Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 101 - Al-Qariah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Qariah 101:1
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)
Verse 2 — Surah Al-Qariah 101:2
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa
Verse 3 — Surah Al-Qariah 101:3
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa
Verse 4 — Surah Al-Qariah 101:4
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa
Verse 5 — Surah Al-Qariah 101:5
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe
Verse 6 — Surah Al-Qariah 101:6
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi
Verse 7 — Surah Al-Qariah 101:7
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda
Verse 8 — Surah Al-Qariah 101:8
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi)
Verse 9 — Surah Al-Qariah 101:9
To, uwarsa Hãwiya ce
Verse 10 — Surah Al-Qariah 101:10
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita
Verse 11 — Surah Al-Qariah 101:11
Wata wuta ce mai kuna