Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 102 - At-Takathur
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah At-Takathur 102:1
Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku)
Verse 2 — Surah At-Takathur 102:2
Har kuka ziyarci kaburbura
Verse 3 — Surah At-Takathur 102:3
A'aha! (Nan gaba) zã ku sani
Verse 4 — Surah At-Takathur 102:4
Sa'an nan, tabbas, zã ku sani
Verse 5 — Surah At-Takathur 102:5
Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni
Verse 6 — Surah At-Takathur 102:6
Lalle ne da kuna ganin Jahĩm
Verse 7 — Surah At-Takathur 102:7
Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane
Verse 8 — Surah At-Takathur 102:8
Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku)