a tsakanin kowa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, masu miƙa wuya ne
[137] To, idan sun yi imani* da misalin abin da kuka yi imani da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun juya baya, to, suna a cikin saɓani kawai saboda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani
[138] Rinin Allah! Kuma wane ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, masu bautawa ne
[139] Ka ce: Shin kuna jayayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhali kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mu, a gare Shi, masu tsarkakewane
[140] Ko kuna cewa: Lalle ne, Ibrahim da Isma'ila da Is'haƙa da Ya'aƙubu da Jikoki, sun kasance Yahudawa ko kuwa Nasara? Ka ce: Shin ku ne kuke mafi sani koAllah? Kuma wane ne ya zama mafi zalunci daga wanda ya boye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa
[141] Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma ba a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatawa
[142] Wawaye daga mutane za su ce: Mene ne ya juyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah ¦ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya
[143] Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya* domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla** wadda ka kasance a kanta ba, face domin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake juyawa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, ta kasance haƙiƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tozartar da imaninku.*** Lalle ne, Allah, ga mutane, haƙiƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai
[144] Lalle ne, Muna ganin jujjuyawar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu juyar da kai ga Alƙibla wadda kake yarda da ita. Sai ka juyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku juyar da fuskokinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littafi, haƙiƙa su, suna sanin lalle ne, shi ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatawa
[145] Kuma hakika, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan aya, ba za su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sashensu ba mai bin Alƙiblar* sashe ba ne. Kuma haƙiƙa, idan ka bi son zuciyoyinsu daga bayan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzalumi kake
[146] Waɗanda Muka ba su Littafi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓoyewar gaskiya alhali kuwa su, suna sane
[147] Gaskiya daga Ubangijinka* take saboda haka, lalle kada ka kasance daga masu shakka
[148] Kuma kowane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gaba ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kome, Mai ikon yi ne
[149] Kuma daga inda ka fita, to, sai ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa ba
[150] Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa, domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kanku, face waɗanda suka yi zalunci daga gare su. Saboda haka kada ku ji tsoronsu kuma ku ji tsoroNa kuma domin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammaninku za ku shiryu
[151] Kamar* yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ayoyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littafi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba
[152] Saboda haka, ku tuna Ni, In tuna ku, kuma ku yi godiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini
[153] Ya ku waɗan da *suka yi imani! Ku nemi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tare da masu haƙuri
[154] kada ku ce ga waɗanda ake kashewa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." A'a, rayayyu ne, kuma amma ba ku sani ba
[155] Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsoro da yunwa da naƙasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace. Kuma ka yi bishara ga masu haƙuri
[156] Waɗanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: "Lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu, zuwa gare Shi, muke komawa
[157] Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan su ne shiryayyu
[158] Lalle ne Safa da Marwa* suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦aki ko kuwa ya yi Umra, to, babu laifi a kansa ga ya yi ɗawafi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙara yin wani aikin alheri to, lalle ne Allah Mai godiya ne, Masani
[159] Lalle ne waɗanda suke ɓoyewar abin da Allah Ya saukar da ga hujjoji bayyanannu, da shiriya, daga bayan Mun bayyana shi ga mutane, a cikin Littafi (Alƙur'ani), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma masu la'ana suna la'anar su
[160] Sai waɗanda suka tuba, kuma suka gyara, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tuba a kansu kuma Ni ne Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai
[161] Lalle ne, waɗanda suka kafirta kuma suka mutu alhali kuwa suna kafirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Mala'iku da mutane gaba ɗaya
[162] Suna madawwama a cikin ta, ba a sauƙaƙa Azaba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba
[163] Kuma Ubangijinku Ubangiji* Guda ne. Babu wani Ubangiji face Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai
[164] Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da saɓawar dare da yini, da jirage wadaɗnda suke gudana a cikin teku (ɗauke) da abin da yake amfanin mutane, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rayar da ƙasa da shi a bayan mutuwarta, kuma Ya watsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da ƙasa; haƙiƙa, akwaiayoyi ga mutane masu yin hankali
[165] Kuma akwai daga mutane wanda yake riƙon kinaye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi imani ne mafiya tsananin so* ga Allah. Kuma da waɗanda** suka yi zalunci, suna ganin lokacin da za su ga azaba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cewa lalle neAllah Mai tsananin azaba ne
[166] A lokacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azaba, kuma sabubba suka yanke da su
[167] Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Da lalle ne muna da wata komawa (duniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (da ba su riƙi kinayen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nuna musu ayyukansu, suna da nadamomi a kansu, kuma ba su zama masu fita daga wutar ba
[168] Ya ku mutane!* Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai daɗi. Kuma kada ku bi zambiyoyin* Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne
[169] Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfasha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah
[170] kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "A'a, muna bin abin da muka sami ubanninmu sun saba a kansa." ashe koda iyayen su sun zamanto basa iya fahimtar komai ballanta ma su shiriya ga gaskiya
[171] Kuma misalin (mai kiran) waɗanda suka kafirta kamar misalin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, face kira da ƙara, kurame, bebaye, makafi, saboda haka ba su hankalta
[172] Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ci ku sha daga masu daɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gode wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa
[173] Kawai abin da Ya haramta a kanku, mushe da Jini da naman alade da abin da aka kururuta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsa, wanin ɗan tawaye, kuma banda mai zalunci, to babu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
[174] Lalle ne waɗannan da suke ɓoye abin da Allah Ya saukar daga Littafi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan ba su cin kome a cikin cikkunansu face wuta, kuma Allah ba zai yi musu magana ba a Ranar ¡iyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi
[175] Waɗan nan su ne waɗan da suka sayi ɓata da shiriya, kuma azaba da gafara. To, me ya yi haƙurin su a kan Wuta
[176] Wancan domin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka saɓa a cikin Littafin, haƙiƙa, suna a cikin saɓani mai nisa
[177] Bai zama addini* ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira da mala'iku da Littattafan sama da Annabawa, kuma ya bayar da dukiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marayu da matalauta da ɗan hanya da masu roƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, da masu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da masu haƙuri a cikin tsanani da cuta da lokacin yaƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne masu taƙawa
[178] Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta, a kanku, yin ƙisasi* a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bawa da bawa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alheri da biya zuwa gare, shi da kyautatawa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zalunci a bayan wancan, to, yana da azaba mai raɗaɗi
[179] Kuma kuna da rayuwa a cikin ƙisasi, ya ma'abuta hankula; tsammaninku, za ku yi taƙawa
[180] Kuma an wajabta,* a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dukiya, wasiyya domin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan masu taƙawa
[181] To, wanda ya musanya masa a bayan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani
[182] To, wanda ya ji tsoron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakaninsu to babu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gafara ne, Mai jin ƙai
[183] Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta* azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi taƙawa
[184] Kwanuka ƙidayayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙara alheri to, shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alheri a gare ku idan kun kasance kuna sani
[185] Watan Ramalana ne wanda aka saukar da Alƙur'ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku, za ku gode
[186] Kuma idan bayiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kira Ni.* Saboda haka su nemi karɓawaTa, kuma su yi imani da Ni: tsammaninsu, su shiryu
[187] An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i* zuwa ga matanku su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karɓi tubarku, kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu itikafi a cikin masallatai. Waɗancan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi taƙawa
[188] Kada ku ci dukiyoyinku* a tsakaninku da ƙarya, kuma ku sadu da ita zuwa ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi alhali kuwa ku, kuna sane
[189] Kuma suna tambayar ka* daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lokatai ne domin mutane da haji, kuma ba addini ba ne ku je wa gidaje daga bayansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidaje daga ƙofofinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammaninku, ku ci nasara
[190] Kuma ku yaƙi waɗanda* suke yaƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsokana, lalle ne Allah ba Ya son masu tsokana
[191] Kuma ku yaƙe su inda kuka same su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yaƙe su a wurin Masallaci Tsararre (Hurumin Makka) face fa idan sun yaƙe ku a cikinsa. To, idan sun yaƙe ku, sai ku yaƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kafirai yake
[192] Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
[193] Kuma ku yaƙe* su har ya zama wata fitina ba za ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to babu tsokana face a kan azzalumai
[194] Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmomi masu dukar juna ne. Saboda haka wanda ya yi tsokana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misalin abin da ya yi tsokana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Yana tare da masu taƙawa
[195] Kuma ku ciyar* a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son masu kyautatawa
[196] Kuma ku cika* hajji da umra domin Allah. To idan an kange ku, to, ku bayar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kanunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, ko kuwa akwai wata cuta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dadi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai samu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun koma, waɗancan goma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyalinsa ba su kasance mazaunan Masallaci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙuba ne
[197] Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji* a cikinsu to babu jima'i kuma babu fasiƙanci, kuma babu jayayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alherin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula
[198] Babu laifi a kanku ga ku nemi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malalo daga Arafat, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harami kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabaninsa, haƙiƙa, daga ɓatattu
[199] Sa'an nan kuma ku malalo daga inda mutane suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙKai
[200] To, idan kun ƙare ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, ko kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: "Ya Ubangjinmu! Ka ba mu a cikin duniya! Kuma ba ya da wanirabo a cikin Lahira
[201] Kuma daga gare su akwai wanda yake cewa: "Ya Ubangijinmu! Ka ba mu mai kyau a cikin duniya da mai kyau a cikin Lahira, kuma Ka tsare mana azabar Wuta
[202] Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sana'anta; kuma Allah Mai gaggawar sakamako ne
[203] Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu.* To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, babu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, babu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne ku, zuwa gare Shi ake tara ku
[204] Kuma akwai daga mutane* wanda maganarsa tana ba ka sha'awa a cikin rayuwar duniya, alhali yana shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husuma ne
[205] Kuma idan ya juya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa domin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shuka da 'ya'yan dabbobi. Kuma Allah ba Ya son ɓarna
[206] Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsoron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙiƙa, shimfiɗa ta munana
[207] Kuma akwai daga mutane* wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bayi ne
[208] Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga cikin Musulunci gaba ɗaya; kuma kada ku bi zambiyoyin Shaiɗan; lalle ne shi a gare ku maƙiyine, bayyanan ne
[209] To, idan kun karkace daga bayan hujjoji bayyanannu sun zo muku to ku sani cewa lalle ne Allah, Mabuwayi ne, Mai hikima
[210] Shin suna jira, face dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwoyi na girgije, da mala'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su
[211] Ka tambayi Bani Isra'ila, da yawa Muka ba su daga ayoyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bayan ta je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙuba ne
[212] An ƙawata rayuwar duniya ga waɗanda suka kafirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi imani, alhali waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Ranar ¡iyama. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, ba da lissafi ba
[213] Mutane sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabawa suna masu bayar da bishara kuma masu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su domin (Littafin) ya yi hukunci a tsakanin mutanen a cikin abin da suka saɓa wa juna a cikinsa. kuma babu wanda ya saɓa, a cikinsa, face waɗanda aka bai wa shi daga bayan hujjoji bayyanannu sun je musu domin zalunci a tsakaninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi imani ga abin da suka saɓa a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya
[214] Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misalin waɗanda suka shige daga gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cuta sun shafe su, kuma aka tsoratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi imani tare da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa
[215] Suna tambayar ka mene neza su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alheri sai ga mahaifa* da mafi kusantar dangantaka da marayu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne
[216] An wajabta* yaƙi a kanku, alhali kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fatar cewa ku ƙi wani abu, alhali shi ne mafi alheri a gare ku, kumaakwai fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma ku ba ku sani ba
[217] Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yaki a cikinsa. Ka ce: "Yin yaƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kafirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutanensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma ba su gushewa suna yaƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhali kuwa yana kafiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓaci a cikin duniya da Lahira. Kuma waɗannan abokan Wuta ne, su a cikinta madawwama ne
[218] Lalle ne waɗanda suka yi imani, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihadi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fatar (samun) rahamar Allah kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
[219] Suna tambayar ka game da giya da caca.* Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfanoni ga mutane, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mene ne za su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage."** Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ayoyi a gare ku; tsammaninku, kuna tunani
[220] A cikin duniya da Lahira. Kuma suna tambayar ka game da marayu.* Ka ce: "Kyautatawa gare su ne mafi alheri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓatawa daga mai kyautatawa. Kuma da Allah Ya so, da Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwayi ne, Mai hikima
[221] Kuma kada ku auri mata* mushirikai sai sun yi imani: Kuma lalle ne baiwa muminaita ce mafi alheri daga ɗiya kafira, kuma ko da ta ba ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi imani, kuma lalle ne bawa mumini shi ne mafi alheri daga da mushiriki, kuma ko da ya ba ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gafara da izninsa. Kuma Yana bayyana ayoyinsa ga mutane; tsammaninsu suna tunawa
[222] Kuma suna tambayar ka game da haila* Ka ce: Shi cuta ne. Saboda haka ku nisanci mata a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son masu tuba kuma Yana son masu tsarkakewa
[223] Matanku gonaki ne a gare ku,* saboda haka ku je wa gonakinku yadda kuka so. Kuma ku gabatar (da alheri) saboda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle neku masu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bayar da bishara ga muminai
[224] Kuma kada ku sanya* Allah kambu ga rantsuwoyinku domin kada ku yi wani alheri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakanin mutane, kuma Allah Mai ji ne, Masani
[225] Allah ba Ya kama ku da laifi saboda yasasshiya a cikin rantsuwoyinku. Kuma amma Yana kama ku saboda abin da zukatanku* suka sana'anta. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai haƙuri
[226] Ga waɗanda suke yin rantsuwa* daga matansu akwai jinkirin wata huɗu. To, idan sun koma, to, lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
[227] Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani
[228] Kuma mata waɗanda* aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma ba ya halatta a gare su, su ɓoye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyarawa. Kuma su matan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su matan). Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima
[229] Saki sau biyu* yake, sai a riƙa da alh eri, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka ba su, face fa idan su (ma'auran) na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyakokin Allah ne saboda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne Azzalumai
[230] Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, ba ta halatta a gare shi, daga baya, sai ta yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sabon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, babu laifi a kansu ga su koma wa (auren) juna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cewa za su tsayar da iyakokin Allah, kuma waɗancan dokokin Allah ne Yana bayyana su ga mutane waɗanda suke sani
[231] Kuma idan kun saki mata, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alheri ko ku sallame su da alheri, kuma kada ku riƙe su a kan cutarwa domin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙiƙa, ya zalunci kansa. Kuma kada ku riƙi ayoyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littafi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kome Masani ne
[232] Kuma idan kuka saki mata, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da juna a tsakaninsu (tsohon miji da tsohuwar mata) da alheri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana imani da Allah da Ranar Lahira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma ku ba ku sani ba
[233] Kuma masu haifuwa (sakakku)* suna shayar da abin haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alheri. Ba a kallafa wa rai face iyawarsa. Ba a cutar da uwa game da ɗanta, kuma ba a cutar da uba game da ɗansa, kuma a kan magaji akwai misalin wancan. To, idan suka yi nufin yaye, a kan yardatayya daga gare su, da shawartar juna, to babu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bayar da ɗiyanku shayarwa, to, babu laifi a kanku idan kun miƙa abin da kukazo da shi bisa al'ada. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne
[234] Kuma waɗanda suke mutuwa* daga gare ku suna barin matan aure, matan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwana goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ada. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne
[235] Kuma babu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta* da shi daga neman auren matako kuwa kuka ɓoye a cikin zukatanku. Allah Ya san cewa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa juna alkawari da shia ɓoye, face dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littafin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, saboda haka ku ji tsoronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gafara ne, Mai haƙuri
[236] Kuma babu laifi* a kanku idan kun saki mata matuƙar ba ku shafe su ba, kuma ba ku yanka musu sadaki ba. Kuma ku ba su kyautar daɗaɗawa, a kan mawadaci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; domin daɗaɗrwa, da alheri, wajibi ne a kan masu kyautatawa
[237] Kuma idan kuka sake su daga gabanin ku shafe su, alhali kuwa* kun yanka musu sadaki, to, rabin abin da kuka yanka face idan sun yafe, ko wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yafe. Kuma ku yafe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakaninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne
[238] Ku tsare* lokatai a kan salloli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna masu ƙanƙan da kai ga Allah
[239] To, idan kun ji tsoro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa ko kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nuna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba
[240] Kuma waɗanda suke mutuwa* daga gare ku, alhali suna barin matan aure, wasiyya ga matan aurensu da daɗaɗawa zuwa ga shekara guda babu fitarwa, to, idan sun fita to babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima
[241] Kuma waɗanda aka saki suna da daɗaɗawa gwargwadon hali, wajibi ce a kan masu jin tsoron Allah
[242] Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa; tsammaninku, kuna hankalta
[243] Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita* daga gidajensu, alhali kuwa su dubbai ne, domin tsoron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rayar da su, lalle ne Allah, haƙiƙa Ma'abucin falala a kan mutane ne, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa
[244] Kuma ku yi yaƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani
[245] Wane ne wanda* zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, domin Ya riɓanya masa, riɓanyawa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku
[246] Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashawarta* daga Bani Isra'ila daga bayan Musa, a lokacinda suka ce ga wani annabi nasu: "Naɗa mana sarki, mu yi yaƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammaninku idan an wajabta yaƙi a kanku cewa ba za ku yi yaƙin ba?" Suka ce: "Kuma mene ne a gare mu, ba za mu yi yaƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhali kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidajenmu da ɗiyanmu?" To, a lokacin da aka wajabta yaƙin a kansu, suka juya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai
[247] Kuma annabinsu* ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦aluta** ya zama sarki." Suka ce: "Yaya ne sarauta za ta kasance a gare shi, a kanmu, alhali kuwa mu ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a ba shi wata wadata ba daga dukiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Ya zaɓe shi a kanku, kuma Ya ƙara masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bayar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani
[248] Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alamar mulkinSa ita ce akwatin* nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Musa da Gidan Haruna suka bari mala'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alama a gare ku (ta naɗin ¦aluta daga Allah ne) idan kun kasance masu imani
[249] A lokacin da ¦aluta ya fita* da rundunonin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kogi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, face, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, face kaɗan daga gare su. To, a lokacin da (¦aluta) ya ƙetare shi, shi da waɗanda suka yi imani tare da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu iko a gare mu yau game da Jaluta da rundunoninsa."Waɗanda suka tabbata cewa lalle su masu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tare da masu haƙuri
[250] Kuma a lokacin da suka* bayyana ga Jaluta da rundunoninsa, suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sawayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutanen nan kafirai
[251] Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dawudu ya kashe Jaluta, kuma Allah Ya ba shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma ba domin tunkuɗewar Allah ga mutane sashensu da sashe ba lalle ne da ƙasa ta ɓaci; kuma amma Allah Ma'abucin falala ne a kan talikai
[252] Waɗancan ayoyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakika, kana daga manzanni
[253] Waɗancan manzannin* Mun fifita sashensu a kan sashe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sashensu da darajoji; kuma Muka bai wa Isa dan Maryama hujjoji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Ruhi mai tsarki. Kuma da Allah Ya so da waɗanda suke daga bayansu, ba za su yi yaƙi ba, daga bayan hujjoji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun saɓa wa juna, saboda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi imani, kuma daga cikin su akwai wanda ya kafirta. Kuma da Allah Ya so da ba za su yaƙi juna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi
[254] Ya ku waɗanda* suka yi imani! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabanin wani yini ya zo babu ciniki a cikinsa kuma babu abuta, kuma babu ceto, kuma kafirai su ne Azzalumai
[255] Allah, babu wani Ubangiji face Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da kome, gyangyaɗi ba ya kama Shi, kuma barci ba ya kama Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin ceto a wurinSa, face da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bayansu. Kuma ba su kewayewa da kome daga ilminSa, face da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su ba ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma
[256] Babu tilastawa* a cikin addini, haƙiƙa shiriya ta bayyana daga ɓata; Saboda haka wanda ya kafirta da ¦aguta kuma ya yi imani da Allah, to, haƙiƙa, ya yi riƙo ga igiya amintacciya, babu yankewa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani
[257] Allah Shi ne Masoyin waɗanda suka yi imani; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kafirta, masoyansu ¦agutu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, su a cikinta madawwama ne
[258] Shin, ba ka gani* ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrahim a cikin (al'amarin) Ubangijinsa domin Allah Ya ba shi mulki, a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rayawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Ni ina rayarwa kuma ina matarwa." Ibrahim ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakafirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
[259] Ko kuwa* wanda ya shuɗe a kan wata alƙarya, alhali kuwa tana wofintacciya a kan gadajen resunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rayar da wannan a bayan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shekara ɗari; sa'an nankuma ya tayar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a ka zauna shekara ɗari." To, ka duba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kowanensu) bai sake ba, kuma ka duba zuwa ga jakinka, kuma domin Mu sanya ka wata aya ga mutane. Kuma ka duba zuwa ga ƙasusuwa yadda Muke motsarda su sa'an nan kuma Mu tufatar da su, da nama", To, a lokacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cewa lalle Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne
[260] Kuma a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nuna mini yadda Kake rayar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi imani ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma domin zuciyata, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsaye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kowane dutse, sa'an nan kuma ka kira su za su zo maka gudane. Kuma ka sani cewa lalle Allah Mabuwayi ne, Masani
[261] Sifar waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwaya ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kowace zangarniya akwai ƙwaya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani
[262] Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma ba su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gori, ko cuta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba
[263] Magana mai kyau da gafartawa su ne mafi alheri daga sadaka wadda wata cutarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri
[264] Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku ɓata sadakokinku da gori da cutarwa, kamar wanda yake ciyar da dukiyarsa domin nuna wa mutane, kuma ba ya yin imani da Allah da Ranar Lahira. To, abin da yake misalinsa, kamar falalen dutse ne, a kansa akwai turɓaya, sai wabilin hadari* ya same shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Ba su iya amfani da kome daga abin da suka sana'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai
[265] Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dukiyarsu domin neman yardojin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misalin lambu ne a jigawa wadda wabilin hadari ya samu, sai ta bayar da amfaninta ninki biyu To, idan wabili bai same ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne
[266] Shin ɗayanku na son cewa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabinai da inabobi' maremari suna gudana daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kowane 'ya'yan itace, kuma tsufa ya same shi, alhali kuwa yana da zuriyya masu rauni sai guguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta same shi, har ta ƙone? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanawar ayoyi a gare ku, tsammaninku kuna tunani
[267] Ya ku waɗan da suka yi imani! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sana'anta, kuma daga abin da Muka fitar saboda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhali kuwa ba ku zama masu karɓarsa ba face kun runtse ido a cikin sa. Kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Mawadaci ne, Godadde
[268] Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha*, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gafara daga gare shi da ƙari, kuma Allah Mawadaci ne, Masani
[269] Yana bayar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an ba shi alheri mai yawa. Kuma babu mai tunani face ma'abuta hankula
[270] Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, ko kuka cika alwashi daga wani bakance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka
[271] Idan kun nuna sadakoki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓoye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alheri a gareku, kuma Yana kankarewa, daga barinku, daga miyagun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne
[272] Shiryar da su ba ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alheri, to, domin kanku ne, kuma ba ku ciyarwa, face domin neman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alheri za a cika ladarsa zuwa gare ku, alhali kuwa ku ba a zaluntarku
[273] (Ciyarwar a yi ta) ga matalautan* nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jahilin halinsu yana zaton su wadatattu saboda kamun kai kana sanin su da alamarsu, ba su roƙon mutane da nacewa. Kuma abin da kuka ciyar daga alheri, to, lalle Allah gare shi Masani ne
[274] Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu, a dare da yini, ɓoye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba
[275] Wadanda suke cin riba* ba su tashi, face kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, domin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya koma, to, waɗannan su ne abokan Wuta, su a cikinta madawwama ne
[276] Allah Yana shafe albarkar riba, kuma Yana ƙara sadakoki. Kuma Allah ba Ya son dukan mai yawan kafirci, mai yawan zunubi
[277] Lalle ne, waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba
[278] Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance masu imani
[279] To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yaƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tuba to kuna da asalin dukiyoyinku, ba ku zalunta, kuma ba a zaluntar ku
[280] Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtawa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma da kun yi sadaka, shi ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani
[281] Kuma ku ji tsoron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta, kuma su ba a zaluntar su
[282] Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kun yi mu'amalar bayar da bashi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubuta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubutu a tsakaninku da adalci. Kuma kada marubuci ya ki rubutawa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubuta. Kuma wanda bashin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsoron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bashin yake a kansa ya kasance wawa ne ko kuwa rarrauna, ko kuwa shi ba ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da adalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mata biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun domin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazakutar* da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙosa ga rubuta shi, ƙarami ya kasance ko babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi adalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gewayarwa da shi hannu da hannu a tsakaninku to babu laifi a kanku, ya zama ba ku rubuta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fasiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kome Masani ne
[283] Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubuci ba, to, a bayar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sashenku ya amince wa sashe, to, wanda aka amince wannan sai ya bayar da amanarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓoye shaida, kuma wanda ya ɓoye ta, to, shi mai zunubin zuciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatawa Masani ne
[284] Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓoye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gafara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne
[285] Manzon Allah ya yi imani da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da muminai. Kowanensu ya yi imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Ba mu rarrabewa a tsakanin daya daga manzanninSa. Kuma (muminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi da'a; (Muna neman) gafararKa, ya Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makoma take
[286] Allah ba Ya kallafa wa rai face ikon yinsa, yana da ladar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa: "Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabaninmu. Ya Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da babu iko gare mu da shi. Kuma Ka yafe daga gare mu, kuma Ka gafarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, saboda haka Ka taimake mu a kan mutanen nan kafirai