Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 100 - Al-Adiyat
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Adiyat 100:1
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki
Verse 2 — Surah Al-Adiyat 100:2
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa
Verse 3 — Surah Al-Adiyat 100:3
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba
Verse 4 — Surah Al-Adiyat 100:4
Sai su motsar da ƙũra game da shi
Verse 5 — Surah Al-Adiyat 100:5
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya
Verse 6 — Surah Al-Adiyat 100:6
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa
Verse 7 — Surah Al-Adiyat 100:7
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka
Verse 8 — Surah Al-Adiyat 100:8
Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne
Verse 9 — Surah Al-Adiyat 100:9
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura
Verse 10 — Surah Al-Adiyat 100:10
Aka bayyana abin da ke cikin zukata
Verse 11 — Surah Al-Adiyat 100:11
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne